Page 24

211 10 0
                                    


Page 24

Kama ta Ameerah ta yi ta mikar, ta zaunar da ita a bakin gado sannan ita ma din ta zauna.
"Ki yi hakuri Bahijja, but I can't marry Haidar, ba Haidar ba ma, I can't marry anyone."

Gyada mata kai Bahijja ta yi tana jin hawaye na sauko mata.
"Ban san yanda kike ji ba Ameerah. Na dai san cewa har yanzu kina cike da kewar Yah Ameer. Sai dai ki sani ba zai taba dawowa ba. Kada rashinshi ya sanya ki yanke sunnar ma'aiki SAW. Shi da kanshi ya ce ba ya tare da wanda yake yanke sunnarshi (aure). So please kar ki ce haka."

Hannunta Ameerah ta kama ta ce
"Ya zan yi da tarin alkawurran da muka daukar ma juna ni da Yah Ameer? Ya zan yi da  zunubin cin amana idan na auri wani ba Yah Ameer ba? Kina tunanin zan ji dadin aurena bayan alkawarin da na sha yi masa kan cewa ba zan taba auren wani ba shi ba?"

"Allah ba zai taba kama ki da wannan laifin ba Ameerah. Ba za ki taba shiga sahun masu karya alkawari ba. Ba ki ci amanarshi ba, saboda he is no more in this dunya. Ko da a ce bayan kun riga kun yi aure ne fa kina da right na auren wani daban after finishing your takaba. Then why kike tunanin alhaki zai kama ki bayan kuma ba ki riga kin aure shi ba sannan ba shi a duniyar ma kwata-kwata?"

Cikin kuka sosai Ameerah ta ce
"Ba za ki gane ba Bahijja, ba ki san abin da nake ji ba shi ya sa har kika nace a kan zancen nan. Don girman Allah..."
Ta koma ita ta yi kneeling din, ita ce ke begging din da hannuwanta biyu dunkule da juna.
"Ki taimaka ki kyale ni da zancen nan. Ba zan taba auren Haidar ba nor any other. Ki yi hakuri ke ki aure shi I will follow you with du'a."

Ajiyar zuciya Bahijja ta sauke. Ba ta dauka abun zai kai su har haka ba. Da alama ba za ta taba iya shawo kan Ameerah a kan wannan batun ba. Sai dai kuma ya za ta yi da alkawarin da ta daukar masa?

"Ameerah me zan fada wa Haidar? Ya zan yi da alkawarin da na daukar masa?"

"Bahijja ya zan yi da alkawarin da na daukar wa Yah Ameer?"

Gajeren murmushi Bahijja ta sauke. Ta kama Ameerah ta mikar sannan ta ce
"Shi kenan. Thanks a lot for your time. Na gode sosai Allah Ya saka."

"Amin." Kawai Ameerah ta fada.

"Wipe your tears before mu sauka wannan naughty Sister din taki ta ce na saka mata Yayarta kuka."

Dariya Ameerah ta yi tana share hawayen nata.
Tare suka sauka kamar babu abin da ya faru. Sai dai duk wanda ya san Ameerah sosai ya ga fuskarta sai ya san ta yi kukan. Shi ya sa ta hau kauce wa haduwar fuskarsu ita da Sumayya gudun dogayen tambayoyi.

Bayan Bahijja ta zauna ta dan gutsiri guntun cake ta ci sannan ta bi da sauran zobon da ta rage a cup duk da ya huce. Mikewa ta yi tana fadin
"Habiba mu je ko? Har la'asar ta yi ga shi kuma akwai inda zan je."

Mikewa ita ma Habibar ta yi tana kallon Sumayya,
"My Sister tafiya za mu yi. Yaushe za ku zo?"

Sumayya ta tabe baki tana yarfe hannunta
"Oho...tambayi Aunty dan ita ce mai tafiyar ba ni ba. Idan ta ga dama ma tana iya rufe ido ta ce babu inda za ta da ni."

Dariya suke su duka.
"Ba za ku jira Ammi ta zo ku gaisa ba? Na tabbata tana hanya yanzu."

"Don't worry Ameerah sai a tari next time. Mun gode sosai da karamci. Ki gaishe ta."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now