Page 63

174 7 0
                                    


Page 63

24/10/2021

Kotu ta cika sosai har ma ta zarce karon farko, inda kowa ya yi jugum domin sauraron wannan shari'ar mai sarkakiya. Familyn Ibrahim tun jiya suka iso Ameerah ta sauke su a wurin Ammi. Haka Kamal ma tun jiya ya iso. Duk families dinsu sun hallara inda suke fatan nasara ta zama tasu. Mr Patric yana zaune tumbi ya yi zundum a gaba, matarshi da yaranshi biyu mace da namiji na zaune a gefenshi dukkansu hankulansu a kwance saboda ba su taba tunanin mahaifinsu zai aikata abin da ake tuhumarshi da shi. Sun sani kamar yanda duk duniya ta sani cewa Mr Patric mutumin kirki ne, mutum mai fara'a da kyauta.

A wurin zaman lauyoyi kuwa Ameerah ce zaune cike da confidence sai sakin murmushi take. Kusa da ita Barrister John ne sai Moses daga gefenshi. Haka kawai John ya tsinci kanshi da faduwar gaba musamman yanda Ameerar ke ta sakin murmushi idan sun hada ido. Sosai ya hango kwarin guiwa a cikin idanuwanta fiye da zamansu na farko.

Shigowar alkali ce ta sanya kowa mayar da hankali gare shi. Bayan ya zauna a mazauninsa mai gabatar da kara ya mike.
"A yau 24th October 2021 ne wannan kotu mai adalci za ta ci gaba da sauraren shari'ar Ameer Nuraddeen da kuma Mr Patric, wanda Ameer din ya shigar da shi k'ara a bisa zargin ya sanya a kashe shi."
Ya dan rusuma hade da mika file dinsu ya isa ga mai shari'a.

Gilashinsa da ke zaune bisa dogon hancinsa ya daidaita, sannan ya bude file din ya karanta layi biyu zuwa uku kafin ya dago kanshi ya ce
"Mr Patric da Ameer Nuraddeen ku bayyana a gaban kotu."
Sannan ya kalli gefen da lawyers din suke ya ce
"Barrister Ameerah, kotu za ta so ki gabatar mata da shaidunki daga inda kika tsaya a wancan zaman namu na mako biyu da suka gabata."

Mikewa ta yi ta dan rusuna cikin girmamawa ta ce
"Na gode ya mai shari'a."

Ta juya ga audience ta ce
"Kamal Ahmad Karofi, kotu za ta so ka bayyana a gabanta domin ka amsa wasu tambayoyi."

Sai da ya dan saci kallon Mr Patric ya tuna yanda ya kore shi daga aiki babu imani, sannan ya tuna da kalar rayuwar da ya shiga a baya sanadiyyar korarshi aiki da aka yi. Cikin kwarin guiwa yake takawa har ya isa inda aka tanadar domin gabatar da shaidu.

Ameerah ta matsa daf da shi ta ce
"Mallam Kamal kotu za ta so ka fada mata ko waye kai da kuma alakarka da AHC."

Babu ko alamar tsoro Kamal ya hau zazzaga bayanin duk abubuwan da suka faru tun daga amincinsu da Ameer har zuwa fada masan da ya yi cewa za su yi tafiya tare da Patric, har zuwa kama shi da aka yi aka kai guest house dinshi, zuwa korarshi da aka yi, sannan a karshe ya dora da
"Rayuwata ta kuntata sosai ta silar kora ta da ya yi. Na rasa mutane biyu mafi soyuwa a gare ni saboda talauci."
Ya karasa maganar da hawaye taf a idanuwansa.

Mutane da dama sun tausaya wa rayuwar da ya shiga, wasu daga ciki sun fara gasgatawa da zancen zargin Mr Patric din, saboda duk gani ake kawai Ameer ya kirkiri Zancen ne saboda ya bata masa suna.

Ameerah ta juya ta kalli alkali ta ce
"Ya mai girma mai shari'a, Kamal Karofi shi ne babban abokin Ameer, wanda Mr Patric ya kora daga wurin aiki kawai saboda Ameer ya fada masa za su yi tafiya tare..."

"Objection my lord!"
John ya furta yana mikewa tsaye.
"Har yanzu zargi bai tabbata a kan Mr Patric ba, don haka bai kamata kai tsaye Barrister Ameerah ta jingina masa laifi ba."

Alkali ha kalli Ameerah hade da fadin
"Barrister Ameerah a kiyaye."

Ta jinjina kai sannan ta ci gaba da cewa
"Mr Patric ya tsorata Kamal sosai ta yanda ya tabbata ba zai sake waiwayar garin ba balle har wani zance ya fito ta bangarenshi. Na gode ya mai shari'a."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now