Page 3

551 25 0
                                    

MATAR AMEER...(2021)

By Princess Amrah
NWA

Page 03

Kai tsaye idan ya je bai san wurin wanda zai nufa ba, haka kuma bai san abin da zai ce ba idan ya je din. Hakan ya sa kawai ya fasa shiga, ya fito tare da dosar inda motarshi take ya tayar ya tafi. Sai dai ga baki daya tunanin lamarin yake yi. Ya rasa dalilin da ya sa Mr. Patric zai masa karya. Komai yake ji yana cakude masa, dukkan wani confidence nashi na samun aiki a kamfanin yake ji yana raguwa, yana rikidewa zuwa wani abun can na daban wanda ba zai ce takamaimai ga shi ba.

Bayan ya isa hotel din ya zauna, bai san abin da zai yi ba, kamar yadda bai san kai tsaye abin da yake ji cikin zuciyarsa ba. Haka ya matsu gari ya waye don ya bar garin, jin sa yake yi kamar a bisa kaya yake. Baki daya dream dinshi yake ji yana neman daukarshi daf, ya kai shi can wani wajen da ba zai ce ga shi ba.

A rayuwarshi tunda aka haife shi yake da ra'ayin zama kwararren mai zana taswirar gidaje, yake da burin zama wani hamshaki kuma sananne a harkar. Sai a yanzu da yake ganin burin nashi na neman cika kuma wani abu ke neman zuwa ya tokare zuciyarshi. Mene ne wannan abun da ya yi babakere a tsakanin kirjinshi wanda ke neman sauya masa raayin da yake tunanin da shi aka haife shi?

***
Da hope ya je garin, da hope ya je wurin Mr. Patric, sai dai ya rasa yanda aka yi yake jin komai bambarakwai a yanzu. Tuki yake amma ya rasa abin da yake masa dadi. A yanzu dai lokaci ya kure, bai da bakin tinkarar mahaifinsa ya fada masa abin da yake ji game da aikin da yake ganin ya cika masa burinsa. Kanshi ya shafa, yana jin duniyarshi na neman sauya masa. Ya zai yi? Dole ne ya karba, dolenshi ya yi aiki a karkashin AHC saboda ba zai iya ba mahaifinsa kunya ba. Da haka ya gama yanke shawarar yin aiki a kamfanin, aikin da zai zama mabudi, ya kuma zama silar rugujewar farin cikin Ameer, Ameerah, da kuma dukkan makusantansu.

***
Karfe uku na rana ya iso garin Kaduna. Akwai hold up sosai saboda gadar Kawo da ake sabuntawa, hakan ya sa ya jima kafin ya isa gida. Da farin cikinshi ya isa gida, yana dora idanuwanshi a kan mahaifiyarshi da ke tsaye tana tattara kaya daga bisa dining table.
"Sannu Umma."
Ya fada yana dafa ta. Da murmushi ta juyo tana kallon shi.

"Umma ke da kanki ke kwashe kayan? Ina su Habeebah?"

"Sun tafi Islamiyya Ameer. Mai aikinmu kuma ta je gida ka sani ai."

"Haka ne umma. Bari in shiga ciki."

"Ka yi wanka ka zo ka ci abinci don na tabbata kana jin yunwa."

"Sosai ma Umma. Tun safe ban ci komai ba. Amma dai in yi wanka da sallah first." Ya fada yana shigewa dakinsa.

Bayan ya yi wanka ya yi sallah ya kira Ameerah tare da yi mata albishirin ya dawo gida, abinci kawai zai ci ya zo.

"Ina School ne Yaya sai idan nan din za ka zo sai ka dauke ni."

"Kin gama ne?" Ya tambaye ta yana mikewa.

"Eh na gama Yaya. Da ma submitting assignment ne zan yi na san kafin ka iso har na yi."

"Okay sai na zo." Ya fada yana tsinke wayar. Ko abincin ma bai tsaya ya ci ba ya lallaba ya fice dan kar Umma ta hana shi fita ba tare da ya ci komai ba.

Kai tsaye department dinsu ya nufa, bayan ya je ya kira ta ta ce ga ta nan zuwa dan ta gama komai dama shi kadai take jira.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now