Page 33

222 22 0
                                    


Page 33

Ta fi minti goma tana bubbuga dakin amma Ameerah ba ta bude ba. Tun tana yi a hankali har ta koma bubbugawa da dan karfi, ita tsoro ma abun ya fara ba ta. Cikin wata irin murya ta hau fadin
"Don Allah Aunty ki bude kofar, ki bude mu yi magana."

Shiru ko motsin Ameerah ba ta ji ba. Da karfi cikin kuka ta ce
"Aunty ki bude mana ko so kike wani abu ya same ki?"

Ita kuwa Ameerah tana jin yanda Sumayya ke mata magiyar ta bude kofa, muryarta na k'ara mata rauni, sai dai ko kadan ba ta da kuzarin da za ta iya mikewa ta bude kofar. Duk da kukan Sumayya na shigar ta, magiyarta na tasiri, sai dai ko kadan ba ta jin za ta iya hada ido da kanwar tata a daidai wannan lokacin.

"Aunty Ameerah mana ki bude ko so kike wai zuciyata ta buga?"
Da wani irin karfi Sumayya ta yi wannan maganar.

Dan saurarawa Ameerah ta yi daga kukan da take yi, ta yi kasak'e cike da al'ajabi, tunda suke da da Sumayya ko da wasa ba ta taba jin ta ambaci sunanta a irin wannan yanayin ba, Aunty sama aunty k'asa take, in dai ta fadi Ameerar a gaba to cikin hira ne.

Ba ta san sadda ta mike ba, cikin azama ta bude kofar, tana jawo Sumayya da karfi ta manna ta a kirjinta, kuka suke yi a tare, kuka mai cike da rauni da ban tausayi. Sun fi minti biyar a haka, kafin Ameerah ta ja ta a hankali ta zaunar da ita a bakin gado, sannan ta mayar da kofar ta yi locking dinta. Ruwan faro da ke kan side drawer ta dauka ta mika wa Sumayyar ta sha kadan sannan ta dawo mata da shi ita ma ta sha. Dukkansu suka hau sauke ajiyar zuciya.

"Aunty..."
Sumayya ta fada cikin sautin kuka, tana dorawa da
"Ki bi komai a sannu, dukkan tsanani yana tare da sauki."

Kai Ameerah ta daga, tana sa yatsunta biyu tana share ma Sumayya hawaye.

"Aunty ni na hakura da auren..."

"Shut up Sumayya!"
Ta fada cikin fada.
"Me kike son fadi? Ba ki da hankali? Kina hauka ne? Ni...a kaina za ki hakura da auren Marwan...Marwan muradin zuciyarki?"

Kai Sumayya ta daga, kafin ta dora da
"Na hakura Aunty, in dai aurenshi ne zai sanya su Daddy takura miki."

Ameerah ta hau gyada mata kai cikin rashin gamsuwa ta ce
"Kar in sake jin makamanciyar wannan maganar daga bakinki. Kina so Daddy ya yi fushi da ke fiye da wanda ya yi da ni?"

Ta gyada kai a hankali.

"To kar ki kuskura in ji wannan zancen a wurin su Ammi da Daddy. Idan ba haka ba kuma ranki zai baci fiye da tunaninki. Kafin Daddy ya yi fushi da ke ni zan fara, har dakin ma zan bar miki."

Kan cinyar Ameerah ta fada, tana kara rushewa da kuka, hawayenta na ratsawa ta tsakanin doguwar rigar robar da ke jikin Ameerah.

Dan bubbuga mata baya ta hau yi a hankali har ta samu ta yi shiru.
"Ba na son kukanki ko kadan Sumayya. You're too young da shiga irin wannan damuwar."

Ta dago fuskarta ta kalli Ameerah, kafin ta ce
"Ke ma ba ki kai girman da za ki rinka shiga damuwa irin wannan ba Aunty."

Murmushin karfin hali ta sakar mata,
"Am 28 years Sumayya, na fara jiyo kamshin 30. A yanda nake jin zuciyata yanzu babu kalar abinda ba zan iya tarbarshi ba. Zuciyata ta jima da kekashewa da rayuwar duniya. Kar ki damu, zan tarbi duk wata kaddara da mai kowa mai komai zai jefa a saitin duniyata. Zan karbi zabin Daddyna ko ba na so, Allah Shi ne masanin sirrin boye, Shi kadai Ya san halin da zuciyata take ciki, ba komai kuke gani ba...kadan daga ciki ne nake iya bayyanawa Sumayya."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now