Page 65

183 15 0
                                    


Page 65

Satin Ameerah daya a asibiti aka ba ta sallama. Amma an ce tana da bukatar a kula da ita sosai hakan ya sa suka yanke shawarar ta koma gidansu kawai don a ba ta kula yanda ya dace. Duk da rashin cikinta da ta yi ko kadan hakan bai sagar mata da guiwa wurin daukaka kara ba. Tun iyayen suna k'in amincewa har suka gamsu da hujjojin da take ba su. Dukkansu suka goyi bayanta amma da sharadin ta bari har sai ta murmure saboda har yanzu akwai sauran sati uku kafin wa'adin daukaka karar ya cika.

Ameer ya zo duba Ameerah yana dakinta wayarshi ta yi ringing, Daddyn Labiba ya gani yana kiran shi ya gaggauta dauka hade da gaishe shi. Ya mai jiki ya tambaye sa ya fada masa da sauki ga ta ma. Ta gaishe shi da sanyin murya ya amsa mata hade da fadin

"Kina burge ni sosai Ameerah. Ina son mutum mai kwazo da jajircewa. Kina da wani irin confidence na ban mamaki. In shaa Allahu a wannan karon za a yi nasara Ameerah. Zan zo k'asar tare da ni za a yi binciken komai har zuwa shari'ar. Addu'a ba ta faduwa kasa banza, da izinin Allah tanadi mai girma ne Allah Ya yi mana."

Sosai ta ji dadin kalaman nashi. Tana da bukatar support sosai fiye da wancan na baya. Takamaimai ba ta san ta inda za ta fara ba, sai dai tana ji a jikinta komai zai zo mata da sauki.

"Zan yi bincike sosai har cikin AHC din. Boyayyen halin Patric da izinin Allah sai Ya bayyana. Sannan akwai abin da nake planning din yi, ina fatan idan ya tabbata zai zama mabudin komai. Ban san haka za a kare a waccan shari'ar ba wallahi da na yi kokarin squeezing duk wani time nawa na ajiye uzururrukan na zo. Amma babu komai, dama haka Allah Ya tsara dole sai an fadi a karon farko. Kodayake ba faduwa ba ce, akasi ne aka samu, nasarar tana zuwa da yardar Allah."

"Haka ne Daddy. Na gode kwarai."
Ta fada cike da farin cikin da rabonta da shi tun kafin jin hukuncin alkali.

"Ya jikin naki?"

"Da sauki Daddy."

"Allah Ya kara sauki. Jikokina suna nan zuwa, so kar ki damu da tafiyar wannan, khairan in shaa Allah."

Kunya ta hana ta fadar komai ta mika ma Ameer wayar. Sun jima suna tattaunawa a kan zuwan da zai yi da kuma ganawa da zai yi da sarkin Zazzau kafin suka yi sallama.

"Daddy ya ce zai tsayu don ganin an samu manyan hujjoji Meerah. Ki kwantar da hankalinki tunda ya ce zai yi din na san zai yi. Nan da kwana uku ko hudu zai iso."

"Allah Ya yarda."

"Ameen. Ni bari in tafi dare ke yi. Me zan zo miki da shi gobe?"

"Nothing cheri. I love you."
Ta fada da murmushi.

"I love you too."
Ya mayar mata hade da manna mata kiss a goshi ya tafi.

Bayan kwana hudu Daddyn Labiba ya iso. Wannan karon ma a Hotel ya sauka kamar wancan. Kwananshi daya da isowa Ameer ya je ya dauko shi ya zo ya duba Ameerah da jiki tare da kara mata kwarin guiwa a kan abin da yake gabanta. Ya jima a nan suna tattaunawa kafin Saddam ya zo. Cikin jin kunya yana sosar keya ya gaida Daddy.

"Saddam my Son in-law."
Daddy ya ce yana kama hannunshi na dama ya saka a cikin nashi.

"An zo lafiya?"

"Alhamdulillah. Ya aikin naka?"

"Lafiya lau Daddy."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now