Page 8

376 16 2
                                    

MATAR AMEER...(2021)

By Princess Amrah
NWA

Page 08

"Ban taba tunanin zan samu biyan bukatata ba saboda na dade da cire raina, ban kawo cewa zan iya aiwatar da komai a kan Nura ba sai lokacin da muke ba junanmu labarin bayan rabuwa. A nan yake shaida min ka kammala karatunka a fannin architecture har ma ka kusa gama bautar k'asa. Ni na bullo masa da shawarar daukarka aiki a AHC, saboda in samu biyan bukatata a kanka. Abun mamaki sai hakan ya yi masa dadi, ya shaida min cewa burinka kenan a rayuwa. In banda shashanci...akwai ma'aikatu na gwamnati inda za ka iya samun aiki da babban matsayi, sai dai idon Nura ya rufe gani yake ga sauki wa zai jira gwamnati? Kodayake, cewa ya yi ka fara a nan sannu a hankali kafin ka samu na gwamnatin."
Dariya sosai Mr Patric ke yi a wannan gabar.
"Bai sani ba ashe makasarka ya kawo ka."

Ga baki daya tsoron da Ameer yake ji na Mr Patric ne yake rikidewa, yana cibre kanshi izuwa tsantsar rashin tsoro da fargaba. Idonshi ya juye daga tsoro ya koma babu alamar tsoro a tattare da shi. Ya tsuke fuskarshi, yana jin yanda nadama da danasani ke dawainiya da shi. Sai dai ta baya ta rago, domin kuwa bakin alkalami ya riga ya bushe. Babu abin da zai iya yi a yanzu, amma da sauki, yana da sauran numfashin da zai iya fada masa maganganun da zai jima suna nukurkusarshi. Ya dan tauni labbanshi duka biyun, kafin ya ce

"Ina alfahari da mahaifina da ya zama silar korar Ifeoma daga jami'a bisa ga zaluncin da ya ga ana neman yi. Haka kuma zan ci gaba da alfahari da shi bisa ga tsayuwar da ya yi don ganin ya cika mini burina na samun aikin da nake so." Ya saki murmushin takaici, kafin ya gyada kanshi, yana jin wani irin kwarin guiwa na zo masa.
"Patric! Ka gode ma Allah ka yi nasara a yanzu, sai dai ina mai tabbatar maka da cewa ba ka ci lalai ba, ko da ba ka shiga hannun hukuma ta silar kashe ni ba, to za ka shiga ta silar zaluncinka, da izinin Allah akwai ranar da za ta zo, wacce za ka yi bakin ciki don ganin an kai ka k'asa, komai daren dadewa."

Cikin halin ko'inkula ya bude motar, yana kallon garadan da ke tsaye dukkansu da bakaken kaya, idanuwansu babu alamun tausayi balle imani, dukkansu majiya karfi ne kosassu. Ya sakar masu murmushi.
"Ga shi nan ku masa laga-laga kafin ku aika shi lahira."

Har zai fita daga motar sai kuma ya dawo, ya kalli Ameer wanda babu alamun tsoro a tattare da shi, ya ce
"Na toshe duk wata kafa da za a iya gane ni na illata ka. Kamal zan san yanda na yi da shi. Ibrahim Surajo ma haka. Kai har gudan ma da kuke gida daya ban yarda da shi ba, su duka biyun za a magance, sai Kamal cikon na ukunsu."
Yana kaiwa nan ya fice daga motar, babu alamun tausayi a tattare da shi.

Kamar an ce Ameer ya waiga, can ya hango Musa driver cikin wata motar yana jiran Mr Patric. Sai ya ji muryarshi yana fadin,
"Idan kun gama da shi ku san yanda za ku yi da gawar. Sannan ku dauki wannan motar na ba ku. Ku biyo ni da lambar motar daga baya."

Ya sake juyowa wurin Ameer, ya saki kayataccen murmushi,
"Ilminka na banza ne tunda ka kasa gane ni din mugu ne. Mutum bai min komai ba ma idan na ga yana neman zarce ni sai na sa an aika shi lahira, balle kai, kai din da mahaifinka ya zama silar da na rasa Ifeoma."
Yana kaiwa nan ya bar wurin, yana dosar inda Musa Driver yake.
A bayan motar ya zauna, idanuwanshi na kallon yanda daya daga cikin garadan ya jawo Ameer daga cikin motar ya yi jifa da shi kasa.

"In shaa Allahu dukkanku karshenku ba zai yi kyau ba. Asirinku sai ya tonu komai daren dadewa." Abin da Ameer ke fadi kenan, duk da azabar dukan da ake masa na shigarshi ta ko'ina.

Duk inda suka samu a jikinshi bugu suke yi, tun daga kanshi har zuwa kafafuwa. Tun yana da bakin magana har ya rasa, a hankali ya rufe idanuwanshi, yana jin komai na jikinshi yana tsayawa da aiki.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now