Page 29

206 11 0
                                    


Page 29

Kai tsaye Stanley Park din suka nufa. Kayataccen wuri ne mai matukar burgewa. Annurinsu ya fadada ganin yanda family ke shiga suna fita cike da farin ciki.

Bayan Maryam ta faka motar an fiddo Ameer, Labiba ta mika wa Leo kudi amma ya hada hannuwanshi wuri guda ya jinjina alamar ta bar shi ya gode. Murmushi kawai ta masa ta mika masa kudin ya karba yana mata godiya.

Yanzu ma ita take tura Ameer har suka je wajen sayen ticket Maryam ta biya.

Suna shiga ciki suka rinka kallon mutane, manya da yara kowa da inda yake zuwa. Akwai bangaren da ake hawa train (jirgin k'asa) kawai saboda nishadi. Sannan akwai gefen da ruwa yake inda ake shiga jirgin ruwa da kwale-kwale a je a dawo cike da farin ciki. Sai gefen da ake yin stunt, sannan akwai restaurant, akwai wuraren wasan yara.

"Wow...Yaya Maryam kin ga yanda nake ta blushing."
Labiba ta fadi tana kallon Maryam.
"Ni na ma rasa inda za mu je."

"Ba dai zan shiga jirgin ruwa ba, a haka ma daga nesa tsoron ruwan nake ba zan iya matsawa ba."
Maryam ta ba ta amsa tana dan turo baki.

"Train fa?"

"Za ku iya shiga idan kina so Labiba. Me I can't can."
Ta fadi tana dariya.

"To kawai mu je mu yi hotuna a can, in ya so sai kawai mu wuce Tea House din can mu yi dinner."

"Okay fine. Mu je."
Maryam ta fada tana yin gaba Labiba ta bi bayanta tana tura Ameer.

Bayan sun isa wani irin iskan ni'ima ya rinka kad'awa saboda ruwan da ke akwai a wurin. Daya daga cikin yaran da ke wurin suka ba waya ya rinka daukar su hotuna har sai da suka ce ya bar shi haka. Daga nan suka koma jikin train ma suka samu wani ya rinka daukarsu.

Tea House suka koma, suka fara tunanin abin da za su yi ordering.

"Ina son coffee and sponge cake." Labiba ta fadi tana mayar da kallon ta ga Ameer.
"Yah Muhammad me kake so?"
Ya daga mata kai.
Ta dan saki murmushi a hankali kafin ta dora da
"I guess cappuccino and sandwich. Don na ga ranan da Daddy ya sayo su ka ci da yawa."

"Ni ma cappuccino din kadai nake so. Banda snack."
Maryam ta fada tana duba wayarta.

Waitress din wurin Labiba ta kira, ta ba ta takardar da ta yi ticking din abubuwan da suke so. Da sauri waitress din ta jinjina kai cikin girmamawa ta tafi.

Babu jimawa sai ga ta dauke da babban tray ta girke shi a kan teburin da suke zagaye da shi bisa kujeru.

Na Ameer Labiba ta dauka ta ajiye a gabansa hade da sandwich dinshi, ta mika wa Maryam nata sannan ita ma ta hau cin nata cikin kwanciyar hankali suna yi suna nishadi. Selfie ta yi musu duk suna dariya banda Ameer da har yanzu fuskarshi ba yabo ba fallasa.

Sai da suka gama duka sannan Labiba ta je ta yi payment ta dawo, Maryam ma ta mike, Labiba ta hau tura Ameer har suka tafi bakin mota.

Wannan tafiyar ba karamin faranta ran Ameer ya yi ba, sai dai ya rasa yanda zai yi ya gwada musu hakan. Wani irin nishadi yake ji wanda tunda ya farfado bai taba jin kamarshi ba. Daukaka darajar ahalin gidan yake yi a cikin zuciyarshi. Suna da karamci sosai, suna da mutunci sannan ba su san wani abu wai shi wulakanci ba. Duk da bai san waye shi ba, sai dai yana ganin yanda darajarshi take k'asa da tasu sosai.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now