Page 10

450 23 5
                                    

MATAR AMIR (2021)

By Princess Amrah
NWA

Page 10

Ta yi matukar farin ciki da ta kira Umma, Umma ta shaida mata dalilin da ya sa suka ji Ameer din shiru. Sai ta samu kanta da nutsuwa, da wani irin confidence. Ta yi kewar shi sosai, kusan sati shida kenan da tafiyarshi, sai ta tsinci kanta a nishadi ta fara haramar girki domin tarbarshi.

Ba ta so ya huce shi ya sa sai da aka yi sallar azahar sannan ta fara. Spaghetti da ta kasance favorite din Ameer ta dauko, ta kakkarya ta kanana sannan ta zuba a cikin mai ta soya har sai da ta zama brown sannan ta kwashe a colander, ta rage man ciki. Ta dauko kidney din da ta yi marinating da maggi da kayan kamshi ta zuba a cikin man, ta zuba albasa kadan sannan ta soya sama-sama. Already ta yanka carrots and green beans dinta ta wanke, ta dauka ta zuba a ciki, ta zuba curry, seasonings da sauran kayan kamshi sannan ta zuba sauran albasar, da tafasasshen peas ta ci gaba da soyawa. Tana jin kamshin su ya fara tashi ta saki sassanyan murmushi sannan ta zuba ruwan nama, ta kara da madaidaicin ruwa sannan ta rufe. Bayan ya tafasa ta dauko soyayyar taliyar ta zuba a ciki.
A dayan gefen kuma kaza ce ta bankare ta wanke ta tas, ta goge ta sosai da kitchen towel. Ta dauko tattasai da albasa, ta zuba mai kadan a cikin frying pan sannan ta jera tattasai da albasar, ta zuba fresh garlic guda biyu sannan ta gasa su gaba da baya. Ta dauko blender ta juye su, ta zuba mai, maggi, da spices duka a ciki da ruwa kadan ta yi blending dinsu har sai da suka zama smooth, peri-peri sauce kenan. Daga nan ta dauko kazar nan bankararra ta shafe sauce din a kanta sosai sannan ta dora a kan baking tray ta saka a pre-heated oven.
Ko da ta waiwayi taliyar har ta dahu sai kamshi take badadawa. Ta sauke ta zuba a cikin wata hadaddiyar food warmer.
Kazar ma bayan ta gasu ta nade ta a foil paper sannan ta dora a kan wani tray mai murfi.
Sobon da ta jika tun dazu ta duba, saboda ba ta cika son dafawa ba yana kashe amfaninshi a jiki. Ta dandana ta ji still akwai sauran tsami, baking powder ta zuba kadan sannan ta tace ta saka a cikin fridge. Abarba, kanka, cucumber da na'a-na'a ta yanka ta zuba a cikin blender ta markada. Bayan ta tace su ta juye duka a cikin sobon. Ba ta bukatar sugar, saboda zakin fruits din ma kadai ya wadatar. Ta dauko hadadden jug ta juye a ciki sannan ta cikin fridge din.

Karfe biyar ta kammala komai. Yanzu kam ta tabbata ko Ameer bai iso ba to yana kusa da Kaduna. Cike da d'oki ta je ta yi wanka, ta saka riga da skirt na material pink, ta yi kyau sosai ta koma parlor. Tana zaune Sumayya ta dawo daga Islamiyya, tun daga bakin kofa take fadin
"Wow! Kamshin girki."

Dariya Ameerah ta yi tana kallon ta.
"To jikamshi sarkin kwadayi."

"Allah kuwa da gaske nake Aunty. Hala dai ke ba ki ji kamshin ba?" Ta fadi tana sake daga hanci sama.

"Ina kuwa zan ji tunda ni na yi?" Ta tambayi Sumayyar tana bude mata hannu alamun ta zo su yi oyoyo.
Da sauri Sumayyar ta shiga cikin jikinta.

"Auntyna me kika girka mana? Allah kuwa yau ba zan ci abincin Ammi ba dan nata ba ya kalar wannan kamshin."

A daidai fitowar Ammi daga daki.
Dariya ta saki tana tafa hannuwa.
"Lallai auta wato ma abun haka ne ko? Ai kuwa daga yanzu abincin mai aiki za ki koma ci."

Dire-dire Sumayyar ke yi tana dariya.

"Yanzu Sumayya in banda rashin tausayi, kullum fa sai na dawo daga Office nake muku girki dan kar ku ci na mai aiki amma ashe ba ya kamshi ba son shi kike ba."

"Allah kuwa Ammi wasa nake yi."

Dariya suke su duka dakin. A daidai nan Saddam da Musaddiq suka shigo. Su kansu kamshin girkin ya shige su sai fadanci suke a wurin Ameerah amma ta yi mirsisi ta ce babu wanda zai ci shi har sai Ameer ya zo ya ci ya rage sannan su ci sauran.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now