Page 31

216 16 0
                                    


Page 31

***
B A Y A N S H E K A R A B A K W A I
***

Kwanaki kam tamkar suna rige-rigen tafiya ne, yayin da watanni suka yi tsere a tsakanin junansu. Kwanaki suna juyewa izuwa satuka, satuka na juyewa izuwa watanni, watanni suna shudewa izuwa shekaru.
Shekaru daya bayan daya har guda bakwai. Abubuwa da dama sun faru a cikin wadannan shekarun, wasu daga cikinsu na farin ciki ne, yayin da wasu suka kasance sai dai hamdala kawai.

Daga cikin na farin cikin su ne; kammala karatun Ameerah, ta zama lawyer mai lasisi, sai dai har yanzu babu batun aure, ba ta ba kowanne namiji damar tinkarar aurenta.
Bahijja ta yi aure, ta auri wani dan uwan mamanta mai hankali da nutsuwa, har da yaranta biyu. Habiba ma ta yi auren amma har yanzu ba ta haihu ba. Saddam da Musaddiq duk sun kammala karatu har sun samu aiki. Daddy ya zama director, Ammi ma ta samu promotion. Sumayya kuma ta gama secondary school har ta jona KASU inda take karantar Biology education.

Idan aka koma Canada kuwa, a nan ma an samu ci gaba. Maryam ta yi aure a Nigeria, duk da tarin gwagwarmayar da aka sha a lokacin auren, Daddy ya k'i amincewa sai da ta rinka saka manyan abokanshi da kyar ta samu ya amince. Labiba ta gama karatun likitanci tsawon shekara shida, tana housemanship wanda ake tsammanin za ta kammala shi a cikin kwanaki kalilan masu zuwa.
Ga baki daya raunukan Ameer sun warke. Kafar ma ta yi sauki sosai tuni an warware abubuwan da aka nade ta da su, sai dai kuma babu maganar tafiya, wheelchair dinshi ma Daddy ya sabunta ta.

Daga cikin abubuwa marassa dadi, akwai ci bayan da aka samu na bangaren larurin kwakwalwar Ameer. Duk yanda za su yi don ganin Ameer ya daina tunani sun yi amma abun ya faskara. Kalamai babu irin wadanda ba su yi amfani ba sai dai duk ba su yi tasiri ba. Ameer ya riga ya sanya ma kansa tunani tun daga sadda ya yi wannan mafarkin na Ameerah, kuma duk sadda ciwon nashi zai taso sai ya yi yunkurin kiran sunanta yana kasawa. Magungunanshi ma a maimakon a samu ragi, sai ma k'ara dosage dinsu da aka yi. Wanda yake shan guda biyu suka koma hudu, wanda yake shan guda daya kuma ya koma biyu. Sai dai a tsayin wannan lokacin, sosai yake samun kula daga wurina Labiba. Kamar yanda ta yi alkawarin dominshi za ta shiga karatun likitanci, hakan bai sanya ta rage ba shi kulawa ba duk da karancin lokuta da take da su, sai ma wani irin tausayinshi da ke k'aruwa a zuciyarta saboda ganin ciwon nashi ya k'i ci ya ki cinyewa.
Tunda suka shiga aji biyu ita ta koma yi masa allura duk sadda ciwon nashi zai tashi. Sai dai kamar yanda suka saba duk bayan wata daya ana mayar da shi asibiti domin karbar masa magani, da kuma duba yanayin brain din tashi.

***

Wani irin annuri ne a fuskarta, wanda tunda take a rayuwarta ba ta taba tsintar kanta a irin yanayin ba. A yau din nan ake musu induction, ta zama cikakkiyar likita.

Daga can gefe take zaune inda sauran dalibai ma suke, wanda mafi rinjayensu jajayen fata ne, sai tsirarun bak'ar fata.
Idanuwanta sai yawatawa suke yi ga family dinta da suke zaune wuri guda dukkansu cike da farin ciki, ciki kuwa har da Ameer, duk da ba dariya yake ba amma akwai shinfidadden annuri a saman fuskarshi.

Kyaututtuka ake kiran sunayensu ana ba su, tare da award ga wadanda suka cancanta. Manyan professors da masu matsayi a k'asar ne suka halarci taron, sosai suke yabawa da kwazon daliban.

A kiraye-kirayen da ake yi ne aka kira sunan Labiba Kabir Sardauna a matsayin best in medicine, best in surgery, and overall student.

Tafi sosai Daddy da su Aminatu ke yi, fara'a ba ta kau daga fuskokinsu ba. Dukkansu suka dunguma zuwa kan high table inda ake ba Labiba kyautuka da awards dinta, suna daukar ta hotuna. Ba a bar Ameer a baya ba shi ma
Leo ya tura shi suka karasa wurin.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now