Page 7

371 19 0
                                    

MATAR AMEER...(2021)

By Princess Amrah
NWA

Page 07

Da sallama ya shiga dakin Ibrahim, ya same shi shi ma din dawowar shi kenan daga wurin aiki. Bayan sun gaisa ya mika masa wayar nan karama tashi da ya yi ma wani irin nadi wanda duk iya kwakwar mutum ba zai iya sanin mene ne a ciki ba idan ba ya bude ya gani ba ne.
"Ibrahim don Allah ga wannan sakon amana, though ba nisa zan yi ba amma dai ka ajje min. Ina ji a jikina zai iya yi min amfani sai dai I don't know when and where. Don Allah Ibrahim try your best to keep it safe."

Cikin mamaki Ibrahim din ya karba yana sake dubawa.
"Amma dai lafiya ko Ameer?"

Da murmushi a saman fuskarshi ya ce
"Lafiya lau Ibrahim. Da yake da yau zan tafi gida to sai wani dan uzuri ya taso min wanda dole sai dai zuwa gobe. To idan na tafi gidan komai zai iya faruwa ciki kuwa har da barin aikina a AHC."

Bai daina mamakin kalaman da ke ratsowa ta tsakanin bakin Ameer ba. Sai kallon tuhuma da rashin gamsuwa da maganganunshi kawai da yake watsa masa.

"Kar ka damu ka ji. Just hide it and make sure ka masa irin adanin da kake ma budurwarka gudun snatching." Suka yi dariya duk su biyun.

Daga nan Ameer ya koma dakinshi ya yi wanka ya shirya cikin manyan kaya farar shadda da aka ma dinkin dogon kaftan, sai bakar hula, bakar agogo da bakin takalmi. Yana cikin fesa turare Mr Patric ya kira shi. Dauka ya yi cikin girmamawa.
"My Son ka shirya dai ko?"

"Eh na shirya Sir." Ya ba shi amsa a hankali.

"Am very happy zan yi tafiyar nan tare da kai. Ka san ban taba haihuwar namiji ba sai dai mace. So duk irin wannan abubuwan dole sai dai daga ni sai driverna ne muke yi babu wanda zan rinka gani yana debe min kewa. Shi ya sa nake ta jin dadi da Allah Ya jeho ka a cikin rayuwata. Am sure you will have fun there. Daga can har gidan gonata za mu wuce."

Ajiyar zuciya Ameer ya sauke, yana kankare duk wani mummunan zargi da yake cikin zuciyarsa. Nutsuwa yake jin tana saukar masa, tana ratsa duk wata kusurwa da ke cikin jikinshi. Wace irin soyayya ce Mr Patric yake masa?
'Haduwar jini.'
Ya tsinto amsar a can wani sashe na zuciyarshi.

"Zai zo ya dauke ka yanzu, ku hadu a bakin titi. Just make sure babu wanda ya sani."

Ji ya yi kamar ya fada masa ya ba Kamal labari sai kuma ya yi shiru, idan ya tambaye shi sai ya ba shi labari.

IPad dinshi ya dauka sannan ya leka dakin Ibrahim yake shaida masa ya wuce masallaci daga can zai dan dauki lokaci bai dawo ba. Fatan nasara ya masa sannan ya juya ya fice yana sauri.

Ya tarar ana huduba hakan ya sa ya kasa kunne yana sauraro kafin ya ji wayarshi ta yi ringing. Ya dauka a hankali yana shaida wa Mr Patric din yana masallaci an kusa tada sallah.

"Don't worry My Son ai ba zan hana ka ibadarka ba. Ka yi idan ka gama sai ka same shi a bakin hanya yana can yana jiran ka."

Murmushi Ameer ya yi yana masa godiya kafin ya yanke kiran.
Yana gamawa ana fara kokarin tada sallah.

***
Ameer ne zaune a gaban mota yayin da Mr. Patric ke bayan mota sanyi AC na shigarshi ta ko'ina. Shiga ce ya yi cikin black and white suits, katon cikin nan nashi ya yo gaba, wanda da gani babu wai ka san ana zuba masa ruwan barasa.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now