Page 32

216 16 0
                                    


Page 32

Bin ta da kallo Ammi ke yi tana kallon reaction dinta, kafin a hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta ce
"Ni fa ba ni da tabbacin maganar da zai yi miki kenan, ta yiwu wata ce daban, kawai dai nawa hasashen ne."

'Shi ne ma confirm.'
Ameerah ta fada a cikin zuciyarta. A zahiri kuwa shiru ta yi tana jin yanda gabanta yake tsananta faduwa.

Sallamar Daddy suka ji dukkansu, Sumayya ta mike tana karbar waya da jakar hannunshi hade da yi masa sannu da zuwa.

"Barka da dawowa Daddy."

Tana fadin haka ya gane ba ta a mood mai kyau, ga shi shi kuma maganar da yake son yi mata ya tabbata ba lallai ba ne ba ta ji dadinta.

Bayan ya zauna a saman sofa ya ce
"Ameerah, Boobah ta fada miki zancen ganin ki da nake son yi?"

Kai kawai ta daga masa kanta a sunkuye kasa tana jin yanda idanuwanta suke neman kawo ruwa.

"Good. Marwan zai turo iyayensa sati mai zuwa. Wai sun shirya don haka ba ma wani dogon lokaci za a dauka ba. Kuma na fada miki tun kwanakin baya cewa tare nake son hada ku ke da Sumayya. Don haka ya ake ciki yanzu? Kin sani mun ba ki dama da yawa Mamana. Girma kike yi, kuma su shekaru idan suka wuce ba dawowa baya suke yi ba. Ki fitar da miji zan duba nagartarshi in aurar da ke a gare shi."

Idanuwanta ta runtse da karfin gaske, wasu irin hawaye masu zafi suka rinka ketowa ta tsakaninsu.

"Ku yi mini hakuri Daddy, amma na dade da cire aure daga tsarin rayuwata..."

"What?"
Daddy ya fada a wani irin razabe. Duk da maganar ba sabuwa take ba gare shi, sai dai ya yi mamaki da har yanzu Ameerah take kan bakarta kan cewa ba za ta taba yin aure ba tunda Ameer ya tafi. Shekara bakwai kenan har da doriya, ita din wace irin zuciya ce gare ta wadda ba ta mantuwa?
"Haba Mamana, kar mu yi haka da ke. Mata da miji ma idan suka rasa abokan rayuwarsu hakuri suke su rungumi kaddara su yi aurensu, talkless of ke din da ba a ma riga da an daura muku aure da Ameer ba ya rasu..."

"Ina ji a jikina yana raye Daddy. Babu wanda ya ga gawarshi fa."
Ta tarbi Daddy cikin kuka.

"Kuma don ba a ga gawarshi ba shi kenan sai ya zama yana raye? Mutane nawa ne suke mutuwa ba a ga gawarsu ba kuma sun tafi din kenan? Allah Ya ba sojoji hakuri, ko in ce iyalansu. Mafi akasarinsu ba su ganin gawar mazajensu, sai dai labari ya riske su sun mutu har an binne su. Kuma hakuri suke su rungumi kaddara. Sai ke Ameerah? Shekara kusan takwas amma still kina nan kan bakarki? Wannan wace irin bak'ar zuciya ce? Wane irin mummunan tunani ne ki ce wai ke ba za ki yi aure ba? Ya kamata ki san me kike yi haka nan, ki farka daga wannan baccin da kike yi, ni ba sakaran uba ba ne, ba zan zira miki idanuwa ki yi abin da kike so ba. Iya hakuri dai na miki shi, na miki alfarma mai yawa da ban taba yi miki zancen aure ba tun bayan case din Haidar Makarfi. Don haka don't try me. Ba ki taba shiga tarkona ba tunda aka haife ki, kar ki ce za ki fara a yau. Sannan na ba ki sati biyu kacal ki fitar da mijin aure, idan kuma babu, ni zan ba ki, ina da tarin mutanen da suka jima suna nuna min kaunarki. Kuma har a gurin Allah ba ni da laifi idan na tirsasa ki sai kin daya daga cikinsu."

Daga haka ya mike cike da takaici yana barin dakin, kai tsaye dakinshi ya dosa, yana jin zafin fadan da ya yi wa Ameerah, wannan shi ne karon farko da ya taba daga mata murya tun bayan haihuwarta, bai ji dadi ba ko kadan, sai dai dole ce ta sanya shi yin hakan, don ya lura ko kadan Ameerah ba ta san ciwon kanta ba har yanzu.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now