Page 11

351 24 0
                                    


***
C A N A D A

"Daddy shi ne ka k'i dawowa jiya, ka ja Yaya Maryam sai dariya suke min, abincin da na maka ma sai dai a cikin fridge na saka shi."

Hannunta ya kama ya saka a cikin nashi.
"Am sorry Labiban Daddy. Halin nan naki da kike kara karfafar guiwata a kan aikata irinsa shi ne ya tsayar da ni."

"Daddy...?" Ta fada tana neman karin bayani.
"Taimako ka tsaya?"

"Shi na tsaya Labiban Daddy." Ya ba ta amsa yana mata murmushi.

"Allah Sarki. Ka kyauta sosai Daddyna."
Suka karasa cikin parlor. Bayan sun zauna ya ce,

"Ina Maryam da Mamana?"

"Yaya Maryam ta je School, Yaya Aminatu kuma tana gidan Aunty Aysha. Sai ni kadai a gidan."

"Me ya sa ba ki je ba ke?"

"Ina expecting dawowar ka yau ne Daddy shi ya sa ban je ko'ina ba. Kuma gobe za mu yi hutun School dama mun gama exams."

"Ma shaa Allah. Labiban Daddy fa an girma."

Murmushi ta yi tana fadin.
"SS 3 zan shiga yanzu Daddy. Na kusa gamawa in shiga University ni ma, su Yaya Maryam a daina yi mini kankamba."

Dariya yake yi, kai tsaye za ka fahimci cikin nishadin da mutumin yake.
"Our future journalist. Miss Labiba Kabir Sardauna."

Wani irin dadi take ji yana ratsa ta. Ta yi kewar mahaifin nata sosai, kwananshi takwas ke nan da tafiya Nigeria, amma tamkar ya yi wata haka take ji.
"Daddyna bari na maka warming abincinka. Ka yi wanka ka huta kafin na hada maka komai."
Ta fadi tana mikewa.

"Thank you so much 'yar Daddy." Ya fadi shi din ma yana mikewa.

Kitchen ta nufa ta bude fridge, chicken kabsa rice ce ta masa, don ta san shi sosai da son Arabian dishes. Ta juye a wata container sannan ta sa a microwave ta rufe. Fruits da ke ajje ta yayyanka ta hada fruit salad, sannan ta tace ruwan lemon zaki ta zuba a ciki, ta rufe ta sa a fridge.

Parlor ta koma, ta dauki wayarta tana kiran Aminatu.
"Yaya Aminatu yaushe za ki dawo?"

"Akwai wani abu ne?" Ta tambaye ta.

"Yes, Daddy is back. Kin san ba ya son zama daga ni sai shi a gida. Saukin ma dai Angelina ta dawo."

"Ga shi kuma Aunty Aysha za su yi tafiya ita da mijinta, ta ce ni za ta bar ma su Khairee."

"Ba sai ki taho nan da su ba tunda hutu za a yi duk schools gobe?"

"Yeah good idea. Bari in fada mata kawai, anjima sai mu taho tunda gobe ne za su tafi dama."

"Okay Yaya Aminatu. Bari in duba girki na ji ya kashe kanshi. Sai kun zo din." Ta yanke wayar tana nufar kitchen.

A cikin warmer ta juye abincin sannan ta dora a kan babban tray, ta dora bowl na fruit salad din sannan ta nufi dining area ta jera a kai. Ta dauko plate da spoon ta ajje, a daidai nan ta ji motsin Daddynta na fitowa.

"Yawwa an yi a daidai Daddy. Na gama shirya maka komai." Ta fadi tana sakar masa murmushi.

"Allah Ya yi miki albarka Labiban Daddy. Zama za ki yi mu ci tare ai dan na tabbata ke ma ba ki ci komai ba."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now