Page 38

220 13 0
                                    


Page 38

Cikin wani irin yanayi hade da rashin sanin yanda zai yi ya fuskanci Doctor Awwal da dukkanin nutsuwarshi, gabanshi bai daina bugawa ba, tsoro yake ji...tsoron sab'a alkawarin da ya daukar wa Mr Patric.
Ya dake, cike da rashin kwarin guiwa ya ce

"Yau zan fada maka dalilin da ya sa aka sallame ni aiki a kamfanin da nake, da kuma dalilina na k'in kowanne aiki idan ba kasuwanci ba."

Duk da Doctor Awwal bai ga mahadar tambayar da ya yi masa da kuma zancen da yake yi ba, ya zura masa idanuwa babu ko kyaftawa, ya matsu ya ji inda ya san Muhammad din.

"Sunanshi Ameer Nuraddeen, dan jihar Kaduna ne. Tare muke aiki da shi a AHC, gidanmu daya da ni da shi da Ibrahim..."

Ya kwashe komai da ya sani tun daga kan ajiyar da Ibrahim ya ba shi, har zuwa kai su da aka yi guesthouse din Mr. Patric, zuwa warning din da ya caskale masa da kuma ba shi umurnin ya same shi a Office, ya tura masa miliyan biyu bisa ga sharadin zai koma garinsu ya ci gaba da business, sai dai haka bai samu ba saboda hacking Bank account dinsa da aka yi.

Ga baki daya kan Doctor Awwal ya cushe, ya rasa gaba ya rasa baya, ya rasa madosar kalaman Sufyan.

"Har yau har gobe ban san dalilin da ya sanya Mr. Patric aikata mana haka ba. Mu uku ne ya kira, kuma kusan duk zance guda ne ya yi mana a kan Ameer, duk da ban ji me ya ce da sauran ba, sai dai na ga yanayin yanda Kamal ya fito, da kuma yanda aka fita da Ibrahim."

Nannauyar ajiyar zuciya Doctor Awwal ya sauke, cikin sanyin murya ya ce
"Yaya Mr Patric din yake? Ina nufin mutumin kirki ne ko na banza?"

"A da dai kallon na kirki nake yi masa, sai dai kora ta da ya yi daga aiki babu laifin tsaye babu na zaune sai na fahimci akwai mugun abu a cikin zuciyarshi. Duk da ban sani ba ko Ameer din ya masa wani abu ne, sai dai da mamaki, ta yanda ya ce in manta da Ameer da Ibrahim a duniyata."
Ya ba shi amsa cikin sarkewar murya.

"Shi Mr Patric din matsayin me yake da shi? Ko kamfanin nashi ne?"

"Gaskiya ba nashi ba ne. Na dai taba ji an ce na mace ne ma, AMAL, shi ya sa kamfanin ma yake da sunanta."

Shiru Doctor Awwal ya yi, kafin a hankali ya ce
"Hakuri za ka yi mu iske Alhaji da wannan zancen. Na tabbata akwai wani abu a k'asa. Yanda yake ba ni labarin ya tsinci Muhammad, hakan bai rasa nasaba da shi Patric din."

Cikin rawar murya Sufyan ke fadin
"Ni dai don Allah ka taimaka ka rufa min asiri mu bar zancen nan a nan, wallahi tallahi tsoro nake ji, tsoro nake kar a yi min wani abun."

Kafadarshi Doctor Awwal ya dafa, cikin kwantar da murya ya ce masa
"Ka kwantar da hankalinka Sufyanu, na tabbata Alhaji ba zai bari a cutar da kai ba, mutumin kirki ne sosai, wanda ya tsani zalunci ya tsani azzalumi. So please, mu juya mu koma ka yi masa bayanin komai, ta yiwu ta haka za a gano iyayenshi a damka musu yaronsu. Allah kadai Ya san halin da suka shiga tsayin lokacin nan na rashin shi."

Duk da haka dai hankalin Sufyan a tashe yake, zufa sai tsatssafo masa take yi. Ganin haka ya sa Doctor Awwal ya sake kwantar da murya, cike da ba shi kwarin guiwa ya ce
"Kada ka zamo raggon namiji Sufyan, kada ka shiga sahun masu taushe gaskiya saboda tsoro. Ka daure mu taru mu yak'i gaskiya, mu ceto yaron nan daga halin da yake ciki. Allah ne kadai Ya san ladar da za ka samu, Shi kadai Ya san rabautar da za ka samu, ta yiwu hakan ya zama silar shigarmu aljannah baki daya."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now