Page 6

397 24 0
                                    

MATAR AMEER...(2021)

By Princess Amrah
NWA

Page 06

Yana kwance a saman karamar katifa irin one person din nan, ya mayar da dukkan hankalinshi kan laptop yana latsawa, kiran Mr. Patric ya shigo masa. Da hanzari ya dauki kiran yana karawa a kunnensa.
"Hello Sir." Ya fada cikin girmamawa.

"Ameer barka da dare."

"Yawwa Sir, barkanmu."

"I hope dai gidan da aka samo you are comfortable. Dan so na yi a samo maka kai kadai shi ne Musa ya ce za ka fi jin dadi gidan da mutane suke, mutanen kuma ma'aikatan kamfaninmu."

"Eh Sir, na ji dadin haka sosai gaskiya. Da alama za mu yi zaman lafiya da su saboda duk mutanen kirki ne. Su biyu ne sai ni cikon na uku. Kuma kowa da dakinsa."
Ya ba shi amsa yana rufe laptop din tashi.

"Okay am glad Ameer. Akwai  shawarwarin da zan ba ka game da aikinka, wadanda su ne tsanin kowanne lucky naka."

Mamakin yanda Mr. Patric ya iya kalmasa Hausa kawai yake yi, ko wani Bahaushen ba zai gwada masa  iya sarrafa harshe ba.

"Ka dauke ni tamkar Babanka. Ni kuma zan ba ka kula sosai fiye da tunaninka. Now, have you eaten?"

"Yes Sir, na yi takeaway na fried rice da aka tashi daga Office. Yanzu ma na gama ci na hau duba wani abu a computer." Ameer ya fada yana mamakin karamci da mutuncin mutumin. A da yana kokwanto a kansa, sai dai yanzu, ganin yanda yake ba shi muhimmanci, ranarshi ta farko a Office tare suka rinka yawo yana gwada wa mutane shi a matsayinshi na wani mutum mai muhimmanci a gare shi, sai ya kawar da duk wani abun k'i da Ameer din yake ji game da shi. Ya dauke shi ya ba shi wani matsayi mai girma a duniyarshi.

"Kamar yanda na fada maka, zan ba ka wannan advices din but not now. Ka bari sai lokacin da aikin ya fara ratsa ka, ka fara bambance black and white a AHC, a lokacin ne ni kuma zan fada maka abubuwan da na tabbata za ka ji dadinsu. Understand?"

"Yes Sir." Ameer ya fada a zahiri, a badini kuma 'Me ya sa ba yanzu ba?' Yake tambayar kanshi.

"Fine. Bari in bar ka haka nan ka huta gobe akwai aiki. Try your very best to be the best person Ameer. I trust you ka ji, don't disappoint me."

"In shaa Allahu Sir." Ya fadi yana jin dadin maganganun mutumin da duka-duka bai yi wata guda da sanin shi ba, amma yake jin shi har cikin zuciyarshi, saboda yanda yake ba shi kulawa mai girman gaske.

"Mu kwana lafiya."

"Thank you so much Sir."

***

Cikin wani irin yanayi ta tsinci kanta, a zahirin gaskiya farin ciki da murna ne fal a zuciyarta, sai dai ta rasa yanda aka yi kunci ke gittawa ba tare da ta yi auni ba. Watanshi daya da sati biyu kenan da tarewa Birnin Kebbi, tunda ya tafi bai ziyarci gida ba, sai yau din nan da ya kira yake mata albishirin gobe da sassafe zai kamo hanya.

Daga shi har ita suka hau murna, suna hirar kalar farin cikin da za su tsinta yayin da suka yi arba da juna, duk da kusan koyaushe suna manne a video call, sai idan tana lectures, ko kuma shi din yana kan aiki mai tsanani.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now