Page 27

202 15 0
                                    


Page 27

Kamar yanda rayuwa ba za ta taba tafiya ba sai da numfashi, haka duniyar rubutuna ma ba za ta taba tafiya daidai ba sai tare da ke. Ke din ta musamman ce, tsani ce, sannan bango abun jingina a cikin duniyata. Na sadaukar da wannan shafin gare ki OUM NASS. Ina rokon Allahu Azza wa Jalla ya ci gaba da daafa miki a dukkanin lamurranki.

***

Bayan kwana biyu aka sallami Ameerah daga asibiti. Sai dai sosai likita ya cake musu warning a kan lura da yanayin Ameerah, don wata rana za ta iya rasa rayuwarta ga baki daya in dai haka na faruwa da ita.

Dukkansu mamakin ganin sauyin da Ameerah ta samu suke yi. Wannan rashin walwalar nata duk babu shi, wanda ya kamata a ce ma a yanzu ne take yin shi saboda rashin lafiyarta.

Tana kwance daki Sumayya ta shigo tare da shaida mata bak'i sun zo duba ta. Mamaki take ko su waye, saboda ita dai ba kawaye gare ta ba sai dai abokan karatu, sai kuma Sarah diyar Mommy Haneefa da ta kasance k'anwa, sannan kuma aminiya a gare ta.

Dankwalin kanta ta warware ta yafa shi. Fuskarta ta yi wani irin fayau, idanuwanta sun zurma sosai, sai dai hakan ba karamin kara mata kyau ya yi ba.

Tun daga kan bene take hangen Umma da Habiba, sai wata guda daya wacce ta juya baya ba ta gane ko wace ce ba.

Kanta a sunkuye ta zauna kasa.

"Sannu Ameerahna."
Umma ta fadi tana bin ta da kallon tausayi.

"Yawwa Umma. Ina kwana?"
Ta fadi fuskarta na sunkuye, hakan ce tsakaninsu da Umma koyaushe, tun Ameer na raye, ita ce mutum ta farko da take jin kunyarta.

"Lafiya lau Ameerah. Ashe jiki bai yi dadi ba. Ba mu sani ba wallahi sai dazu da safe ne Mahboobah ta kira take shaida min. Ban ji dadi ba da har sai da aka sallame ki sannan na sani."

Da murmushi a saman fuskarta ta ce
"Babu komai Umma. Ya jikin naki?"

"Na warware sosai."

"Aunty ina kwana?"
Habiba ta fada cikin girmamawa.

"Ameerah ashe daga tafiyarmu kuma sai rashin lafiya."
Bahijja ta fada cike da tausayi tana kallon Ameerah da duk ta fada cikin kwanaki uku.

"Na ji sauki Alhamdulillah."
Ta ba su amsa cikin sanyin murya.

"To Allah ya kara sauki."

Ta amsa da
"Amin na gode."

Umma ta ce
"Mahboobah ta ce min tana wurin aiki ko? Ashe ita ma tsautsayi ya hau kanta."

"Eh Umma, ni ma sai dazu ne take fada min ta yi banka. Amma yaron ya ji sauki sosai an ma sallame shi."

"To ma shaa Allahu. Allah Ya kara tsare gaba."

"Amin Umma." Ta fadi tana kallon Sumayya.
"Ki kawo drink kika yi zaune jiran sai an ce ki yi."

Da sauri Umma ta ce
"Wallahi da ta bar shi ma, wucewa za mu yi."

"A'a Umma ko ruwa dai ku sha. Je ki kawo Sumayya."

Mikewa ta yi ta ciko tray da ruwa da lemu, ki space din dora cups ma babu.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now