Page 13

304 22 2
                                    


***

Page 13

Bakar doguwar rigar roba ce a jikinta, ta yana babban mayafi ta dauki wayarta. A parlor ta samu mahaifinta zaune yana jiran ta.
"Daddy am sorry, na bar ka da jira ko?"

Murmushi ya yi yana mikewa tsaye.
"Babu komai Labiban Daddy. Mu je ko?"

"Okay Daddy. Yaya Aminatu bari mu je asibiti mu dawo. Ba za mu jima ba in shaa Allahu." Ta fadi tana kallon 'yar uwarta.

"Okay sai kun dawo. Daddy Allah Ya tsare." Aminatun ta fadi tana taka musu har zuwa bakin kofa.

Kai tsaye Excellent Health Care suka nufa. Bayan sun isa asibitin suka zarce Office din Doctor Farhan. Sun samu da mutane a ciki hakan ya sa Daddy ya ce su je su duba Ameer kafin nan ya gama da mutanen.

"Ya ji sauki Alhamdulillah. Na tabbatar da yanzu za ki iya ganin shi Labiba."

"Alright Daddy. Dama can fa zan iya, kai ne dai ba ka so in gani." Ta fadi tana murmushi.

"Abun ne babu kyawun gani. Da a ce kin gan shi a ranar da muka fara zuwa na tabbata ba za ki iya barci ba. Idan ma kin iya din to kina yi kina zabura. Raunukan sun munana sosai, ba na marmarin ko a mafarki in sake ganin irin su. Ban ma taba tsammanin zai tashi ba, haka nan dai na kai shi asibitin tare da hope din ya rayu, amma ko kadan ban kawo ba a raina zai ci gaba da rayuwa."

"Ai cuta ba mutuwa ba ce Daddy. Da cuta ce mutuwa da Mommyna ba ta tafi ta bar ni ba." Ta fadi cikin rawar murya, hawaye na niyyar zubo mata.

"It's Okay to ya isa haka." Ya fada dan ba ya so maganar ta yi nisa Labiba ta rikice masa.

Suna shiga dakin suka same shi a kwance, kafafuwanshi matse da karafa, sai dai idanuwanshi a bude yana kallon ceiling.

"Alhamdulillah! Sannu bawan Allah. Sannu, barka ka ji. Allah Ya kara maka lafiya, Ya kara tsare ka." Daddy ya fadi yana karasawa kusa da Ameer da ke binshi da kallo.

"Na san ba ka san ni ba. Ba ka san a inda kake ba. Na maka alkawarin ba zan taba cutar da kai ba, sannan zan tsaya maka a dukkan abin da kake so, idan ka zabi daukar fansa a kan abin da aka yi maka, zan tsaya a bayanka matukar kai aka zalunta ba zan kyale su ba, zan taya ka daukar fansa."

Shi dai Ameer bin shi kawai yake da kallo yana son sanin inda kalaman nashi suka dosa, sai dai bai sani ba. Hasali ma, bai san komai ba game da rayuwarshi ba. Bai san ko waye shi ba. Komai yake ji yana sabunta kanshi a duniyarshi.

Tunda suka shigo Labiba ta tsura masa ido tana kallon shi, wani irin tausayinshi ne ya tsirga zuciyarta. Ga shi kyakkyawa da shi, fuskarshi duk da raunukan da ke jiki amma hakan bai hana kwarjini ya bayyana kanshi ba. Ta taka kusa da shi tana kallon shi cikin ido, shi ma din ita yake kallo, yana jin sannun da take ce masa amma ya kasa amsawa, saboda bai san manufarta ba,  bai san me zai ce ba ya amsa mata.

"Ko wane ne ya maka wannan abun Allah ba zai bar shi ba. Ka bar su da Allah, da sannu zai maka sakayya." Ta fadi tana share hawaye.

Ganin haka ya sa Daddy ya kama ta, dama abin da yake gudu kenan. To da a ce ta gan shi tun farko ya za ta ji kenan? Wani irin raunin zuciya Labiba gare ta. Tana da matukar tausayi wanda shi kanshi gani yake ta zarce shi. Sai dai ba abun mamaki ba ne, saboda mahaifiyarta ma haka take, sai shi ma din haka yake. Shi ya sa da Labiba ta tashi gadon ma sai ta zarce su.

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now