Page 50

264 11 0
                                    

Page 50

Sai bayan la'asar sannan Ameer da Khalil suka zo daukar Ameerah. Abinci ta fara gabatar musu, Ammi ta ba su wuri don su sake sosai.
Suna cikin ci Saddam ya shigo.
Ganin su ya sanya shi karasawa inda suke, bayan sun gaisa suka masa sannu da dawowa shi kuma ya wuce Dining ya zuba nashi abincin.

Wuraren shida na yamma suka gama. Ameerah ta shiga dakin Ammi ta same ta tana waya, sai da ta gama sannan ta ce
"Ammi wani aiki ne ya taso min, amma kafin nan ina bukatar albarkarku a ciki ke da Daddy."

Ammin ba ta yi mamaki ba, saboda kusan duk aikin da Ameerah za ta yi ba tun yanzu ba sai ta fada musu don su taya ta da addu'a. Sai dai abin da ya daure mata kai komawa aikin da za ta yi bayan kuma hutu take yi.

Fahimtar tunanin da Ammin ke yi ya sanya ta ce
"Ba yanzu za a fara shari'ar ba, kawai dai zan yi kokarin fara bincike ne tun yanzu. A kan abin da ya faru da Yah ameer ne."

Ido Ammin ta zaro da mamaki ta ce
"Ameerah me ya sa zancen da ko iyayensa ba su tayar da shi ba ke za ki kokarin jefa kanki a ciki?"

Guntun murmushi Ameerar ta yi don ta san dole za a yi haka dama.
"Ammi ba lallai don sun yi shiru ba ni ma in yi, saboda ba aikinmu iri daya da su ba. Ta yiwu suna shakkun d'aga zancen ne, ni kuma alkawari na daukar ma k'asata cewa zan kare hakki da martabar kowa gwargwadon ikona. Kuma ko ba a kan Yah Ameer abun ya faru ba zan jajirce don ganin an kama ko su waye suke da hannu a cikin lamarin. Barin irinsu shi ke kara jawo tabarbarewar k'asarmu. Shi ya sa babu wani ci gaba har yanzu a Nigeria. Ana barin 'yan ta'adda suna ci gaba da zuba iskancinsu yanda suke so. Tsoro na sanya wasu daga cikinmu suna ji suna gani a zalunce su amma su rasa bakin magana. Wasu daga cikinmu kuma rashin gata da galihu, rashin masu tsaya musu ne yake jawo haka, yayin da wasu ke amfani da wata baiwa da Allah Ya yi musu ta kudi ko mulki suke taka mutane yanda suke so. Don Allah Ammi kada ki hana ni yin wannan aikin, albarkarku kawai nake nema."

Daddy ne ya karasa shigowa dakin duk ya ji maganganunsu. Da sauri Ameerah ta sauka kasa ta gaishe shi, ya amsa mata da sakin fuska sannan ya ba ta izinin zama kan gado.

"Duk na ji maganganunki Ameerah, na kuma goyi baya dari bisa dari. Ina fatan Amminki ma za ta goyi baya tare da dukufa yi miki addua dare da rana."

Murmushi Ameerah ta yi tana kallon mahaifin nata cike da kauna da tarin kewarshi da ta yi.

"Na gode sosai Daddy."
Ta fada tana kallon shi.

"Fatana dai za ki bi komai a sannu, saboda idan ba ka iya kama barawo ba shi zai kama ka. Kodayake da Barrister Ameerah Ishraq nake magana."
Ya karasa maganar yana fadada dariyarsa.

Ajiyar zuciya Ammi ta sauke, kafin cikin sanyin murya ta ce
"Ba wai amincewa ce ba na son na yi ba, kawai na tsorata ne da yanda Daddy ke labarta min lamarin ne. Duk da yanayin da aka ce an same shi amma iyayenshi ba su kawo zancen daukar fansa ko wani bincike ba, sai ke Ameerah, ina gudun kada wani abu ya same ku ke da Ameer din duka."

Hannuwan Ameerah duka biyu ta dora a saman cinyoyin Ammi, cikin kokarin kwantar mata da hankali tare da ba ta kwarin guiwa ta ce
"Ammi please ki daina maimaita wannan maganar. Let's say ma sun yi shirun, Ammi ni ba ni da damar d'aga zancen? To balle ma tana iya yiwuwa tunanin makomar zancen ce bai zo musu a rai ba. Kin ga yanzu idan muka yi shiru da maganar, su wadancan mutanen da suka masa aika-aikar da zarar sun gane he is still alive za su iya sake yunkurin cutar da shi ko don gudun tonuwar asirinsu."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now