Page 15

272 15 0
                                    


***
Page 15

Duban shi ya yi a tsanake, fuskarshi cike da fara'a ya ce
"Abokina ya sunanka?"

Kallon shi kawai Ameer ke yi dan bai san abin da yake nufi ba.

"Ba ka iya magana ko? Sorry. Zan rinka kiran sunaye, idan na zo kan naka sai ka daga min kai." Duk yana yi ne ba wai dan yana da tabbacin Ameer din zai iya ba, sai dai idan yana samun ire-iren wadannan abubuwan to wata rana za a wayi gari yana catching.

"Abubakar? Umar? Usman? Aliyu?" Duk sunan da ya fadi sai ya kalli Ameer din amma ba ya ganin canjin wani yanayi a tattare da shi.
"Sulaiman? Hafiz? Ibrahim? Shamsuddeen? Ahmad? Mahmoud? Yusuf? Saleem? Tahir?" Haka ya rinka zayyano masa duk wani suna da ya sani sai dai kallo kawai da Ameer yake bin sa da shi.

"Ni ka ga sunana Awwal. Sunan babana Muhammad. Ina da yayye maza biyu, Sagir da Munir. Sannan kannena uku duka mata. Zainab, Hafsat, da kuma Zakiyya. Suna kirana da Yaya Awwal. Ina da mata daya sunanta Hindatu. Ina da yara uku Muhammad ne babba muna kiran sa Hammad, sai Fatima da Safiyya. Ni dan asalin jihar Zamfara ne, a karamar hukumar Tsafe. A nan k'asar na yi karatuna kuma na samu aiki a nan saboda kyakkyawar sakamako da na fita da shi. Iyalina ma a nan suke sai dai mahaifana ne da har yanzu suna can Tsafe. A bangaren abinci na fi son namu na gargajiya kamar su danwake, tuwo, dambu da sauransu. Sai abun sha ina son lemon kwakwa. Ina son kalar blue ko a kayana ma sun fi yawa kalar. Ina son football sosai though ban iya ba amma ba na missing kallon favorite club dina Manchester United. Ina son friendship da mutum mai shiru-shiru wanda magana ba ta dame shi ba, shi ya sa ina ganin ka kawai na ji sha'awar ka zama friend dina. Ai za ka amince ko?" Ya kalli Labiba da ta tsura musu ido tana kallo.

"Abincinshi ne wannan?" Ya tambaye ta.

Kai ta daga masa.
"Yawwa miko shi nan, ni da kaina ma zan ba abokina abinci." Ya karbi takeaway din da take miko masa.

Budewa ya yi ya zaro spoon din,
"Amma yana da bukatar ruwan zafi dan ya warware masa hanji. Ko ya sha?"

Kai ta gyada masa.
"Bai kamata ya ci wannan ba ai ba tare da ya warware hanjinshi ba. Cikinshi zai iya yin ciwo. Dauki cup ki je jikin water dispenser din da ke reception ki matso ruwan zafi. Ina ji ba za a rasa sugar da teabag a office dina ba." Ya fada yana mikewa.

Ta nufi reception shi kuma ya je Office dinshi ya dauko, yana dawowa ya tarar ita ma din ta dawo. Da kanshi ya hada masa shayi ruwan bunu, sai da ya tabbatar ya dan fara hucewa sannan ya matsa kusa da shi da kujerarshi ya zauna.
"Yawwa abokina haa bakinka ka sha ruwan zafi."

Bai gane abin da yake nufi ba har dai ta ya nuna masa da bakinshi ya ce
"Haa!" Ya bude.
Shi ma bude nashi ya yi yana kallon shi.
"Yawwa abokina to karba ka sha." Ya zira masa cokalin shayin a baki.
Ya sake diba ya ba shi ya sha, daga haka har sai da ya shanye shayin duka, yana jin wani irin dadi a cikinshi.

Abincin ya koma ba shi a hankali yana karba, har sai da ya ji cikinshi ya cika. Bai san ya zai yi ya san ya koshi ba, sai dai yanayin yanda ya koma taunar abincin ya tabbatar wa Doctor Awwal cewa ya koshi.

"Yanzu za ka ji har jikin naka ma ya kara yi maka dadi." Ya kalli Labiba yana fadin
"Gobe ma haka za ki yi masa. Kar a rinka barin shi da yunwa. Drip din nan a bar shi ya huta da shi, ji ki ga yanda hannunshi duk ya kumbura."

Kai ta jinjina masa. Ita kam mamaki ma likitan yake ba ta. Kamar ba likita ba, sai wadansu abubuwa yake yi sai kace zararre.

"Abokina, zan dawo da daddare mu karasa hirarmu. Ka ga yanzu zan je duba wani patient din." Sannan ya mayar da kallon shi ga Labiba.
"Kin ga yanda kika ga ina sakartar da kaina din nan a wurinshi? To haka za ku rinka yi. Kuke masa hirarraki masu dadi, ko da wasa kuma kar ku sako wani abu da ya shafi tashin hankali dan kwakwalwarsa ba za ta iya dauka ba. Haka zalika kar ku bari ya gani ko da kuwa a kallo ne. Kafin ku bar asibitin nan ki tabbata na ba ki shawarwari da hanyoyin da za ku zauna da shi. Da izinin Allah sannu a hankali komai zai dawo masa. Sai dai kin san Hausawa sun ce tafiya sannu-sannu kwana nesa. So ba dole sai yanzu ba, ba dole sai cikin shekarar nan ba, ba ma dole sai cikin shekara ta gaba ba. Sai dai dukkanmu nan Allah Ya fi mu iyawa. Idan Ya so a gobe ma kina iya ganin Ya warware masa duk matsalar. So ba dubararmu kadai ba ce mafita, sai an hada da addua, sannan da sadaka, in da yanda za a yi ki koya masa tasbihi da istighfaar, ko su kadai ya rinka maimaitawa, Allah Yana ji kuma Yana gani, a hankali zai ba shi lafiya."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now