Page 14

316 14 0
                                    


***
Page 14

Ba su wani sha wahala ba wurin ganin likitan k'ashi saboda refer ne. Kai tsaye likitan ya hau duba shi, aka yi hoton kafafuwan da duk wani abu da ya dace. Ba karamar illa aka yi wa kafafuwan ba. Babu ma ta yanda za a yi su iya mikewa saboda wasu kasusuwan ma rugu-rugu aka yi musu.

"Kafafuwanshi sun yi illatar da babu abin da zai iya sanya su gyaruwa, domin kuwa an karairaya masa kasusuwa, har gwara ma kafar damar, domin ita ba ta fi karaya uku ba, ta haggun kuwa babu inda babu karaya. Don haka ni dai zan ba shi magunguna, sai dai wadannan magungunan ba su za su sanya shi mikewa ba sai dai zai samu sauki, sannan idan an kiyaye su za a iya samun nasarar ya samu sauki. Za ku saya masa keken guragu wanda zai zama mataimakinsa, daga yanzu har zuwa karshen rayuwarsa."

Kai kawai Alhaji Kabir ya dafe, yana sauraron maganganun likitan da yake yinsu cikin harshen Turanci. Kenan dai da gaske shikenan ya zama gurgu? Ji yake tamkar ya yi masa kuka. Ya kalli gefen da Labiba take ya ga yanda ta zabga uban tagumi tana hawaye.

"Allah Ya sa hakan shi ne mafi alkhairi." Ya furta yana mikewa. Daga nan ya wuce wurin neurologist din.

"Kai tsaye ba zan ce ga abin da yake damun shi ba sai dai hasashe. Dementia ne confirm, sai dai wane iri? Dole sai an yi hoton kwalwarsa. CT scan nake tunanin a yi, kodayake, a yi MRI scan,  ya fi bayyana komai fiye da CT scan. Saboda ko an yi CT din ba lallai a ga wani abun ba, dole dai sai an yi MRI din, don haka za a yi shi daga nan zuwa gobe, ina da tabbacin za a gane matsalarshi ta nan."

"Okay Doctor. Thank you so much." Daddy ya fada yana mikewa. Fatanshi dai Allah Ya sa ciwon ya zo masa da sauki. Akwai wani abokinshi da dementia ta kama shi, shi kam hauka ma abun ya zame masa, accident ne ya yi kanshi ya bugu ashe dementia ya shiga, tun daga nan sai hauka tukuru. Shi ya sa ya tsorata lokacin da Doctor Farhan ke shaida masa abin da ke damun yaron.

Dakin da Ameer yake suka koma. Daga gefenshi Daddy ya zauna yana kallon shi cike da tausayi.
"Sannu Muhammad. In shaa Allahu za ka samu lafiya."

Bai iya fadin komai ba Ameer din sai hawaye kawai da suke sauko masa. Ya gane cewa da shi yake magana. Amma me zai ce? Wace kalma zai fadi? Gyada kanshi kawai yake yi, yana jin hawayenshi suna tsananta.

Kusa da shi Labiba ta dawo, har ta kai hannunta za ta kama shi sai kuma ta fasa, ba muharraminta ba ne, don haka akwai iyaka a tsakaninsu. Idanuwanta a cikin nashi, ya yi saurin janye nashi yana kokarin shanye kukan da yake yi sai dai abun ya faskara.

"Sannu..." ta fadi cikin kuka, tana dorawa da
"Cuta ba mutuwa ba ce. In shaa Allahu sauki zai zo gare ka. Allahn da Ya halicce ka bai manta da kai ba. Akwai tanadi mai girma da yake yi maka. In shaa Allahu ko nawa ne Daddy zai kashe don ganin ka samu lafiya. In dai ka ga ba ka samu ba to lokaci ne bai yi ba." Ta kokarta shanye kukanta, tana sakar masa murmushi alamun kwarin guiwa ne take ba shi.

"Ina ganin ai mu tafi gida ko Labiban Daddy? In ya so gobe sai mu dawo. Na tabbata za su kula da shi yanda ya dace a nan. Kuma nurses da kansu suke zuwa su ba shi magani."

"Zan zauna tare da shi Daddy. Irin wannan larurin ba ya son kadaici. Ka ga a haka ma kuka yake yi, idan an bar shi shi kadai tunane-tunane za su yi masa yawa."

Shiru Daddyn ya yi yana nazartar kalamanta. Gaskiya ta fada. Sai dai kuma ya za a yi tana mace ya barta ta yi jinyar namiji?
"Labiba ki yi hakuri mu tafi, in ya so da sassafe sai ki zo. Ki rinka zuwa ki wuni har zuwa sadda za a sallame shi. Kin ga bai kamata ki kwana a nan ba."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now