Page 44

223 16 0
                                    


Page 44

Sai bayan sallar jumu'a sannan suka dunguma cikin motar Doctor Ashraf, Ameer ne zaune gidan gaba sa Daddy da Labiba a baya, dukkansu sun yi shiru kowa da bikin zuciyarshi.

Horn ya yi a daidai kofar gidan su Ameer din mai gadi ya bude gate, kasantuwar sabon mai gadi ne ba asalin wancan nasu ba ya sa bai san Ameer ba, sai dai ya san Doctor Ashraf tunda yakan zo wurin Daddy shi ya sa babu haufin komai ya bude masa gate din suka shiga ciki.

Bayan ya daidaita parking ya dauki wayarshi ya latsa kiran Abba, a take ya dauka.
"Allah dai Ya sa kana gida, na zo kuma ban ga motarka ba."
Doctor Ashraf ya fada cikin sakin fuska.

"Ina gida kuwa, motar ce ke dan fitar da farin hayaki shi ne na sa Khalil ya kai a duba min ita. Kuma ka taki sa'a don yanzu na baro wancan gidan."

"To Alhamdulillah. Ga ni nan shigowa."

"Okay."
Abba ya fada hade da yanke kiran.

Da taimakonshi Ameer ya sauka, ita dai Labiba biye take da su ta kasa fadar komai, tana jin yanda Daddy da Doctor Ashraf ke ta hirar farin ciki har suka karasa isa bakin kofar da za ta sada ka da cikin gidan.

"Ameer ka dan jira mu a nan, sai mun yi magana tukunna zan fito in shiga da kai."

Kai kawai ya jinjina ma Doctor Ashraf yana sake yawata idanuwanshi a cikin gidan nasu da ya canja sosai, an yi gyare-gyare kamar ba shi ba.

Da sallama suka shiga, sun samu Abba daidai yana fitowa parlor sanye da light brown din jallabiya.
Ganin Doctor Ashraf tare da bak'i ya sanya shi fadada murmushinshi yana musu sannu da zuwa.

"Barka da rana Alhaji."
Daddy ya fada yana mika masa hannu suka gaisa.

"Yawwa barkanmu. Sannunku da zuwa."

"Yawwa."

Labiba ta duka har kasa ta gaishe da Abba ya amsa mata da sakin fuska. Da kanshi ya tashi ya jero ruwan faro bisa tray sannan ya dora glass cups guda uku.
A kan center table ya ajiye yana sake fadin
"Sannunku fa."

"Sannu da kokari abokina."
Doctor Ashraf ya fada yana murmushi.
Sannan ya dora  da
"Na san dole za ka yi mamakin gani na tare da BAKUWAR FUSKA, ko in ce bakin fuska."

"Gaskiya ne."
Abba ya fada yana kallon shi.

"Bari dai in tafi to the straight point. Wannan bawan Allah'n sunanshi Alhaji Kabir Sardauna, wannan kuma sunanta Labiba diyarshi ce. Shi ne wanda ya tsinci d'anmu Ameer a cikin halin rayuwa ko mutuwa, kusan shekaru takwas da suka gabata. Shi ya kai shi wurina na ba shi taimakon gaggawa duk da ba mu kawo a ranmu cewa zai rayu ba, to sai Allah Ya nuna mana iyakarmu. A lokacin ban gane shi ba gaskiya, saboda fuskarsa ta dame sosai, jina-jina baya ga tarin raunukan da ke jikin fuskar. Ni na ba shi shawarar ya canja tsarin tafiya kawai ya tafi da shi, kasantuwar ba a nan Nigeria yake zaune ba, Canada yake zama sai dai yana dan zuwa Nigeria ne saboda  businesses dinshi."
Ya dan tsagaita daga nan, yana kallon yanda Abba ya yi mutuwar zaune, ya kasa ko da kyafta kwayar idonshi.

"Duk tsayin lokacin nan Ameer yana raye, yana karkashin kulawar bayin Allah'n nan. Sai dai yanayin jikinshi ya sanya shi jimawa a asibiti, kasantuwar dementia da ta kama shi wadda ta sanya ya mantawa da ko shi waye, ya manta da rayuwarsa ta baya ma kwata-kwata, sai kwatsam..."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now