Page 70

565 20 1
                                    


Page 70/epilogue

Washe gari Ammi ta ci gaba da shirya 'yarta da kyau. Komai na gargajiya take yi mata ba saye take yi ba. Bazarkwaila, kanumfari, minannas da danyar citta ta dafa su sosai sannan ta tace ta sa a fridge Ameerah ta mayar da su tamkar ruwan shan ta. Sannan ruwan da take tsarki ma kanshi hade haden ganyen magarya, ganyen lalle, da kanumfari ne, idan ma sun huce to sai ta yi warming tunda a cikin butar karfe ne. Ita kanta Ameerar sosai take jin dadin jikinta. Sannan kullum idan za ta yi wanka da garin lalle take amfani hakan ya sa skin dinta ya dan sauya zuwa wani irin jaja-jaja mai kyau da daukar ido. Fatar tata ta yi santsi sai dadin tabawa.

Ranar da ta cika sati daya ana mata gyara ranar ne Ameer ya zo ya tafi da matarshi, driving yake yi amma hannunshi na kan fatarta saboda dadin tabawa da yake ji.

A wannan daren raba shi suka yi suna soyayya. Sosai suke nuna ma junansu yanda suka yi kewar kansu. Ameer sai albarka yake shi ma Ameerah saboda yanda yake ji tamkar a yau ne ya fara sanin ta. Sai wuraren biyu na dare sannan suka yi bacci.

Kwanan Ameerah biyu da dawowa kuma suka hau shirin tarewa Birnin Kebbi. Duk wasu kaya nasu sun tattara su an yi gaba da su saboda su a jirgi za su tafi. Daddy kuwa cike yake da farin ciki saboda ziyarar da Maryam ta kawo masa ita da mijinta da yaransu biyu. Da yake Lagos suke shi ya sa ba su samu zuwa a wancan karan da aka zo da Labiba ba.

Sai da Ameerah ta fara zuwa wurin sunan Bahijja da ta haifi saurayi da yake ba tashin wuri za su yi ba sai bakwai na yamma.
Daga gidan sunan ta wuce gidan Sumayya da ke da tsohon ciki ta mata sallama sannan ta wuce gidansu a lokacin karfe biyar da rabi. Ba ta wani jima ba sosai Ameer ya zo ya dauke ta suka tafi gidansu. Daga can kuma Khalil ya kai su airport.

***

Tunda Saddam ya yi wa Musaddiq zancen Fauzah ya gagara gane halin da yake ciki. A kullu yaumin tunanin yarinyar yake yi. Ko abinci yake ci murmushinta yake hange. A yanzu kam ya fara gasgata cewa son Fauza yake yi, so kuma mai tsanani. Sai dai bai san ta inda zai fara ba. Bai san komai ba game da soyayya saboda shi bako ne a harkar. Yana son tinkarar Saddam ya neme shawararshi tunda shi ba wasu abokai ne da shi ba amma yana tsoron tsokanar da zai rinka yi masa. A karshe dai daurewa ya yi Saddam na daki ya same shi. Yana ganin fuskar Musaddiq ya gane akwai wani abu tafe da shi. Tashi ya yi zaune ya ce

"Ya dai dunkum? Akwai damuwa ne?"

"Eh Yaya."
Ya ba shi amsa a hankali.

"Ina jin ka."

"Dama...uhm...a kan zancen yarinyar nan ne..."
Ya kasa karasawa.

Dariya Saddam ya dauka da karfi yana tafa hannuwa.
"Iyyyeee kar dai hasashena ya tabbata Musaddiq? Kai madalla. Ni fa wallahi ban sani ba da niyyar sharri kawai na yi..."
Ya kasa kai karshen zancen nashi saboda dariya.

"Ni dai ba wannan ba Yaya. Ban san yanda zan yi ba. Kome nake ita nake tunani. Kuma ni ban san yanda zan yi ba."

Cikin dariya Saddam ya ce
"Ka kuwa kawo matsala inda za a warware maka ita yaro. Yanzu dai bari in sa Khadija ta turo min lambarta. Idan ta turo sai ka kira. Da farko ka fara da gabatar mata da kanka, daga nan kar ka tsaya wani jan lokaci kawai ka isar mata da sirrin ruhinka. Na tabbata Fauza ba za ta k'i handsome guy din nan na gabana ba."

Murmushi Musaddiq ya yi yana jin dadin shawarar yayan nashi.

A take kuwa Saddam ya kira Khadija ya ce ta turo masa lambar Fauza. Bayan ta turo ya karanta ma Musaddiq sannan ya ce
"Ba ta gama secondary ba ina ji SS 2 take. Ka ga sadda za ta gama kai ma ka shirya. Daga nan sai kawai mu sha biki. Na san kila a lokacin Beebahna na dauke da ciki na biyu."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now