Page 34

209 16 1
                                    


Page 34

Kanshi ya jinjina alamun da gaske yake babu wasa a cikin maganarshi.
"Aunty mu za mu tsaya miki don ganin ba a aura miki Yaya Junior ba tunda dai ba ki son shi. Ina dalilin auren had'i, ai tuni an wuce wannan zamanin. Shi ma kanshi na tabbata ba sonki yake yi ba, kamar yanda aka yi miki haka aka yi masa."

Murmushi ta saki mai hade da hawaye.
"Kada ka shiga wannan maganar Musaddiq, tsakaninmu ne ni da iyayena. Ni na amince, na yarda zan aure shi ba don ina son shi ba, sai don biyayyar iyayena. Ko ka manta addini ya ba da izinin iyaye su zaba wa 'ya'yansu mazan aure?"

Ya gyda kanshi Musaddiq yana dafa ta.
"Ban manta ba Aunty, sai dai mu ma muna da hakkin da idan muka ga wani abun k'i yana tinkararki mu yi kokarin kare ki."

"Auren Yah Junior din ne abun ki?"
Ta yi gaggawar tambayarshi.

"Abun k'i ne mana tunda bakya son shi ba ya son ki Aunty. Kowacce mace tana da burin ta auri wanda take so yake son ta, kamar yanda a bangaren namijin ma haka ne. To me ya sa ke kike son jefa kanki a dawwamammiyar rayuwar da ba za ki riski farin ciki a cikinta ba?"

Ta gyada kanta idanuwanta cikin na Musaddiq,
"Ina da yakinin zan samu farin ciki a gidan Yah Junior. Mahaifinshi aminin mahaifinmu ne tare muka gan su. Sannan Yah Junior yana da tarbiyya, yana da ilmin addini, ya yi zurfi a ilmin boko. Babu tab'ewa a aurenshi. Duk da ba na son shi ba ya so na hakan ba yana nufin za mu yi zama irin na makiya ba ne."

Shiru ne ya ratsa a tsakaninsu, kafin Ameerah ta dora da
"Mutum ba ya da zabi a kaddararshi, da a ce kowa shi yake zaba wa kanshi kaddarar da za ta riske shi da ban tsara ma kaina nisanta daga Yah Ameer ba, da tuni muna dinke a duniya guda ni da shi, mun zama itaciya guda mai rassa. Sai dai ina! Allah Shi yake tsara wa bawa kaddarar da Yake ganin ita ta fi cancanta da shi. Don haka na karba da hannu bibbiyu. Allah Ya fi ni sanin abin da ya dace da ni da rayuwata."

"Kada ki cuci kanki Aunty..."

Ta yi saurin tarar numfashinsa,
"Idan har Daddy da Uncle ba su cuce ni a kan zaba min auren Yah Junior ba to karbarshi ba zai zama cutuwa a gare ni ba. Ka kwantar da hankalinka Musaddiq, Allah ne Ya tsara rayuwata a haka, da ma sau da yawa bawa yakan tsara ma kanshi rayuwa ne sai dai yana nashi Allah kuma na Nashi, na Allah kuma shi ne na gaskiya. Haka Allah Ya kaddaro zan karaci rayuwata ni kuma. Idan ka tuna tun daga tashi na har zuwa girmana ban taba samun tangarda ba, komai yana zo min ne straight babu kwana-kwana. To a haka bawa zai ci gaba da tafiya babu jarabawar rayuwa? A'a! Sai Allah Ya tsara min rabuwa da Yah Ameer, sannan Ya zuba min kewarshi fiye da komai na duniyata. A karshe kuma Ya kaddara min auren wani wanda ba shi ba. Na karba...na karba Musaddiq, zan auri Yah Junior, kawai ku taya ni da addu'a Allah Ya sassauta wa zuciyata kar ta buga, Allah Ya ba ni ikon yarda da shi a matsayin mijin aure na."

Duk dakiyar Musaddiq sai da ya zub da hawaye, magana Ameerah take yi cike da rauni, damuwa na bayyana kanta da kanta a saman jikakkiyar fuskarta. Saurin share hawayenshi ya yi, ba ya so ta ga gazawarshi, so yake ya ba ta kwarin guiwa, sai dai yanayinta da komai yana kashe masa jiki, hakan ya sanya shi dafa kafadarta, cikin sanyin murya ya ce
"Aunty tunda kin san cewa taki kaddarar ce ta zo da wannan salon me ya sa za ki rinka yi mana asarar hawayenki? Ki daure, na san dole da zafi da ciwo, amma tunda har Ammi ta aminta da zancen nan to ta san babu aibu a ciki ne. Idan kin tuna a can shekarun baya ita da kanta ta nuna rashin gamsuwa da aurenki da wannan yaron dan gidan Makarfi. Ta tsaya tsayin-daka wajen ganin Daddy bai tirsasa miki aurenshi ba, kuma ta yi nasarar hakan. A yanzu kuwa da ta aminta da zancen, hakan na nunar da cewa ta san za ki tsinci farin ciki a gaba ne."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now