Page 62

185 8 0
                                    


Page 62

Sai dare sannan suka isa Kaduna. A gajiye suke lis shi ya sa wanka kawai suka yi suka kwanta. Washegari da safe Daddyn Labiba ya kira Ameer bayan sun gaisa ne yake tambayar sa yanda aka kare a kotu. Ameer ya labarta masa duka har binciken da suke kan yi a yanzu.

"Allah Ya sa a dace. Tabbas mugu bai da kama Ameer. Yanda Patric yake da mutunci ban taba tsammanin haka halinsa yake ba. Kodayake dama ba ka cika gane true colour din mutum musamman ni da ba kasar nake ba."

"Haka ne Daddy, ko ni ma kaina na jima ina mamaki saboda karamcinshi, ya ja ni a jiki sosai farkon zuwana AHC. Sai dai kuma a yanzu ne nake ta tuna wadansu abubuwan; yanda ya matsu in yi aiki a kamfanin, ko ni ko mahaifina ba mu kai shi matsuwa da aikin ba. Tsabar yana so in yi aikin fa har cewa yake wai akwai karancin masu irin karatuna a kamfanin, da na bincika aka ce ai sun ma fi kowa yawa. Na yi ta tunanin dalilin da zai sanya shi yi min karya amma na gaza gano komai. Ashe yana son ja na a jikinsa ne don ya kassara rayuwata."

Daddy ya ce
"Ai ka raba kanka da mutanen wannan zamanin, ba kowa yake zama da kai da zuciya daya ba. Kuma ni wani abu daya da yake ta yi min yawo shi ne, wai me ka yi wa Mr Patric ne da ya sanya a kashe ka? Wane dalili ne zai sanya shi jan ka a jiki don kawai ya ga bayanka?"

"Tambayar da nake ta yi wa kaina na kuma gaza gano amsarta kenan Daddy. Sai dai ina tunanin zuwa wurin Abba, ya yi tunani da kyau ta yiwu ko akwai wata boyayyar tsama a tsakaninsu wadda ta sanya shi daukar fansa a kaina."

"Gaskiya dai ba za a rasa ba. A ce duk mutanen da ke cikin kamfanin nan sai kai kadai ne zai sa a kashe? To kuma kai ba ka tsinci wani sirri nashi da ba ya so a sani ba wanda ya sanya shi daukar mataki a kanka?"

Ameer ya dan yi shiru alamun tunani, kafin ya ce
"Ta iya yiwuwa akwai amma na manta Daddy. Ka san ba komai ba ne ya dawo min, sai dai a hankali nake ta tunawa da wadansu abubuwan. Zuwan mu wurin Kamal jiya ya tuna min da wasu abun, kamar cewar da ya yi za mu yi tafiyar sirri kar in bari kowa ya sani amma na shaida masa na riga na fada wa Kamal. Tabbas yanayinsa ya sauya a lokacin, duk da ban san dalili ba amma ni dai na ga sauyuwar."

"Babu komai, da izinin Allah asirinshi yana daf da buduwa baki daya. Idan ma akwai wasu halayen nashi bayan wannan duka dai gaskiya za ta yi halinta. Ka ga dole hukuma ta yi aiki a kansa kafin ni kuma in raba shi da komai nawa da yake hannunsa. Na tsani mugunta da mugun mutumi. Ba na son mutum mai fuska biyu. Ina zaune da shi da zuciya daya a ko'ina zan iya bugar kirji in shaide shi da halaye na gari ashe na sab'a lamba. Muna nan muna ta fada wa Allah kuma zai ji kokenmu tunda mu ne da gaskiya."

"Haka ne Daddy. Ina amaryarmu?"

Dariya Daddy ya yi ya ce
"Ta je wurin aiki. Ni ma akwai uzurin da yake gabana ne shi ya sa har yanzu ban zo Nigeria ba. May be ma sai nan da wata daya ko sati shida zan zo. Ina wani contract ne kuma dole sai ina tsaye a kanshi. Daga zarar ya kammala in shaa Allahu zan zo mu zauna da magabatan Saddam mu yi zancen aurensu. Zuwan nawa ne kawai wuya amma ba za a dauki dogon lokaci ba a yi auren ba tunda dai sun riga da sun fahimci junansu."

"Haka ne Daddy, to Allah Ya kawo ka lafiya."

"Ameen yarona. Ina 'yata?"

"Ta je wurin aiki."
Ya ba shi amsa.

"Okay a gaishe ta. Ai tana kokarin kira tana gaida ni sosai gaskiya. Allah Ya yi muku albarka duka."

MATAR AMEERWhere stories live. Discover now