babi na d'aya

3.9K 158 2
                                    

         Zaune take kan sallayarta bayan ta idar da sallar la'asar tana lazima. Mace ce 'yar kimanin shekara  arba'in da shidda zuwa d bakwai amma Sam batayi Kama da shekarunta ba saboda irin kyaun jikin da Allah yayi Mata, da kuma kasancewar ta 'yar Hutu.
Tabbas  idan aka ce ka  fadi shekarunta zaka iya  rantsewa 'yar talatin ce,
Kyakkyawa ce mai cikar mutunci da kamala,

     Wata kyakkyawar yarinya naga tafito cikin shirinta da alama fita zatayi don sanye take da hijab Mai hannu iya  guiwa. D'ayan hannuwanta riqe da yar post dinta kalar takalminta ko ba'a fada ba kasan cewa diyar hajiya zainab ce saboda tsantsar kamar da sukayi duk da cewa yarinyar bazata wuce shekara  goma sha tara ba.

   Gurfanawa tayi gaban mahaifiyar tata tana murmushi tare da cewa,
"Momy naga kina ta kallo na ko banyi kyau ba ne?" ta fada cikin shagwaba,

Tab'e baki mommy tayi.

" ba dole in kalleki ba naga kinci uban ado haka, kuma kinsan yau ba islamiya"

b'ata fuska tayi , " haba momy nafa gaya miki ina so inje gurin  maryam in karbo wani littafi da nake so in koya gurin malaminmu"

Cikin fad'a fad'a momyn tata take magana,
" kin San dai mahaifinki baya son irin wannan yawon ko ? Ko so kike yadawo bai ganki ba  ya hauni da fad'a? Gskiya abunda kike mun Afnan Sam ba na son shi kin fi kowa sanin halin mahaifin ki amma ke Sam ba kya gudun abunda kanje ya dawo,"

Cikin ladabi da girmamawa Afnan take magana " Dan Allah momy kiyi hakuri insha allahu Abba bazai dawo yasame bana nan ba amma idan har bakya son fitar na hakura sai wani lokaci sai inje in karbo"
Ta karashe maganar tare da mikewa idanuwanta cike da kwalla ta juya zata koma,

Yazeed ko YaseerWhere stories live. Discover now