Dakyar aka kwace hajiya tayi muguwar gala baita su Huzaifa ne suka shigo gidan,domun Hamnatu ta kirashi awaya ta gaya masa abunda yake faruwa addu'oe suka hauyi wasu matan ma suna tayadu cikin hukunci uban giji duk suka mike huzaifa yayi saurin cewa." Mun yafe kowacce akaita dakinta kowa yatafi,gidan su." cikin bacin rai yayi maganar.
Sumsum,mata suka fara kwasar kayan su daya zube dan kwali jaka ta kalmi mayafi,waya da sauransu kowace amarya aka kaita,dakinta aka kwantar aka futo aka tafi da sauri Huzaifa shida amininsa Anas suka dauki hajiya suka kaita dakinta suka kwantar Huzaifa yakira likita yadubata tare da saka mata ruwa da yimata allurar barci yatafi.
Anas ma ganin dare yayi yace." Huzaifa kazo in raka ka gun matan naka ko." wani mugun kallo,ya watsa masa sannan yace." Karabu da ni da sha anin wancan mahaukatan jibi abunda sukayiwa Hajiyata muje kawai in raka ka." ganin ran huzaifa ya baci yasa Anas yin shiru suka futo ya rakashi ya tafi yana dawowa yayi dakinsa wanda yake can gefe daga karshe yashiga ya kulle kofarsa ya watsa ruwa ya kwanta yana tunanin wannan wahallal auren kamar yadda tayi masa la'kabi ahaka har barci barawo yasace shi.
Dasafe 'yan aikin gidan suka hau gyara gidan saida ko ina yayi tas sannan suka dora abun kari.
Amare kuwa kowacce bata futoba sai wajen karfe sha dayan rana lokacin hajiya har ta tashi Hannatu ta taimaka mata tayi wanka ta ci abinci tasha magani suna falo suna kallo hadda Huzaifa suna dan taba hirar abunda yafaru jiya.
Suna cikin hirarsu saiga Zabba'u tashigo cikin kwalliya tana yatsina fuska kujera ta samu ta zauna ta kallesu dukansu tace." Sannu Hajiya ya jikin." washe baki,hajiya tayi tace.Da sauki.
Hannatu tayi saurin cewa.Anty kintashi lafiya.Lafiya'' kawai tace sannan ta kalli Huzaifa tace.Dear barka da safiya hunwa nakeji,sosai.
Wani bakin cikine ya tokare masa,aransa amma saboda,alkawarin daya daukar wa aminin sa nacewa bazai taba barin hajiya tagane baya farin ciki da wannan auranba yasa yayi murmushi yace." Ok ga abun kari can akan tebur kije kici." wani shagwagabewa tayi.Haba dear muje kabani ma......maganar ta ta katse saka makon ganin Fatima ta shigo cikin hadaddiyar kwalliya taje kusa da Huzaifa ta zauna tare da rike hannun sa.Honey kokazo ka tasheni gada,barci ko. wani uban tsaki Zabba' u ta saki tare da cewa.Aikin banza wayaga damau.
Wata uwar harar Fatima ta hurga mata tare da cewa.Ai kwanda damau da kwabau.'' Huzaufa yayi saurin mukewa tare da cewa.Hajiya bara inje gun Anas domun amso wasu kayana da jiya na,manta agunsa.'' Sadiya ce tashigo tana danba waya waje ta samu ta tsata tace.'' Hyy Hajiya. saiga Nusaiba itama tashigo tana wani harare hararen su Sadiya ran Huzaifa yayi mugun baci yasa kai yafuce daga dakin aikwa yuuuu suka bishi wai rakiya yana zuwa harabar gidan ya bude motarsa zai shiga Nusaiba tayi saurin rikewa.Habba byba yazaka tafi ko ganawa bamuyi,ba wadannan sharar matan naka sun hanamu,ganawa.
"Fatima ta tsako huyanta ke suwanene sharar,banza mai kama da dan bera." wata uwar tsawa Huzaifa ya yi. Dallah malamai ku bace mun daga gani shashashan banza wadanda basuda gurma saina jikinsu. sum sum suka bargun yashiga motarsa yaja cikin bacin rai yabar gidan.
Kowacce dakinta tashige tana yiwa yar uwarta habaici,da harare harare Hajiya tasaka 'yan aimin gidan kowacce aka kaimata abinci dakinta zuwa rana kowacce 'yan uwanta sukazo dubasu.
