page 6

262 22 0
                                    

NA
Zainab Abdullahi
(Real_shaxee)

ZAMANI WRITERS ASSOCIATION

Yana futowa ya ganta azaune jikin mudubi ya nufa dan shafa mai dasauri ta karasa inda yake ta kamo hannunsa ta zaunar dashi akan gado tara shafa masa." Haba saikace wanda bashida mata dukkanmu fa aikinmu mukula da kai dan Allah kayi hakuri damu akan halinmu kasan mu mata akwai kishi musammamma a kan abunsa mukeso kayi hakuri,dan Alfarmar manzon Allah (S.W.A)kaji nawan." dayake mai saukin halinne kuma kowaye aka hadashi da ma aiki zai sauko dan haka cikin sakin fuska yace." To shike,an amma koda kinga sunayi kidaina biyemusu tunda naga ke mai,saukin halince acikinsu dansu bawacce tayi tunanin bani hakuri kidaina biye musu banason hayaniya." cikin farin ciki tace." Insha Allah hakan bazata kuma faruwa kota baru to babu ni aciki nayi maka alkawari." suna dan taba hira harta gama shafa masa man ta shiryashi tsaf ta rakoshi har bakin motarsa suna dara a abunsu gwanin sha awa sanda yashiga motarsa ya laiko da kansa ya mika mata mukullin dakinsa." Fatuma ki gyaramun dakina kan in dawo kinji." " Insha Allahu byeee." yasakai yafuce daga gidan dama abunda take naima kenan kuma ta samu." Wallahi saina nunawa wadancan yaran bayan magani dole sai ka hada da kissa kudi nakeso kuma saina samu kota halin yaya ne ni ba ruwana." dakinta ta nufa tashiga cikin farinciki.

Lokacin da suka futo daga daki Zabba'u ta gani ranta yayi mugun baci dan haka da dau alwashin koyawa Fatima hankali.

Masu aikin gidan suna gama girkin rana suka kaiwa kowa dakinta kamar tadda hajiya tace abinci saidai kawai kaci da hakuri domun kullun shinkafa da miya sai safa duka ko alala babudai wani canji.

Fatima tana zaune saiga sallamar wata dattijuwar mata tashigo da gudu tazo ta rungumeta." Inna dama kenake ta jiran zuwanki zomuje daga ciki." uwar dakin suka shige suka kulle abunsu inda Fatina tabawa Inna labarin abunda yafaru jiya dayau." Yauwa 'yata daga yanzu karki kara kula kowacce acikinsu ki maida hankalinki akan babarasa dashi kansa in mungama wawashewa mukara gaba kuma ungo wannan maganin duk yadda za ayi kiyi kizubawa babarsa a abuncinta taci indai tace ko da idonta taganki kindau mata kudi bazata yi miki,magana ba barema ta gayawa wani." amsar maganin rayi taboye sannan ta kawo mata abunci taci da kayan dadi tabata kudin data sata." Wannan kibawa masu filinnan cikon kudinsu kinga sai ginine yarage mana."To shikenan shima da huri zamu gamashi ai dama nasan nayi farar haihuwa 'yata.

Tana gamawa ta bata kayan dadi tafuto ta rakata ta tafi ita kuma ta huce Dakin Huzaifa ta gyarashi tsaf ta bunkice ko ina taga inda yake ajiye komai batadau ko fucikaba tasaka turaren huta tafuto ta rife dakin kicin dinta na daki ta shiga inda tayi farfesun kifi tazuba maganin ta zuba a fulas tatawo dakin hajiya tana zaune ita hannatu tana mata fada akan ta futo da mujin aure.

" Hajiya sannunki da hutawa dama kifine nayi mimi farfesu nasan jikin girma saida romo danyayi kwari." Amma kwa 'yarnan kin taimaka mun dan inason kifi kuwa kawo muga.

" Haba hajiya ai kamar Inna ta haka kike aguna abaki zan baki domun ayanzu kece mamana kinga kuwa 'ya bata barin uwa tasha wahala." Allah yayi miki albarka Fati na kinada hankali gaskiya nagode wa Allah dana samu sirika irinki.

Zama tayi tana cire mata kaya tana bata abaki Hanbatu tace." Kai anty hajiya kadai kika sani ko sammin in maida yahuna abu sai kamshi yake." kunjimu da yarinya to badan halinkiba dakko faranti kidibi kadan.

Dasauri ta tashi ta dau filat tadiba tafara ci suna hirarsu inda Fatima cikin dabara take bugar cikinsu tanajin wani sirrin,nasu tana gama bawa hajiya ta dauke kwanon ta bawa mai aikin akan awake sai akai mata daki ita kuma ta amshi abincin Huzaifa ta jera masa adakinsa ta koma dakinta dan tayi wanka.

Sadiya kuwa tana daki tayi mankas abunta tanata uban barci duk kwalaben maye abaje a kan gadonta.

Zabba'u kuwa tana cikin chating dinta taci karo dawani hhadaddaen saurayi yaruro mata da.

Salam

ta amsa masa da

wlkslm
amma ka hadufa ba karya

yamaido mata da amsa

himmm harna kaiki kyau jibekifa ko ina da ina yaciki ya hadu ba karya.

wata shewa tayi domun dama tana ganinsa ta ji yayi mata kuma tana da burin hada alaka dashi saikuma gashi yanuna mata shima dan hannunne, daga nan suka cigaba da hirarsu tabanza da turawa da juna hotunan banza abunta har ma ta manta dawani Huzaifa da wasu kishiyoyinta.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now