page 11

370 15 5
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_____________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_____________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Page 11*

Wata kara hajiya tasaki tare da dafe kanta, nan take jini ya wanke mata fuska, agigice hannatu ta futo daga daki wata kara ita ma ta saki ta wawuro wayar ta ta danna nomber Huzaifa. " Hello yaya maza kazo matanka sun kashe hajiya." bata tsaya saurarar abunda zaice ba ta kashe wayar ta karasa inda hajiya take.

Su Fatima kuwa suna ganin abunda ya faru kowacce ta fuce aguje, tayi dakinta ta kulle, kowacce tana cikin furgicin abunda zaifaru in Huzaifa yazo.

Huzaifa yana cikin cin abinci Hannatu ta kirashi afurgice ya mike. " Anty bara intafi gida, wai wadan can matan sun kashe hajiya nasan yauma dukan sukayi mata, Hajiya ta kwaso mana bala'i wallahi." ita kanta anty hanka linta yayi mugun tashi. " Huzaifa bara indakko maya fina muje tare." da sauri ta dau mayafi tare da gayawa su maryam zata futa suka tawo.

Saida suka biya suka tawo da family doctor dinsu sannan suka tawo gida, cikin mahuya cin hali suka zo suka tarar da ita, kanta sai zubar jini yakeyi Hannatu sai faman kuka take, dasauri suka karasa inda take, likita ya fara aikinsa na ceton rayuwar ta, Huzaifa hankalin sa yayi mugun tashi ganin irin abunda sukayi wa mahaifiyar sa, ga dakin kaca-kaca an hargitsa komai, saida aka gama nade mata ciwon Anty ce ta kaita daki ta kwantar likita yasa mata ruwa dan kara jin kwarin jikin ta, yayi mata allura ta fara barci sannan ya futo daga gidan.

" Hannatu gaya mun mai ya faru acikin gidannan yau." Huzaifa ne yake tambayar ta, cikin kuka ta gaya masa duk abunda ta sani, wani tiriri ya fara yana huci idon sa
yayi mugun yin ja, afusace ya futo daga dakin hajiya, dakin Zabba'u ya fara nufa.


*Adadin commen adadin type🤷🏻‍♀*

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now