page 39

177 13 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳
 
    *SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
      *(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp  nomber*
08085898952


*Page 39*

Wa shegari Hannatu ta tashi da ɗan ƙarfinta saka makon taimakon da maganungunan nan suka yimata.

Falo ta futo inda ta tarar da yayan ta azaune shida hajiya suna magana, zama itama tayi akan kujera, inda taji yayan ta yana cewa. "Hajiya babu inda ƴan sanda basu duba taba amma bata nan, wasu ma daga cikin ƙawayen ta suntabbatar da cewa bata gatinma tun jiya, wai ta tafi wani gari wanda suma basuda tabbacin kowanne ne, iyayen ta ma ashe basa ƙasar suna dubai anje duba lafiyar mahaifinta kasan cewar kwana biyu baiji daɗin jikinsaba." "Huzaifa rabu da ƴar iska, tunda dai kakaiwa ƙanin ubanta ta kaddar saki aishi kenan, Allah ma ya temake mu bamu haɗa zuri'a da gayyar tsiya ba aishikenan, to ya jikin Fatima yake?" "Da sauƙi hajiya dan nama je ɗakinta induba ta natar da ta tafi gidan bikin da kika bata izinin zuwa, ita kuma Zabba'u naga jikin nata da sauƙi sosai." Hannatu ya kalla sannan yace. "Kekuma yaya jikin naki? Jiya da daddare nazo hajiya tace mun kina bacci." "Da sauƙi yaya, yauwa yaya ɗazu big boy yayi mun waya cewa gobe iyayen sa zasuzo naiman aure da kawo kuɗi da sarana." wata buɗa hajiya tayi tare da shewa. "Wayyo Allah na! Hannatu mai yasa tuntuni baki sanar dani ta tabbata goben zasuzo ba, wayyo daɗi kasheni, yauwa maza Huzaifa kaje ka gayawa su kahu ɗan Ladi, maza- maza nace." da zaiyi wata magana amma tunowa da yayi da gargaɗin hajiya yasashi ɗan yin murmushi. "To hajiya Allah ya sanya Alheri, amma hajiya ko karyawa banyi ba." Hannatu hajiya ta kallah tukun tace. "Maza jeki kisa ƴan aiki su haɗo mana abun kari dukanmu." tashi Hannatu tayi ta futa, yayinda hajiya ta juyo da kallon ta ga Huzaifa. "Da baka karyaba amma ka tsaya kana ƙananun magan ganu akan nace matar ka taje biki ko?" "Wallahi hajiya bahaka bane kawaidai na faɗane, amma hajiya bazakwa a kira masu duba karaya ba su duba Hannatu." cikin mamaki hajiya tace. "Maikuma ya faru?" "A a hajiya naga kamar tafiyar ta tacanza ne shine nayi tunanin ko ta yi targaɗe ne." ɗan tsaki tayi. "Bawani tar gaɗe abunda likita ya dubata sosai, kawai inaga ta bugune a ƙafar shiyasa." shitu yayi bai ƙara maganaba Hannatu ta shigo da kaya ahanunta bayan ta ma ƴar aikin suce itama ɗauke da kaya ahanunta.

Fatima kuwa ba biki sukeyiba wani matsafi ta samu wanda yayi muguwar shahara aduniyar marasa tsoron Allah, shikuma shara ɗinsa shine duk matar da takeson yayi mata aiki dolene saitazo tsuburin sa tayi kwana uku rak, yana biyan buƙatar sa da ita, wai da sunan aljanune suke yin haka, to indai mace tayi hakan to babu abunda zata zomasa da shi bai biya mata buƙatar taba, ta sanadiyyar wata ƙawarta da suka haɗu a watsapp ta sanshi, ta rakata taje masa da buƙatar ta shikuma ya kafa mata wannan tsaraɗin take ta amince masa shine yanzu ta tazo.


*Ruga*

Ruƙayya ce abakin rijiya tana ɗiban ruwa tana kaiwa ɗakinta don cika durom ɗinta na banɗaki dana kicin, hankalinta kwance takeyin aikinta tana ƴan waƙoƙinta.

Inna Larai ce ta leƙo ta ganta dan haka ta koma ɗakinta da sauri ta samu Samira. "Ke Samira! Maza tashi kije kisamu waccan ƴar rainin hankalin ki tsokanota gata can tana ɗiban ruwa arijiya nikuma innaga zata yimiki wani abu infuto muyi mata shegen duka acikin gidannan, naso ace su Laure basu tafi tallaba yau data ci ubanta." cikin hanzari da ɗoki Samira ta tashi. "Inna yau kice zamuyi lugude acikin gidannan, bara inje in tsokanota." bokitin daya ke ɗakinsu ta zara ta futo tsakar gida.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now