page 31

182 12 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952

*CALL nomber*
08175993608

*DEDICATED TO*
*BINTA UMAR😘*

*Masu yimun ya jiki gaskiya naji daɗi kuma na gode haka ma masu kirana awaya duk nagode muku sosai Allah yabar ƙauna ameen, jiki kuma da sauki shiya sa ma yau namuku type*


*Page 31*


Huzaifa yana futa office ɗinsa ya nufa,yana zuwa yasa manajan sa ya siyo masa abun kari ya karya sannan ya futo ya nufi gidan antyn sa.

Ita kaɗai ya tarar tana gyara falon dama yasan haka tunda ranar makaran tace. "Yaro na kaine kake tafe ashe? " "E wallahi anty abun duniya ne yamun yawa shine na tawo nan dan in samu sa'ida kinga ma garin ssuri har waya ta na manta da ita a office." "Hmmm Huzaifa nikaina har na fara jin kunyar baka haƙuri wallahi, yaya ta matsalar ta bata ƙarewa samm wallahi." "Anty kedai bari kawai, bara ma jiki abunda ya faru." komai ya kwashe ya gaya mata, girgi za kai kawai takeyi tukun tace. "Gaskiya wannan babbar matsala ce, amma tunda har tayi wannan furucin to karka kuskura ka ƙara yin magana dan zata iya yima mugun furuci, kawai muyi ta addu'a, sukuma matanka kamar yadda ka rabu da ɗayar cikin luma na insha Allah sauran ma haka, kuma ina kyautata zatan kwanan nan zata dawo dai-dai."nasiya tayi masa sosai duk da tasan haƙurin sa da tunanin sa, hirar su suka shiga yi harda dariya.

Nusaiba ɗakin ta takoma ta ɗakko ƴar fulawar tulun ta, dake gefen tv ɗinta ta futo, ɗakin Fatima ta nufa, a hauka ce tadinga buga wa, Fatima tana cikin barci taji wannan bugun cikin ɓacin rai ta futo dan tana tunanin ƴan aikine, buɗe kofar tayi cikin masifa. "Wai wanene yake mun w... tushhh kukeji wanda yasa ragowar maganar Fatima ta koma, wata uwar ƙara ta saki wacce ta furgita mutanan gidan. "Muna fukar banza dama tara ki nake, yau kuma kashinki ya bushe agidannan, saina sauke duk haushina da kuka tara mun yau." hajiya da Zabba'u nesuka futo dan ganin abunda yake faruwa, Hannutu ma ta biyo bayan su.Cikin alajabi hajiya tace. "Mai kuma yafaru asafiyar nan? Wai ke Nusaiba mai yasa baki da hankali maikika yimata kuma? Naga goshin ta da jini." wani mugun kallo ta hurga mata sannan tace. "Kanta na fasa mata wanda hakan zai iya faruwa da ke kema, dan ba tsoron ki nakejiba ehhe." baki hajiya ta riƙe cikin mamaki. "Eheee to uwar marasa kunya, ina ƙawar babar ki zaki mun wannan rashin mutuncin to wallahi zanyi maganin ki, Fatima Hannatu Zabba'u maza kuyi mata shegen duka." basu tsaya wata-wata ba suka hau dukan ta, da ƙarfi Nisaiba tace. "Kushi go." Aikwa sai ƙartin mata lafta- lafta guda biyar, basu tsaya komai ba suka rufe su hajiya da duka Nusaiba tana taya su, ƴan aiki sunyi cirko-cirko sun kasa shiga, ihu kawai suketa yi amma basu daina dukan suba, a haukace mai gadi yazo cikin gidan ganin abunda yake faru wa ya sashi ɗakko wata ƴar wayar sa yana kiran Huzaifa amma tana ta ƙara bai ɗaga ba, gashi faɗa yafi ƙarfin sa faɗan mata.

Ganin hakan ba mafuta bace saboda su hajiya anwage baki sai ihu suke tayi, ba shiri yafuta waje dan kiran mutane amma babu kowa kasan cewar unguwa ta masu kuɗi kowa gidan get kuma akulle, ƙara kiran Huzaifa yayi amma baiɗa gaba kuma yasan baitaɓa yimasa hakan ba, koma wa yayi cikin gidan yana basu haƙuri."Dan Allah kuyi haƙuri ku sake su." eenah babu ma wanda yasan sunayi saida suka ga su hajiya sunyi lilis sannan suka rabu da su, wata shewa Nusaiba tayi. "Bani kike yiwa gori ba? Gashinan na baki tawa salon garar saiki kira tsinannun ƙawayen naki kuyi fatyn bikin amsar gara, aikin banza kuma gida ne nabarmiki abunki da wannan ɗan naki mara amfani, keku ma Fatima dama kin tsaya mun arai ke wai tagaban goshin miji da uwar miji ko kuka haɗu da wannan yarin yar kuke gayamun magana to gobe ma kwa sake, keku ma Hannatu babu ruwana dake amma dan kini bibi shine ance ku dakeni kina hau dukana to ganaki tikwiy cinnan mutanan banza kawai." tana gama faɗa ta sa kai ta shige ɗakin ta suma suka bita dama duk ta haɗa kayanta kuma da mota suka zo kayan suka fara kwashe wa suna kaiwa mota.

Mai gadi sai sannu yake musu amma ya rasa yazai yi dasu shi ba mota ya iyaba bare ya kaisu asibiti, kuma Huzaifa baya ɗaga wayar sa kwata-kwata, ƴan aikin gidanne guda biyu suka tawo suka kakka ma su kowacce aka kaita ɗakinta, cikin azaba hajiya tace. "Ku kiramun Huzaifa kar in mutu." mai gadi yace. "Hajiya naita kiran wayar sa bai ɗauka ba inaga baya kusa da wayar ne." "To kukira mun likita." "Hajiya ai bani da nomber sa bare in kirashi." "Kadu ba waya ta zaka ga nasa doctor." sosa kai mai gadi yayi. "Hajiya nida ko aji ban taɓa shiga ba taya zan gane sunan nan."

Su Nusaiba kuwa saida suka kwashe komai ras sannan suka sa kai suka fuce daga gidan.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now