https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*Page 33*
Su Laure ne suka shigo ɗakin kowacce da tambaya abakin ta, amma ganin halin da inna Larai tashiga ne yasa su samun waje suka zauna suka zuba mata ido,Samira ce ta yi ƙarfin halin cewa. "Haba inna! Yakike sawa kanki da muwa bayan gamu, kokina tunanin cewa zamu barta ta zauna acikin gidan nan ne? mu kaɗai ma mun isheta dukan safe daban na dare da ban, kekuma kinsan yadda zakiyi mana da baffa yadda bazai taɓa iya ɗaukar mataki akan muba, kinga huya ce zata sata ta gudu da ƙafarta sukuma su Bilkisu kinsan yadda zakiyi da su ai, ni in anyi aure nama kibani ita amatsayin ƴar aiki shike nanfa." wani murmushi ne ya sau karwa inna Larai Laure ma tace. "Haka ne inna, kibar mu da ita kawai." hannu ta miƙa musu suka tafa. "Yauwa yaran kirki da duk nasara ma mafuta, wannan shawarar taku tayi baka ɗan ba, ayi mugani dai." wata dariya suka kwashe da ita.
Amarya kuwa tana ɗakinta da ƙwayen ta guda biyu wanda a gidan innar ta zasu kwana gobe su huce burni da yaya Shamsi da matar sa , Baffa ne ya shigo cikin shiga ta kamala da abokin sa aminin sa, ɗauke da laidojin su, anɗan taɓa yira sannan akayi addu'a sannan suka tashi baffa ya rakosu har soro sannan ya koma bai nufi ɗakin inna Larai ba dan sanin hali ya shige ɗakin amaryar sa.
Haryan zu tana kan gado fuskar ta arufe murmushi yayi sannan ya dawo falo ya buɗe kicin ɗinta ya ɗakko plat da cofuna guda biyu ya dawo ɗakin. "Amarya bakya laifi, ki buɗe maya fin man kisha iska." a hankali ta ɗan zameshi kaɗan, wani kallo yake mata azuciyar sa yace. "In ba rabo ba taya za'ayi insamu wannan tsaleliyar yarinyar amatsayin mata." afili kuma murmushi yayi sannan yace. "Koke fa tawan." ita ma murmishin tayi da koɗaɗɗan idon ta wanda kana gani kasan tasha kuka ne.
Laidar dasuka shigo da ita ya janyo kaza ɗaya ya ɗora musu a plat sannan ya tsiyaya musu tataccen nono mai kyau ya ɗora durowar kusa da gado, cinya ya ɗakko ya kai mata baki. "Bu ɗe in baki kinji amarya ta." murmushi tayi tare da maƙe kafa ɗa, cikin shagwaɓa tace. "A a saidai kai kafara ci tukun inci." jiyayi uwa ya kurma ihu dan daɗi saboda mai tsammaci furuci mai daɗi daga gare taba. "A a nima naƙi ɗin, naci girma keza ki fara ci." murmushi tayi tare da buɗe baki yaba ta, ita ma ta ɗakko ta bashi abaki, cikin marmari suka ci suka ƙoshi sannan sukayi sallah ya kama kanta yayi mata addu'a, bayan sun nuke sallayar ta kalleshi tace. "Nidai kaje falo zansa kayan barci." murmushi yayi sannan ya maƙe kafaɗa. "Naƙi ɗin, saidai kikawo insa miki." fuska ta rufe alamun kunya,murmushi ya ƙarayi sannan yaja kumatun ta. "Inkin gama saiki mun magana." falo yazo ya zauna yana mamakin kansa. "Dama haka na ƙware a iya soyayya? Allah mai iko yarinya mai sauƙin kai, Allah nagode maka." tana gama can zawa tace. "Nagama to." murmushi yayi sannan ya shiga ɗakin, wata sanda rewa yayi, riga ce ƴar doguwa dan ta huce gwiywa mai santsi duk da ba surar jiki take nunawa ba amma rigar tayi mugun yi mata kyau. "Amma fa kinyi kyau." cikin kunya ta nufi kan gado duk da gaban ta faɗuwa yake dan bata san abunda zai faru aga ba, girgiza kai yayi dan yasan kowacce amarya tana shiga wannan yanayin kayan jikinsa ya rage sannan ya nufi kan gadon shima ya kwanta.Asuba ta gari.
*Da asuba*
Baffa ne ya rigata tashi, falon ya futo ya buɗe kicin ɗinta da zummar ɗora mata ruwan wanka da na gasa jiki amma yaka sa kunna rishon, ido kawai yazuba masa yana tunani, shiba abun yaje gun Inna Larai ba yace ta bashi ruwan zafi, yasan hakan ma baza yuhuba, magana ya jiyo daga bayan sa. "Baffa na, bara inkunna." ƙara sawa inda take yayi riƙota. "A a inkin san bazaki iyaba ki barshi kije zan san yadda zanyi." murmushi tayi. "Zan iya fa." tana riƙe ahanun sa suka ƙarasa gun ta kunna yana gani, ruwa ya ɗemo adurom ɗin kicin ɗin ya ɗau tukun ya ya ɗora sannan ya riƙeta suka koma ɗaki. "Ki zauna kinji, yanzu zanje in ruwan yayi insirka miki abun kari kuma basai kinyi ba." harya juya zai futa ta riƙe hanun sa. "Dan Allah kabar ni nidai zan iya." huyan ta ya taɓa. "Kinji fa haryan zu da zazzaɓi ajikin ki." "Wallahi nidai zan iya." yadda ta narke masa baima san ya amsa mataba saida yaji tace. "Nogode." sannan ya farga da ya amsa mata, murmushi yayi sannan ya fuce daga ɗakin.
