page 28

201 15 2
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952

*Yau two page nayi niyar yimuku kamar yadda nace amma azumi da aiki ya hanani kumun uziri insha Allah gobe zanmuku.👏🏻*

*DEDICATED to*
*Real_shaxeee fans group*😘


*Page 28*

A hauka ce ta shige cikin ɗaki ta ɗakko maya fi ta fuce daga cikin gidan.

Baffa kuwa saida ya haɗawa Ruƙayya laife irin na burni dan abokinsa daya ke zuwa burni yabawa kuɗi ya tawo musu dashi, Shamsi ba ƙaramun daɗi yajiba ganin karramawar da yayi musu, amma haryau yakasa zuwa gun Ruƙayya zance saidai ya tura mata ɗan saƙo in ankwana biyu.

Inna Larai takasa kwantar da hankalinta duk kuɗinta ya ƙare agun bokaye kullun cikin yawo take gini kuma har angama anyi fenti.

Inna Larai ce azaune akan kujera a tsakar gida, ta rabka uban tagumi ta rasa maiya ke mata daɗi, gani tayi mutane sun fara shigowa da kaya, da ido ta bisu gaba ɗaya babu wanda yace mata ko ƙala acikinsu dama inna ta yimusu gargaɗi.

Jere sukeyi hankalin su kwance, matar yaya Shamsi ce agaba,kaya ne na gani na faɗa ake jera mata ɗakin su Auwalu ma an saka musu katifa kowa da tasa, ɗakin Bilkisu ma haka.

Inna Larai tana ɗaki takasa zaune ta kuma kasa tsaye. " Wai da gaske aurannan sai anyi shi? Bayan boka ya tabbatar mun da baza ayi ba jibi kaya uwa daga turai, nikuma ko ginin ba san jamun ba sai wani fenti da akamun ko kyau babu, nida inanan ma wallahi baza ayimunba, wallahi ya rinyar nan saina tanadar mata bala'i kala-kala wanda yama fi na yayar ki zaki gane dawa kika tinkaro kishi hhhh." zama tayi a ɗaki tana tubka sharri gashi su Samira suna gun tallan nono, murmushin mugunta tayi tare da girgiza kai.

Ƴan jere sai magariba suka gama kuma haryau basu sake ganin inna Larai ba tana ɗakin azaune abunta, saka kai sukayi suka fuce daga cikin gidan, inna Larai tana jin sun futa ta futo da sauri ta nufi ɗakin da akayi jere da niyar lalata kayan amma inah sun rufe ɗakin kuma ƙofar ba irin ta tabace mai kwarice ƙwafa tayi sannan ta zauna akan kujera tana girgiza ƙafa. "Wai haryau banga yarannan sun dawoba, kodai basu siy... Sallamar su Laure ce ta katse mata maganar ta. "Yanzu nake zan canku, ashe ma kuna tafe." Samira ce tayi saurin cewa. "Wallahi inna Laure ce bata da lafiya muna gun tallah ta tashi ta tafi wai akwai wanda yace ta kai masa nono, to tana da wowa tace wai bata jin daɗi, shine muka jira ta ɗanji daɗi muka tawo." da sauri ta miƙe ta riƙeta. "Maiya ke damunki?" "Inna cikina ne yake mun ciwo." kama ta tayisuka shige ɗaki. "Samira maza ki jiƙa mata kanwa ta sha, bara inje in ɗora mata ruwa tayi wanka."

Baffa yana waje ya kasa shigowa saboda tsoron bala'in da zai tarar a gida dan ya san bazai ji daɗiba yau, sai misali 9:00pm sannan ya tawo gaban sa yana faɗuwa, a tsakar gida ya tarar da ita azaune tana ɓare gyaɗa tana ci, wani wani mugun kallo ta hullah masa." To muna fukin tsohin annamimi, ashe auran da kace mun ka fasa ƙarya ne? Yau saina ga mutane sunzo suna jere, to wallahi ka taro wa kanka bala'i daba ka taɓa ganiba,halin da zaku shiga kaida ita, saiya fi wanda nayi muku sanda yayar ta tanan, kuma saika futa kanaimi abinci dan banyi da kaiba, kuma wallahi karka kuskura inganka aɗakina da zumman kazo kwanciya zaku gani indai nice wallahi aika sanni."

Ko ƙala ba baice mata ba yasamu gu ya zauna dama ya tsammaci fin haka ma da gunta, saboda sanda zau auri Amina ma har goshi ta fasa masa saboda bala'in ta, lazimun sa ya farayi. "Oo jibi uwa mutumin arziƙi saiwa mucincina baki kake waikai kana yin lazimi, amma tsiyar ka tafi ta wani kafurinma dan su mata ɗaya sukeyi ba ƙari amma kai sai aura auran bala'i kawai ka iyayi, kuma wallahi wa ɗannan yaran da aka barma kawai kaisu gidan kakarsu dama kayi kuskuren barinsu daka ga ɗanyan aiki wallahi" ko kallo bata isheshiba ganin bazai kulata ba yasa ta tashi tashige ɗaki ta kullo ƙofar da ƙarar tsiya, girgi za kansa kawai yayi yaci gaba da laziminsa.

Bala'in inna Larai yakai har da ko kwana bayayi acikin gidan, abinci kuwa yama manta rabonsa da cin abinci acikin gidan, abokin sane ya buɗe masa shagon gidan sa yake kwana anan.

Inna Larai ce azaune a tsakat gida ita da yaran ta dan yau basuje tallah ba. "Kun san mai inaso in yarin yarnan ta yi gangan cin shigowa cikin gidannan muhaɗu da ku musaukar mata da kondon bala'i wanda zaisa da kanta tabar cikin gidannan." Samira ce ta amshi zancan. "Ai wallahi inna ki kwantar da hankalin ki saimun zamar mata kondon ƙaya acikin gidannan dan nuna iko harda wani yi mata ginin ƴan gayu duk garinnan gidan maigari ne da ƴaƴan sa ake musu irin wannan gini." tafawa sukayi gaba ɗayan su, Laure tace. "Inna nifa gaskiya tallah zan rafi dan akwai masu siyan nono kullun ahannuna."Lami ma tayi saurin cewa. "Wallahi kuwa inna gwara mumuje tallan in yaso sai ita Samira ta zauna agidan." "Kudai wallahi sarakan son tallane, maza kuje ku ɗauka Allah ya bada sa'a amee." cikin zumuɗi suka tashi suka shiga ɗaki zuwa can kowacce ta futo da shirin tafiya tallah.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now