page 32

181 13 0
                                    

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952

*Jina dakukayi shiru bakomai bane illah da nace nadaina post anan sai wattpad kaɗai, amma saka makon wasu dasuka naimi alfarma zan cigaba da post amma iya group biyu kacal group ɗina na Real_shaxee pans group saikuma zan buɗe group na surukarmuce pans wanda anan ne kaɗai zaka samu damar karantashi tunda ga farko kuma na daina turawa ta pc duk mai naima ya tambaya awannaɓ group ɗin nikuma zan turo maka.Nagode.👏🏻*


*Page 32*

*Ruga*

Inna Larai ce a ɗakinta tana ta nike wakakkun kaya,Samira kuma agefan ta. "Inna saurayi na fa yace asatinnan zai turo iya yen sa." "Haba dai ƴar nan? Kice mun kusa fara jiƙewa da arziƙi, wannan ɗinnanne da kike gaya mun ko? Wanda baban sa yake da shanu masu yawa." kyaɓe baki Samira tayi. "Inna ba wannan bane, wani na haɗu dashi yazo siyan nono guna ɗan burnine yana zuwa nan garin siyan shanu yajw burni yana siyar wa ɗan masu kuɗine sosai fa." wata shewa inna Larai tayi."Kuma da kansa yace yana sonki har kuma zai turo? Kice ƴata tayi farin jini in anyi auran burni zai kaiki?" "Eemana inna haka yace bakiga gidan sa na burni ba daya nuna mun ƙatoto dashi." wata buɗa inna Larai ta ranga ɗa. "Wayyo Allah na ƴata tayi goshin arziƙi, wallahi zamu war wasa kice masa ya turo ɗin koyau she ya shirya." "To inna jibi zai zo garin zan gaya masa, shiyasa kika ga yau naƙi futa tallan saboda bazai zoba, inna wai su Laure mai yasa yanzu suke daɗe wa agun tallah, kuma wallahi yanzu ba agun da muke zama suke zama ba sai in zamu tawo gida zakiga sun dawo sai mu tawo in kuma banje ba kiga sai magariba zasu dawo." taɓe baki inna Larai tayi. "Tunda dai suna siyarwa su kawo mun kuɗina cas ai shikenan, kuma sun gaya mun wasune suka ce sudinga kai musu nono kullun suna siya." Samira bata ƙara cewa komai ba ta cigaba da taya innar tata ninkin kaya.

Da yamma Inna Larai tana cikin tuƙa tuwo, kawai taji an fara buɗa muta ne suna shigo wa cikin gida, sakato tayi tana binsu da kallo, bawan da ya kulata suka buɗe sabon ɗaki suka shige, ɗaya daga cikin su taji tana cewa. "Ai amaryar ma yanzu zasu tawo daga burni, yanzu masu tarar tasu ai ba zama zamuyi ba mugyaggyara ɗakin inda yayi ƙura a goge." Inna Larai bata san sanda muciyar hannun ta ta suɓuce ba. "Dama kwanta- kwanta Baffa yayi mata, da bakin safa yace mata ya fasa ashe ƙarya yake mata bai fasa ba." cikin zuciyar ta take wannan zancan,Samira ce ta futo daga ɗaki. "Inna wai mai nake ji haka? Uwa naji ana zancan kawo amarya, dama baffa bai fasa ba?" Inna Larai ko amsa bata bata ba ta sauke tukunyar tuwon tashoge ɗaki Samira ta rufa mata baya.

Kasa zama Inna Larai tayi sai zagaya ɗakin take."Ni za'a yau dara?" kawai take faɗa tana girgiza kai, Samira ma tagumi tayi kawai tana kallon innar tata.

*6:30pm*

Ƴan kawo amarya suka fara shigowa suna ranga ɗa buɗa, aka shigo da amarya lulluɓe da mayafi, ko ɗakin inna Larai basu kaita ba,ɗakinta suka nufa da ita, anata shewa. "Allah ya kawo mu gidan Ruƙayya sa'ar mata." inna Larai data ji wannan lafazin jitayi uwa ta haɗiyi zuciya dan baƙin ciki.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now