page 18

226 11 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952


*Page 18*

Huzaifa ya fara da cewa. "Da farko dai inaso ku saurareni kuma ku fahimceni sannan bana son haya niya, dafarko dai abunda yasa natara ku anan shine karkuga bana zuwa ɗakin kowacce daga cikin ku dalili kuwa shine bani da lafiya ba abunda zan iya yimuku, ga wannan ta kaddun zaku iya duba takaddun gwanji da akamun ne, amma ana shirin yimun aiki nan da ƴan wasu watanni, duk wacce zata iya zama to bisimillah wacce kuma take ganin bazata iya ba to ƙofa a buɗe take." duk su ukun kallon sa kawai sukeyi banda Fatima domun tariga da ta san komai, kowacce ta karanta. "Kun tabbatar da magana ta yanzu? Nusaiba ta yi saurin fara cewa. "A gaskiya nidai bazan zauna ba dama aurannan ya takureni da yawa ina buƙatar saki." Wani farin cikine ya saukar masa. "Yanzu kubari saida safe a gabanhajiya sai ayi maganar ko." fuuuu kowacce ta tashi ta fuce banda Fatima, kallonta yayi sannan yace. "Baki gamsu da bayanin nawa bane? Wani fari tayi. "Karka damu ni ina sonka akowane yanayi da kake, zan iya zama da kai." "To naji tashi kije ko." duk da ranta ya ɓaci amma bata nuna masa afuska ba ta tashi ta futo. "Wannan na fuskan ci yana da mugun rainin hankali, sai nayi da gaske tukun akansa wallahi." ɗakin ta ta buɗe ta shege tana saƙa da warwara.

Sadiya ta zauna ta rafka uban ta gumi. "Allah yasani ni dan sha'awar Huzaifa na aureshi kuma yanzu ban cika burina ba to zaman mai zanyi? gaskiya gwara in bar gidannan inje can inci gaba da harka ta kawai." da wannan shawarar ta yanke wa zuciyar ta.

Zabba'u kuwa tana zaune akan gado tana waya da big boy. "Kaji abunda yake faruwa, yanzu na yanke hukuncin barin gidannan kawai." daga can yace. "Lallai yarin yar nan baki da hankali, to in kika bar gidannan ni taya burina zai cika? Inkinaso kisamu abinda kikeso aguna kawai ki zauna har in cika burina, sannan wannan matsalar ba wata matsala bace bagani ba ninassn yadda zanyi indinga shigowa gunki akai-akai ina ɗebe miki kewa koya kika gani? "Yauwa ɗan gari kakawo shawara hakan kuwa za ayi."

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IFKLlTPJT997rWJWIxc4AF

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now