page 21

221 13 0
                                        

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952


*Page 21*

Hannatu ta cire ta gumin da tayi ta kuma ɗakko wayar ta, akaro na ba adadi ta ƙara kiran wayar big boy, cikin sa'a kuwa akunne take amma bai ɗaga ba, ta sake kira harta kusa tsinkewa ya ɗauka kantayi magana ya riga ta. "Dan kinsan bazan iya fushi dakeba ko? Shiya sa kike mun abunda kika gada ma, jiya kwata-kwata banyi barci ba saboda damuwa, yan zuma kaina inbanda ciwo ba abunda yake mun." cikin raunin murya tace. "Kayi haƙuri wallahi ba haka ne nufi naba, dan Allah kayi hakuri wallahi bazan sakeba, komai kace inyi zanyi." saida yayi wani malala cin murmushi tare da shafo wani munafikin gemun sa sannan yace. "Koke fa tawan yanzu nasan ina tare da wayayyar yarinya amma da kina mun irin uwa wacce bata je makaran taba, yanzu shike nan zuwa dare zanzo gun Zabba'u in kawo mata saƙo zan biyo ma tagun hajiya in nasalla meta sai ki sameni amota ko? "To shike nan mai kakeso in dafa maka? "No! Karki wahalar mun da kanki zan tawo mana da ice cream musha ko? Kawai kiyi mun kwalliya mai kyau amma banason kisa wannan ƙaton mayafin ko hijabi dan insamu ganin kwalliyar ki da kyau." "To shike nan saika zo." wayar ta kashe tare da daka tsalle.

Hajiya kuwa ɗakinta ta shiga tana ƴan ƙananun magana ta shirya tsaf taɗau jakarta. "Ooni ƴasu mai tuƙa motar nan haryau baidawo daga garin suba, yazama dole insa asamomin wani niba iya tuƙi nayiba bare inyi yanzu dole in hau motar haya." maya fin ta ta yafa tafuto bata bi takan kowa ba tayi fucewar ta abunta, dan duk ranta ajagule yake.

Fatima ce da innar ta a ɗaki. " Innah wannan kayan gara zaku haɗo na bajinta wanda za'a ɗauke imanin waccan munafukar matar dan inaso inzamo tagaban goshinta." "Ai basai kin faɗaba hakan kuwa za'ayi yan zu bara inje can gida insamu Rashida muje mu haɗo komai ayau gobe da yamma ki gaya mata za akawo kayan, halin wannan matar wallahi da fi'ilin tsiya take indai akayi garar aishikenan duk ƴsn kuɗin damuka tara zata sa mu taɓasu." "Ai inna kibarta kawai duk da kuɗin natane amma aita samu ɓatnar kuɗi, koda yake zamu fanshe ai." "To nidai Fatima bara in huce dahuri ko naga waccan matarma bata nan ai."

*Ruga*

Inna Larai ce azaune a mada fa tanayin girki dama tun rashin lafiyar babar su Bilkisu girki yadawo hannunta inta gada ma ta basu inbata gada maba ta hanasu.

Bilkisu tana zaune a gaban umman su yayyan ta duk sun tafi kasuwa, karatun ta da yaya Musa ya koya mata taketa biyawa saboda kullun saita biya masa wanda yabiya mata sannan yake ɗora mata wani, baffa ne yashigo gidan ɗauke da wata baƙar laida."Bilkisiwa ta! kina inane? da sauri tafuto tsakar gidan. "Baffa ganinan karatu nakeyi, yau yaya Musa yace saina biya masa zaimun wani." tabarma ta koma ɗaki ta ɗakko masata shimfuɗa masa ta amshi laidar hannunsa yazauna itama ta zauna, inna Larai sai harara take joho mata. "Bilkisuwa tun rannan Musa yaran kirki yake ta zuwa guna akan in barki kifara zuwa makarantar boko tunda kinaso amma ni kwata-kwata banason harkar baturannan to dayamun bayani nagane kuma na amince zan haɗaki da su Samira duka inkaiku mak... "Allah ya sawa ƙe inkai ƴaƴana wata makarantar nasara suje su lalace abanza ita ɗindai da dama suka gaji iskan ci saitaita zuwa am... "Waike Larai yaushe ne zakiyi hankali kigane gaskiya duk garinnan wakika taɓa ji ya lalace saboda karatun boko? "Oho maka dai amma wallahi bawan da ya isa ya kaimun yarana makarantar boko." cikin masifa take magana tana murguɗa baki, inda sabo ya saba da halinta. " ƴaƴa dai nakine tunda bakya so toshike nan amma ita nasan na isa da babarta ita zata je, ke gungo wannan kayan maka rantar kine ɗazu Musa ya kawo mun ranar litinin zaizo da safe ya kaiki kishirya da huri."

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now