https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*DEDICTED TO*
*KUCHKAR KISHIYA FANS**Yau ina fama da ciwon kai sosai amma naɗan yimuku taɓa ka lashe zuwa gobe in maikowa mai komai ya bani lafiya zanyi muku type in kuma kunjini shiru to.🤕*
*Page 30*
Huzaifa yana shiga ɗakin sa ya durƙushe yana kuka saboda baƙin ciki."Ya Allah ka kawo mun ƙarshen wannan abun, Allah ka shirya hajiya ta dawo hanya ma dai-dai ciya ya Allah, Allah kabani ikon cinye wannan jarabawat taka ameen." yafi wajen minti goma agun sannan ya tashi ya shige ɗakin sa akan gadon sa ya kwanta sannan ya zaro wayar sa da ga aljihu anty yake son kira amma kuma dare yayi dan haka saiya haƙura, karatun kur'ani ya kunna awayar sa yana bi, nan take zuciyar sa tayi sanyi barcima ya ɗauke shi.
Hannatu kuwa video call sukeyi da big boy. "Hany byba ina fatan dai gobe zaki rakani wannan chasun? Saboda manyan yara ne zasuje kinga kuwa ya kama ta muje." "Karka damu byba duk abunda za'a yima saina je." wata dariyar mugunta yayi. "To shike nan Hany byba saida safe." kashe kiran tai tana zumuɗin faty dan tasan za'a cashe sosai.
Big boy kuwa kiɗa ya kunna yana rawar murna. "Yarin ya gobe zan cika aikina nagaji da kashewa uwarki kuɗi ni ban amfana da komai hhhhh gobe akwai shagali."
*Washe gari*
Huzaifa da huri ya fuce daga gidan ko ɗakin hajiya bai ƙwanƙwasa ba, Nusaiba tana kallonsa yana fuce wa taji ƙarar motar sa tabar gidan tayi tsalle ta futo tsakar gidan."Hhhh yau za ayi yaƙin duniya na biyu acikin gidannan, dama tara ku nakeyi, miji bashida amfani uwa maison abun duniya gashi duk ta addabeni da habaici akan gara kukuma waɗan can kuna mun kallon raini musamman ma Fatima,hmmm yau za ayi ta ta ƙare inci mutuncin ku inbar gidan dama na gaji da zaman sa." wayar ta ta daddan na ta kira wata nomber. "Hello in kun ƙaraso ku tsaya abakun get da kunji nace kushigo to kushigo, kuma karku tsaya komai kurufe su da duka." sauri tayi ta kashe wayar ta tare da yin murmushin mugunta.
*Real_shaxee...✍🏻*