https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*Page 27*
*Ruga*
Jiya aka share zaman makoki kowa ya watse sai su Inna kawai.Dan haka inna tace Shamsu ya tsaya zatayi magana da su mai muhimmanci, shida matarsa dan ta ɗauketa ƴar uwa itama sai kuma Ruƙayya. "Da farko dai abunda ya tara mu anan shine, da farko dai kunsan kaf ɗinku babu wanda na tauye haƙƙinsa kowa abunda yakeso shinake barinsa yayi mutuƙar bazai cutar da shiba kuma bai saɓawa addiniba,amma yau nazo da buƙatata ina so kuyimun amma bisa sharaɗi dukanku kowa ya tabbatar cewa ba wai dan bayaso zai amunce ba a'a saidan ya amince in aka yimun haka kuws daga baya nagano ba dan son ran mutun bane tofa zanyi matuƙar fushi dashi, kowa acikinku yasan baƙar wahalar da Amina ta sha agidannan da kuma kan yaranta, to yanzu ta mutu kuma kunssn cewa mahaifinsu bazai iya rabuwa dasu dukaba kasan cewar sune masu taimaka masa kuma in muka ɗauki wani muka bar wani bamuyi adalciba saboda wanda muka bari mun barshi cikin uƙuba da tashin hankali, dan haka na yi tunanin Ruƙayya ta maye gurbin Amina babisa tursa sawaba bisa amincewar ta inkuma bata aminceba wallahi wallahi bazanji haushintaba saidai nasan bamuyiwa Amina adalciba munbar ƴaƴan ta zasu tagayyara aduniya, yanzu zance ya zama naku nidai amsa kawai nake buƙata." tana kaiwa nan ta tashi ta fuce daga ɗakin kowa kallon kowa yakeyi, matar Shamsu ce tafara magana. "Tabbas inna ta faɗi gaskiya, kuma ta cancanci a yi mata wannan buƙatar tata kidsn farin cikinta amma Ruƙayya kitabbatar gaskiya zaki faɗawa inna gudun samun matsala anan gaba, inna tasha wahalarku aduniya ita kaɗai hannunta yayi kanta gun naima muku abinci da kuɗin makaranta, kuma bata taɓa naiman komai agun kuba kuyi tunani." murmushi Ruƙayya tayi sannan tace. "Yaya ka daina damuwa wallahi har ga Allah na amince da zuciya ɗaya, kuma zan zauna in kula da su Bilkisu kamar yaya ce araye,amma abunda nake buƙata dan Allah yaya ka aurar dani kamar kowace budurwa amun komai da akeyiwa mace in zatayi aure." kamo ta yayi ya rungumeta. "Nagode miki ƙanwata tun kan inna tayi wannan tunanin nayishi amma ina gudun tararki da wannan zacan guduk karkiƙi amuncewa, wallahi wallahi saina yimiki gatan dabaki taɓa tsammaniba a auranki mungode miki sosai ƴar autarmu." inna duk tana jinsu ba shakka taso barin ƴarta ta zaɓo mijin aure kamar kowane ɗanta daga ciki amma ƙaddara ta riga fata, tana fatan auran nan yazame mata alkairi.
Ankira Baffa an masa bayani kuma taji daɗi sosai kasancewar yasan gidan su Ameena akwai tarbiya dama yana tunanin halin dayaran zasu shiga musamman ma Bilkisu, amma Shamsu ya roƙi baffa akan ya bashi mazan biyu daga cikin su ya tafi dasu baffa ya amince inda ya bashi Salisu da Rabi'u.
Da wannan zancan duk suka tafi inda inna ta tafi da Bilkisu akan in anyi auran da sati biyu saita dawo.Duk wannan budurin da akeyi inna Larai bata saniba ganin duk an kwashe yara yasata murna gida ya zama nata.
Cikin sati biyu Shamsi yazo da masu gini suka rushe ɗakin Amina suka yanki wani gu suka tada gini da amincewar baffa babban falo da uwar ɗaki sai kicin acikin falon da ban ɗaki suka futar sannan akayi ƙananun ɗakuna akusa dashi guda biyu gini yayi kyau sosai.
Baffa yana dawowa inna Larai ta tareshi. "Wai wannan ginin da akeyi fa? Ina fatan ba gado ka fara rabawa ba? Da har ƴan uwanta zasuzo suna wani gini jibi dan Allah gini uwa a birni." murmushi yayi ya miƙa mata babbar baƙar laidar hanun sa. "Dama yau nakeso in gaya miki komai, ƴan uwan Ameena sun bani ƙanwarsu Ruƙayya saboda yara, shine yayan ta yake mata gini kinsan ita ƴar birnice, wannan ma kayan faɗar kishiya ne nakawo miki." wata sandarewa tayi, shikwa baffa yasa kai ya fuce dan anfara kiran sallar magariba.
Hannu ta ɗora aka. "Nashiga uku yanzu wannan futunanniyar yarinyar za'a kawo mun amatsayin kishiya? Wallahi bazata saɓuba koda zan rasa komai arayuwa ta inyi yawo tsirara saina hana wannan auran, bazai taɓa yuhuwa ba."