page 10

454 14 0
                                        

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_____________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_____________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Page 10*

Dakin hajiya ta je ta tarar da ita ta na kallo dama aikinta kennan daga kallo sai tara kawaye aita gulma da munafunci. " Fatima kece haka, zauna mana yata." washe bakinta tayi kamar gaske tasau gu ta zauna. " Nice wallahi hajiya daga kicin nake naje nadan taya su girki, daya ke nasaba to in banyiba bana jin dadi." " Ai ke fatima naga ba irin ragowar bane keda Zabba'u amma wadan can duk basuda kirki." washe baki Fatima tayi. " Ina hannatu ne bangan taba." Tana can dakin ta tana waya da mijin daza ta aura, kinsan ku yaran zamanin nan soyayyar ku tasha babban da tamu." yake kawai Fatima take yi ita kuma hajiya sai zuba takeyi abunta.

Zabba'u ce ta futo daga dakinta tazo na hajiya ta tarar da Fatima inda suka hau harar juna, Sadiya ta hango sanda su Fatima suka shiga,wani malalacin murmushi tayi. " Wallahi yau saina rama abunda kukamun rannan kuka bata mun shirina zaku gani." futo wa tayi ta shigo dakin hajiyar ita ma tana yatsina fuska ta tsaya akan Fatima tana danne danne a wayarta, hajiya tasski baki tana kallon ikon Allah, cikin bacin rai Fatima tace. " Malama ki matsamun daga kai, karki samun ciwon kai." wata dariy Nusaiba tayi tace. " Dama ku talakawa komai kuce ciwon kai, babu ishashshen abinci bare na gina jiki aidole aita kamun ciwo." a fusa ce Fatima ta mike. " Dallah malama tsaya inda matsayin ki yake karki kuskura ki gaya mun maganar banza data hofi." Nusaiba ta cakumi huyan Fatima. " Mai zaki iyayi ne in angaya miki magana keda waccan abun mai kama da matar mahaukata."Zabba'u ta daka tsalle ta wankawa Nusaiba mari. " Ke karki kuskura ki sakoni a shirmenku na fi karfinku keda wannan yar talakawar." fada ya kaure Hajiya takasa zuwa inda suke saboda tsoron abunda ya faru da ita kwanaki, tana daga zaune take magana. " Baza ka ku bari ba nace, wallahi ranku zaiyi mugun baci." ba wanda yasan ma tanayi dabbe kawai sukeyi ba kakkautawa wannan tadaki wannan wannan ta daki waccan, duk abun nan da akeyi Nusaiba tana jinsu amma ko futowa bata yiba.

Hannatu kuwa tana can suna ta shan soyayyar su Big boy tajiyo haya niya, falon ta futo taga abunda yake faruwa. " Gaskiya matannan baku da aikin yi ku kullun cikin fada kuke, kuje ku karata kuda mijin ku, ni babu ruwana wallahi." ta koma warta daki hajiya kuwa ta zuba musu ido tana kallon sarautar Allah.

Huzaifa kuwa yana can gun aikinsa, yana ta aiki wani lokacin kuma ya tsaya yayi tunani ya girgiza ka, koyayi guntun tsaki, ganin hakan bazai kaishi ga komai ba kawai ya hada kayan sa yabar office, gidan anty sa ya nufa kanwar maman sa, a falo ya tarar da su duka suna zaune suna hirar su, waje ya samu ya zauna kowa ya gaishe shi saikuma suka tashi sukayi daki suka barsu su kadai. " Huzaifa yaya dai ko dai hajiyar ce." dan guntun tsaki yayi sannan yace. " Aikin sani kullun itace matsala ta, yanzu kuma tasamowa hannatu miji wanda labarinsa naji nasan kwata-kwata ba mutumin kirki bane, zuwan farko yayi kyautar har naira dubu dari hudu, ko aina ta samoshi ohoo." girgiza kai anty tayi sannan tace. " Ko da wasa karka nuna baka son yaron inba haka ba akwai matsala, kaidai kawai kaje ka binciki yaron inka sameshi da mugun hali saika gaya mata, wata kila zata iya hakura, dukda abune mai wahala saboda ita ma Hannatun irin halinsu daya da ita." shiru yayi kawai yana girgiza kai, anty taje ta kawo masa abinci.

Su Fatima kuwa fada kawai sukeyi uwa zakuna duk sunjiwa kansu ciwo hajiya tayi tayi su daina amma sunki dainawa, Sadiya ta ciji Fatima aikwa ta kwalla kara ta je da dakko tulun fula tayo kan Sadiya suka fara gudu ganin bazata cimmata ba yasa ta hullowa Sadiya tulun jikuke tushhhhhhhhh akan hajiya.





*😳🙆🏻Turkashi.*

*Adadin comment adadin type🤷🏻‍♀*

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now