page 22

234 13 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952


*Page 22*

"Inna ai wannan matar uwa mai zama da ruhanai, kullun cikin sake hali take." ruwan laimo inna ta kurɓa tare da yagar cinyar kaza. "To nidai juye mun waɗannan kayan daɗin intafi dasu, kar inzauna ta dawo ta tarar da ni."

Sadiya kuwa tana ɗakinta tana ta haɗa kayan ta komai saida ta kwashe har mayuka sannan ra jere su, ta ɗakko mayafi ta yafa ta ɗau ƙaramar jakarta ta futo bata ɗau akwati ko ɗaya ba ta fuce daga gidan.

Hannatu kuwa tana bakin kwabarta a tsaye tama rasa wane kaya zata saka, inta ɗakko wannan saita chanza ta kuma ɗakko wani da ƙyar tasamo wata riga da siket bama tataɓa sasu ba, ajiye wa tayi akan gado ta haɗa komai iri ɗaya ta ajiye su.

Hajiya ce a zaune a gaban wani mai bada maganin hausa. "Wallahi yarona ne akayi masa aure har mata huɗu to saida ga baya yazo yake ce mun wai ashe bashida lafiya gashi har matan sun fara cewa ya sakesu, shine nazo katai maka ka bani magani ki'a dace." "To shike nan hajiya yanzu zan haɗa miki magani mai kyau kibashi yadinga jiƙawa yana sha tsawon sati biyu inya shanye komai zai dai-dai ta da izinin ubangiji, inya shanye ki dawo a ƙara masa wani." "Yauwa malam haka akeso yanzu nawa ne kuɗin maganin? "Dubu biyar ne ba tsada hajiya." washe bak tayi tare da zuge jakar ta ta ɗakko kuɗi. "Dama ƙawata tace mun maganin ka babu tsada shiyasa nazo gunka." murmushi yayi ya ɗakko mata ƙullin magani yabata, ita ma tabashi kuɗin sa ta tashi ta futo daga shagon, wata uwar dariya yayi. "Lallai wannan matar tafini son banza wallahi dubi kayan jikinta masu tsada amma take naiman sauƙi, to wallahi kin haɗu da wanda yafiki sabara na baki ba komai ba kije kita wahala hhhh."

*Ruga*

Farinci kine ya lulluɓe Bilkisu domun burin tane tayi karatu amna baffan ta baya so dan haka ta haƙura. "Baffa nagode Allah ya ƙara girma." shafa kanta yati cikin ƙauna. "Ameen ameen maigadon zinare autar baffa." ɗaukar kayan tayi tashige ɗakin su da gudu.

Ran inna Larai yaƙara ɓaci. "Wallahi karage nuna ban banci akan yaran ka, ko su kaɗaine ƴaƴa agidannan? "Oho miki dai kekika sani, nidai harga Allah ina iya bakin ƙoƙarina akan yarannan kece dai baƙya gani." ko ƙara kulashi batayi ba taciga ba da aikin ta.

Bilkisu cikin farin ciki take nunawa umman ta kayan makaran tarta harda litattafai da fansil. "Yauwa Bilkisuna kinga Allah ya cika miki burinki, dama ina yawan gaya miki duk mai haƙuri yana tare da samun nasara." "Umma haka ne kuma naga ribar haƙurina yanzu bara in aje kayan makarantar innunawa su yaya insun dawo."

Baffa yayi fucewar sa abunsa, inna Larai tagama girkinta tas tazubawa su Bilkisu a kwanan su ta ajiye musu a inda ta saba dama haka takeyi sukuma insunzo sunsan nasune saisu ɗauka ita da ummansu, maganin da boka ya bata ta ɗakko ta barbaɗa akan dambun marasar da tayi tarufe shi ta ajiye ta shige ɗakin ta, zuwa jimawa ta futo cikin shirin futa. "Ke mai kama da aljanu zonan!" Bilkisu tana ji tasan da ita take dan haka da sauri tafuto. "Gani inna." "To uwar iyayi da kinibibi to futa zanyi bazan daɗe ba kigyara mun gida na tas sannan insu Samira sundawo daga tallan nono ki amshi kayan ki haɗa da wanda nayi girki ki wanke su tass, kuma wallahi inna dawo naga ba ayimun yadda nake soba raiya ɓaci kuma ga abincikunan saikin gama aiki zaki ɗauka kici ki jini ko." "To inna naji." sakai tayi ta fuce abun ta.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now