page 36

184 18 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952
*CALL NOMBER*
08175993608

*Page 36*

Ɗan tunani tayi na abunda zata dafa sannan ta gaya masa suka sake sallah ma ya futo, inna Larai bata tsakar gidan sai su Samira ko gaisu wa babu wanda yayi masa dama ya saba kallon su yayi. "Yana ganku agida bazaku huce kutafi islamiyyar bane?" daga ɗaki inna Larai tace. "Nice nan na hana su zuwa, inma taƙaice maka da zance na ciresu tun watan baya." "Laure mai kike nufi da kin ciresu? Ilimin ne bakya son suyi kokuma yaya?" "Wannan kuma kaika sani nidai yarana aure zan musu gudun suje su lalace irin wannan yarinyar mai kama da aljanu, dan yazu nasan ma ta kwaso cikin shege saura mujira bayyanar sa musha fati, in an haifeshi musha buduri acikin gidannan inyi rawa inyi juyi." ran baffa ba ƙaramun ɓaci yayi da wannan kalaman nataba. "Insha Allahu duk cikin ƴaƴana babu wanda zai haɗu da wannan baƙar ƙaddarar, kekuma Allah ya ganar dake." yana gama faɗa yasa kai ya fuce daga gidan.

Ruƙayya tana jiyo su ranta itama yayi mugun ɓaci, amma bata futoba, ta fara ɗan gyare-gyaren ta tama gyara abunda bai mataba aɗakin.

Inna Larai tana ta nazatin hanyar dazata samu ta muzgunawa Ruƙayya da baffa duk ta kasa sukuni, saiga ƴan uwan Ruƙayya sunzo kai tsaye ɗakin ƴar uwar su suka huce suka ƙwanƙwasa ta zo ta buɗe musu, suka kwashe da shewa, inna Larai gani take dama da ita suke yi."Inna nikinga zan huce gun tallan nida Laure ga Samira nan tace wai ita ta daina tallan nono saurayin ta ɗan burni baya so, tomu zamu tafi." Lami ce take maganar tana gyara zaman robar ta dake kanta. "E Lami kukuje ita munyi magana da ita tunda baya so ai sai a haƙura tunda kuɗine dashi masamu ajikinsa, kuɗin dai kuje kuma kanku samu mijin aure duk in aurar daku cikin farinciki." dariya sukayi dukansu sannan Laure da Lami suka fuce daga gidan.

Sai wajen ƙarfe uku tukun ƴan uwan Ruƙayya suka tafi, yayin da suka kakkawo mata ragowar kayayyakin ta da kuma gudun mawar data samu daga ƙawaye da abokanan arziƙi.

Misalin ƙarfe huɗu saura saiga baffa ya dawo ɗauke da laidojinsa, inna Larai ta kalleshi ta ɗora hannu aka. "Nashiga uku ni Larai, malam yanzu kaine da ranar Allah ka dawo, kaida sai dab da maga riba kake dawo wa, na shiga ukuna sun tsafa ce mun miji, wallahi bazai yuhuba maza ka juya kakoma inda ka futo kuma wallahi ka mayar da wannan laidojin sunzo zasu sabauta ka ko? Wata kan ɗan arziƙin naka sukeso suƙara sa cinyewa ko." "Wai ke Larai mai yasa kikeyin haka, tunda kika ganni yanzu aikinsan da dalili, to yarinyar ce tace ita bazata amshi kuɗin cefane ba indinga siyowa da kaina ina kawowa shine naje nasiyo mata wanda zaiyi mata ɗan kwana biyu ko uku, kuma na biya kuɗi za ajawo mana hutar nefa, kuma mai gari ya gayamun anayi sallar la'asar masu aikin zasuzo shiyasa na rawo kar suzo bana nan." haɓa inna Larai ta riƙe. "Eheee yau naga sana be, watakan ita kalar nata iskan cin kenan da kinibibi to wallahi bazai yuhuba samm." kallon ta kawai yakeyi. "Yan zu tsaya kiji, tun farko ni ban tauye kowa ba, kows saina tambayi she ra'ayinsa, kema yanzu in kin yadda sai indinga siyo miki komai t... "Wallahi baka isaba wata kan ɗan gutun canjin ake mun baƙin cikinsa, yanzu na ganota wata kan ɗan abunda nake samu take mun baƙin cikin sa, to bazai yuhuba." cigaba da tafiya yayi yana cewa. "To kin gani kowa yayi yadda yakeso nikuma bazan tauyewa kowa haƙƙin saba." kyaɓe baki tayi. "Wannan kuma kai kasani, indai nice wallahi zaka zo kasame ni ai kasan halina." samira data ke zaune tana daka daddawa a turmi ta kalli inna tace. "Wallahi inna saifa kin tashi tsaye sosai, dan na fuskan ci take-taken wannan matar ba bu alheri acikin safa." "Samira kedai barni, bara su Lami su dawo daga tallan in ɗan haɗa ɗan kuɗin akwai inda nake son zuwa ayimun maganin su dukan su." "Yauwa inna gwara kiyi hakan inba haka ba mu kaɗai zamu sha ta ƙaici."

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now