page 45

141 9 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952


*Page 45*

*Tuna baya*
Fatima tana isa gun matsafin da aka rakata, dama da farko saika cika sharaɗinsa nayi kwana uku tukun aranar ta huɗi kagaya masa buƙatar ka, kan kaje gida yagama yimaka abunda kakeso.

Hakance ta faru da Fatima yau tacika kwana uku ciff,dan haka azaune take akusa da matsafin tana kora masa bayanin abunda takeso. "Inaso duk gidannan yazama na nice zanfaɗa kuma aji ayi yadda nakeso, sannan inaso duk wata dukiyar su yazama na nice zanyi yadda nagada ma batare da suncemun ko ƙalaba, sannan wannan kishiyar tawa inason tafuce daga gidan tunkan inkoma kuma ayau yabita da takaddar saki, kaga gida yazama nawa ni kaɗai." wani mudubi ya kallah tukun ya juyo da kansa gareta yace"Buƙatar ki mai sauƙice saidai wannan yaran zaiɗan yimiki gaddama saboda yanada ruƙo da addini sosai, amma tunda yana matuƙar jin maganar babarsa ita kuma tana hanunki to kingama komai, itakuma kishiyarki bakida matsala da ita dan yan zu hakama tana haɗa kayanta kankije tabar gidan."

Mudubin ya ƙara dubawa naɗan lokaci tukun yace"Amma akwai aikin da zaki dinga yi duk bayan wata bibbiyu, aikin kwa shine, inlokacin yayi kisamu ɗan bunsuru kisami bokoyi babba azuba wannan garin maganin adinga watsawa ɗan bunsurun har ruwan ya ƙare sannan kar abari ya bushe a haƙa ƙaton rami a bunne shi da ransa, indai kikayi haka to aikin ki bazai taɓa ɓaciba amma inbakiyi ba komai zai war gaje." "Boka ai bawani ma dogon lokaci zan ɗauka agidan ba, dana samu dukiya shikenan zan bar gidan." maganin ya bata sannan yayi mata wankan magani tukun ta haɗa yan kayanta ta tawo.

Gidan su ta huce tabawa innar ta labari sannan tayi ƙunshi da gyaran jiki ta tawo gidan ta, dan kowa inya kalleta yace tabbas daga gidan bikin ta tawo.



*Adadin comment adadin type🤷🏻‍♀*

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now