https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*Page 20*
Ran hajiya ya ƙara ɓaci sosai."To kukuma fa? Kokuma sakin kukeso? Cikin alamun tausaya wa Fatima tace. "Haba dai hajiya wane irin saki kuma, aike uwace baza ki taɓa cutar da muba, da kinga zamu cutu ai da bazaki ce muzaunaba." nanda nan hajiya ta sakko. "Yauwa yarinyar kirki, aike dayake mutuniyar arziƙi ce kin fahimceni." daga Nusaiba har Zabba'u ba wanda yace ƙala. "Hajiya toni na tafi office." "To Allah ya kiyaye hanya." fucewa yayi yana mamakin halin hajiya.
Nusaiba ta tashi tafuce ya rage sai su biyu. "Hajiya big boy yace intambaye ki wai wace irin mota kikeso asaimiki." wata irin zabura hajiya tayi saigata a ƙasan tayal. "Ke ƴarnan da gaske kike koda wasa? Murmushin yau dara tayi. "Hajiya da gaske nake mana, yau ma zaizo ya kawo mun saƙo zaitawo miki da mukulin motar, cewa yayi baida ce ace yar yau motar ki guda ɗayaba kullun da ita kike yawo." "Wayyo daɗi kasheni kedai yarinya Allah yayi miki albarka kinzama mai ƙashin arziƙi, dama ina cewa ƙawayena kune silar arziƙina gashi kuwa, kice masa yasamo mun mai tsada sosai kuma motar takasance ruwan toka." cikin zuciyar Zabba'u tace. "Ji wannan matar duk ta wani ruɗe gaskiya Allah yayi wannan matar da shegen son kuɗin tsiya tabb." afili kuma tayi murmushi. "To shikenan hajiya zan gaya masa." ta tashi ta fuce daga ɗakin, Fatima kuwa tarasa mai suke nufi duk da tanason sani amma harsuka gama maganar bata gane komai ba, ganin hajiya ta shiga wasu ƙananun surutar uwa wacce ta zauce tasa da sauri tace. "Hajiya bara inje in gyara miki ɗakinki." "To ƴarnan kamar kinsan kuwa mai gyaran yau bata gyaraba naga kamar bata jin daɗin jikinta." shige wa tayi da sairi saida ta gyara ko ina gu yayi tas sannan ta buɗe kwabar hajiya tana duddubawa kuwa taga wata jaka tana buɗewa taga kuɗi rafar ƴan dubu-dubu ta ɗauka guda huɗu ta ƙulle a laida ta cillah ta taga zuwa bayan gidan cikin ciyayi sannan ta maida komai ta gyara ta futo bata ga hajiyaba sai muryar ta data jiyo a ɗakin Hannatu dan haka ta fuce abunta.
Bayan gidan ta nufa inda ta ɗakko kuɗin ta ɓoye a rigarta sannan ta tawo ta shige ɗakinta ta rufe.
"Waike Hannatu yau mai yake damunki? duk kin wani canza nazo ingaya miki abun arziƙi amma natarar dake a haka, lafiyarki kuwa? "hajiya jiya ne mukayi faɗa da big boy kuma inata kiran sa yaƙi ɗagawa ƙarshema ya kashe wayar haryan zu baikunnaba." "Innalillahi wa inna'ilahirraju'un ! nashiga uku na, yanzu yarinyar nan abunda zakiyimun kenan yanzuba yaturo wai in zaɓi motar dana ke asiyamun inata murna harda kiran ƙawaye na ina cemusu sirikina yasaimun mota ashe ke kinanan kin ɓata komai ko? To wallahi baki isaba duk yadda ma za ayi kiyi kushirya kandare kuma komene ne yace ki yadda kawai kushirya, dan haka bara inje dan inason infuta kan indawo intarar komai ya daidaita eheee." a fusace ta futa, Hannatu kuwa ta rabka uban tagumi.
*Ruga*
Inna Larai ce a zaune agaban wani boka cikin jeji. "Boka sonake yarannan kota halin yaya ne ya auri Samira tunda ance baban sa yana kuɗi sosai, ita kuma wannan yarinyar Bilkisu sonake kasata takoma ƴar iska taita bin maza uwa karya kuma komai za ayi bazata dainaba ni ƙarshema ta ɗakko ciki kuma cikin duk abunda zasuyi karya zube." garin magani guda biyu ya ɗakko. "Kinga wannan ɓakin shizaki zuba a abicin kibata taci indai taci to angama kuma maganin makarin sa ɗaya ne kuma yana can wani surƙuƙin daji wanda mutun baya iya zuwa, dan haka ki kula ki tabbatar da ita ce zata ci, shikuma wannan turare zata yi dashi ta ambaci sunansa sauɗaya inta gama taje gunsa ya shaƙi ƙamshi shikenan angama." wani farincikine ya lulluɓe ta ajiye masa ƙuɗin aikinsa ta tawo.