https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*Page 44*
Dariya suka kwashe da ita gaba ɗayansu,Lami tace. "Inna ni wallahi inna samu mai kuɗi na aura ko, ɗaukeki zanyi daga ƙauyannan in maidake burni kema ki waye sosai." "Wai waya ganni aburni nayi ƙwam." dariya suka kuma kwashewa da ita suka tafa.
Wasa-wasa su baffa haryan zu basuga Auwalu ba, duk inda suka san yana zuwa sunje amma babu wanda yace ma ya ganshi, rai babu daɗi haka suka nufo gida suka tawo.
Bilkisu tana ɗakinta azaune ta kalli tsuntsuwar nan, ta ɗan shafata, saikuma ta tashi da sauri ta futo tsakar gidan su, sanɗa takeyi a hankali harta isa ɗan ɗakin dasuke ajiye kayan abinci, ahankali ta shiga ta buɗe buhun gero ta ciko hannunta da shi ta futo, wata ƴar roba ta ɗiɓi ruw tukun ta koma ɗakin, a ƙasa ta juye geron sannan ta ɗakko tsuntsuwar ta ajiyeta a gaban gero, saikuma ta ɗakko wani ɗan kwalinta ta yageshi ta ɗaurewa tsuntsuwar ƙafa gun dataga yayi jahh sosai.
Zubawa tsuntsuwar ido tayi amma bataga taci geronba tun tana kallonta har wani bacci ya ɗauketa mai uban nawi.
Take tsuntsuwar nan tayi wata fufguka ta girgiza jikinta nan take ta dawo Bilkisu sak, hatta kayan jikinta da ciwon hannu itama tana da shi, kallon Bilkisu tayi wacce taketa sharar baccinta ta girgiza kai ta futo daga ɗakin.
******
Hajiya ce a tsakar gida tanata wankin kayan ciki wato su wando siket da bireziyya sai wanki take iya ƙarfinta, Hannatu kuma tana can daga gefe tanata wanke-wanke mai uban yawa, Fatima kuwa tana kan kujerar roba agefe tana danna waya tana korawa da cake da laimo, sai dariya take wanda kana gani kasan tana jin daɗin abunda takeyi.*Tuna baya.*
*Dadin comment adadin type🤷🏻♀*
