https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*Page 47-50*
*End book 1*
Inna Larai tana kwance amma ta buɗe idonta, magana takeyi a fili tana murmushi. "Na ƙagu inga gobe tayi wallahi insha Allah yarannan zaicika mun aikina yadda nakeso bawata tantama, inkwa yayi mun haka wallahi saina bashi kyautar saniya ƙatuwa kuwa hh." jitayi uwa anhau kan ƙafarta da sauri ta tashi zaune, ido taketa zazzarewa gani manya-manyan ɓeraye ne yasata firgita. "Wayyo Allahna! Jama'a kuzo ku tainkeni zasu kas..." maganar ta ta tsaya sakamakon wani ɓeran dayayi sufa yahaye jikinta, azabure ta miƙe tsaye tana karkaɗe jikinta, wanima ya cabko ƙafarta wani hannunta duk sukayo kanta suna cizonta ihutakeyi iya ƙarfinta amma babu wanda ya kawo mata ɗauki, kota ina cizo sukeyi saikuma taga sunyi hanyar waje dukansu sunfuce daga ɗakin, wani zaman daɓaro tayi tana maida numfashi azabure ta tashi taje ta rufe ƙofar ɗakin nata, abakin ƙofar ta zauna tana dudduba jikinta babu tabo kokuma alamar wani abu ya cijeta bare kuma jini ya futo saidai azabar datakeji acikin jikinta, anan barci ya kwasheta.
Tsuntsuwar nan datayi kamar Bilkisu tana zaune abakin rijiya tana ɓaɓɓaka dariya wani dattijone ya bayyana agabanta cikin wata irin shiga. "Yarima sarki yana naiman ka da gaggawa." azabure tamiƙe tsaye. "Waziri yagamun mainene ya faru? kaddai kacemun sunkashe sarki?" dattijon nan ya ƙara matsowa kusa dashi yace"Ko kaɗan basu kashe shiba saidai sunyi mana babbar ɓarna a garinmu kaina naga duk cihuka ajikinka shine sarki ya turoni akan kazo dan muɗau fansa." nan danan yayi wata girgiza saigashi ya dawo wata halitta daban. "Sanda muka fafata dasune nasamu wannan raunikan, amma duk na kashesu, yarinyar gidannan ce ta taimakeni kuma nima naso taimakonta dan tashiga raina amma muje can inna gama da can nadawo nan." wata iskace tazo take suka ɓace daga gun ɓat,amma duk kayan wankin an wanke kuma anshanya.
Bilkisu bata tashi farkawa ba saida asuba taita dudduba tsuntsuwar nan amma bata ganta harta gaji ta haƙura, alqala tayi sannan tayi sallah, bakin murhu tazo tafara kunna huta kamar yadda inna ta yimata bayani, ruwa ta ɗora sannan tafara sharar gidan tajanyo ruwa ta ciccika ko ina, waje ta samu ta rabka uban tagumi.
Inna Larai tana farkawa ta kalli gari ta waje nan da nan ta tashi tsaye da sauri, mayafinta ta zara ta futo tsakar gidan bata bitakan kowaba ta fuce da sauri daga gidan.
Bata jimaba saigata tadawo tana murmushi, ɗakinta ta huce sannan kuma saita futo ta kalli Bilkisu tace"Maza ki huce ɗakinki anjima zan kiraki." tabacewa inna komai ba ta tashi ta huce ɗakinta taɗan kwanta.
Inna Larai tana ganin ta shige tayi saurin laiƙawa soro ta dawo ta shige ɗakinta, saigata ta futo da kwaɗo guda uku ɗakin baffa ta nufa tarufeshi a hankali tukun ta huce ɗakinsu Lami suma ta rufesu saita ajiye ɗayan a ƙasa ta shige ɗaki, yallone da abokinsa suka shigo cikin gidan suka ɗau mukullin suka rufe ɗakin inna tukun suka nufi ɗakin Bilkisu suna shiga basu tsaya wata-wata ba yallo ya afka mata.
Sani yana kwance yaji ƙarar Bilkisu da gudu ya tashi ya futo yayi ɗakinta inna Larai tana hangoshi ta taga ta daka uban tsaki. "Yaya akayi na manta ban kulle wancan ba kashh Allah yasa karya ɓatan shirina."
Sani yana shiga yaga abunda yallo yaƙe ƙoƙarin aikawa Bilkisu wani kukan kura yayi yanufi kansa ya shaƙo masa huya yahau naushinsa, baffa yana ɗakinsa yana jijjiga ƙofarsa dan yajiyo kukan ƴarsa kuma yaga shigar Sani, amma ƙofa taƙi buɗuwa.
Abokin yallo yana ganin abunda Sani yakeyi aikwa ya ɗaga sandar sa ya rafka mai akansa, wata ƙara sani yayi ya faɗi akasa ko motsi mai ƙara yiba, ganin Sani aƙasa baisa sunfasa abunda sukayi niyyaba.
Duk ihun da Bilkisu take hakan baisasu barintaba saida suka yimata fyaɗen su biyu tukun suka futo aguje suka buɗe inna Larai suka bar gidan.
Inna Larai tana futowa tahau kukan ƙarya taje ta buɗe baffa bangajeta yayi yayi ɗakin Bilkisu da gudu.
Wata irin cin burki yayi saka makon abunda ya gani, hawaye yafara bin kuncinsa, Bilkisu nannaɗe da zanin katibarta amma ganin jinin dayayi dakuma kayanta daya gani agefe ayage yasashi gane abunda ya faru, rarrafowa Bilkisu tayi dukda raɗaɗin datakeji tayi kan Sani tana jijjigashi, baffa ma yayo kansa yana duddubashi. "Wannan wace irin ƙaddara ce haka, Bilkisu wayayi miki haka? mai mukayi musu? Da zasuyi mana wannan aikin, Bilkisu sun kashe Sani sani bashi da rai sun kashemun ɗan daya r..." saitin zuciyar sa baffa ya riƙe Bilkisu ta riƙeshi tana kuka. "Baffa karkayi mun haka karka tafi kaima kabarni, inkatafi ka barni yaya zanyi da wannan abun daya sameni? Wazai soni wazai yadda inkasance tare dashi baffa? Narasa komai baffa karka barni a..." murmushi yayi tare da shafa kanta a hankali yace"Allah yabi miki haƙƙinki yasa mana, Allah ya haskaka miki rayuwarki Allah yayimiki albarka nayafe miki duniya da lah.." kalmar shahada yafarayi nan take ya faɗi ba numfashi, wani ihu inna Larai tasaki tayi waje, tana murmushi acan ƙasan maƙoshinta.
Wata sandarewa Bilkisu tayi ta kalli Sani ta kalli baffa.
**********
Tunda ranar ta maida su hajiya ƴan aikin gidan, Huzaifa ne kawai bata juyawa yadda takeso saita haɗa da babarsa tukun yakeyimata abunda takeso.Hannatu kuwa alaƙar ta da big boy babu abunda ya canza ita kuma ganin ankawo kuɗi harda sarana yasa taƙara sakar masa jikinta sukeyi abunda suka gadama.
Huzaifa ya dawo dan ɗaukar wata takadda ya tarar da hajiya tanata kokawar yin girki Hannatu kuma tanata yanka salat, ransa yayi matuƙar ɓaci aikwa yayi ɗakin Fatima rai a ɓace.
A kwance ya ganta tana kallo a tv, yana zuwa ya wanka mata mari azabure ta miƙe. "Ni ka mara?" tana rufe bakinta ya ƙara mata wani marin cikin zafun rai yace"Wallahi idan bakije kin warware abunda kikayiba saina yi mugun saɓa miki dan bakida hankali mahaifiyar tawa zaki ayar ƴar aiki? To wallahi kan indawo inbaki warwarw abunda kikayi musuba sainayi miki saki har guda uku, inkuma kina ganin wasa nakeyi to muzuba mugani nida ke." yana gama faɗa yasa kai ya fuce daga ɗakin.
Tunani takeyi tabbas zai aikata abunda yace tunda shi asirin bai kama shiba, ɗakinta tashiga ta ɗau mayafi da mukullin motar hajiya data ƙwashe ta zuba kuɗi ajaka ta futo ta hau mota tayi gaba.
Wannan gun matsafin taje, tana zuwa ta shiga ɗakin dayake, akwance ta tarar da shi yana wasa da wasu duwatsu ya cilla sama su ɓace.
Yana ganinta ya miƙe zaune yace "Tabbas ansanar dani akwai matsala kuma kina kan hanyar zuwa nan." zama rayi ta gaya masa duk abunda ya faru. "Yanzu maikikeso ayi masa?" "Inaso kawai ka haukata shi kuma haukan batuburan ba hauka wanda zaikasance bashi da amfani bazai magana ba kuma bazai taɓa moruwaba." "Kina nufin in maidashi dolo kenan?" wani murmushi tayi tukun tace "Ƙwarai da gaske haka nake nufi." wata dariya ya kwashe da ita yace "Ki ajiye kuɗi aƙasa ki tafi kankije angama aiki sanɓan jibi kizo ki bani tukwiyci na, shikuma harta kashi da futsari azaune zaidinga yinsa." "Angama boka kwana biyarma zan maka cifff in aiki yayi yadda nakeso." kuɗi ta zube masa sannan ta tashi ta tawo cikin ƙwarin gwiywa.
Tana zuwa gida wajen sallar la'asar akeyi, hajiya ta gani ta futo daga ɗakin Huzaifa "Ya akayi ne hajiya naga kin futo daga ɗakin sa." wata ƙwallah hajiya ta goge sannan tace "Yarannan ne kawai yana ɗaki naji ya ƙwalla ƙara muna zuwa mukaga ya koma wani dolo yanzuma futsari yayi a zaune baya magana saidai yaita kallon mu." wani murmushi Fatima tayi tukun ta shige ɗakinta.
*Alhamdulillah anan na ko ƙarshen book 1 Allah yasa an anfana da abunda na rubuta duk da ban gama shiba nagodw sa irin sa ƙwanninku masoyan book ɗina Allah tabar ƙauna ameen. 80k ina godiya sosai da irin ƙoƙarin da kayi mun🤝🏻🤝🏻*
*Saimun haɗu a book 2👋🏻*