page 26

208 17 2
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952

*Ƴan group ɗina da ƴan ragowar group haƙiƙa ina miƙa ɗinbin godiya agareku irin Addu'oin da kuke yimun Allah ya bar ƙauna ameen.*😘🥰👏🏻

*Page 26*

*Cigaban labari*

A zabure hajiya ta miƙe."Kotu kuma? Dama ƙawan cena da babar yarinyar nan abanza, harna aura mata ɗana,ashe mutuniyar banza ce, ni da ko ƙaunar jin sunan ƴansan da banayi amma ace anksini ƙara kotu, nashiga uku na." ko ƙala baice mataba kwashe-kwashen ta ne ya jamata, kallon ta kawai yake yi, kallon sa itama tayi. "Au kai ko ajikin kako? na gama hankalin ka akwance yake sai wani kallona kakeyi uwa kasamu tv ko?" gudun sababinta yasahi cewa. "Hajiya bawai farinciki nakeba kawai ina tunanin irin halin dazaki shiga agidan yarine, dan na tambayi abokina lauya akan wannan batun kan inzo gida yake cemun kotu zata yanke miki hukunci wata biyune a gidan yari tare da horon fasa dutse da sare bishiya da zakiyi, kuma ssnnan zaki biya tarar dubu dari biyar." hannu ta ɗora akanta. "Nashiga ukuna, yanzu ni ina zan iya sare bishiya bayan ko farkara ice bazan iya ba, balle fasa dutse wayyo Allah na! naga ta kaina." Huzaifa dariya ce take son kufce masa amma yasan inyayi ya shiga uku, yana sane ya gaya mata haka saboda yasan halinta yanzu zata ɓullo da wani abun, kallonsa tayi cikin muryar mai shirin yin kuka tace. "Yan zu babu mafuta awannan lamarin? Wallahi bana son zuwa gidan yari." "Eto hajiya akwai mafuta guda ɗaya raƙ." cikin zumuɗi ta zauna ta ce. "Me cece mafutar gaya mun dan Allah ɗannan." "E to hajiya mafutar ita ce, adarar indai kika yadda inrubuta mata saki uku kibayar akai mata gidansu hakanne zaisa ta janye ƙarar gobe shikenan." wani murmushi tayi. "Abu mai sauƙi kenan, maza kiramun ita kasake ta kowa ya huta." "Ai hajiya tun rana bata gidan." kyaɓe baki tayi. "Muguwa mai mugun hali kenan ashe ma bata gidan, maza rubuta sakin kaje ka kai mata." wani farin cikine ya lulluɓe shi. "Hajiya ai dare yayi shawara ɗaya ce intura mata da saƙon saki ta waya tana gani shikenan." da hanzari tace. " Maza tura mata maza kayi sauri." wayar sa ya zaro a aljihu ya tura mata da saƙon sannan ya tashi ya fuce daga falon, tama manta bata bashi maganin saba.

Hannatu kuwa tana ɗakinta amma tana jiyo su kuma takasa futowa gani take uwa inta futo suka kalleta zasu gane abunda big boy yayi mata ne, gefe ɗaya kuma tana jin uwa har yanzu big boy baicire hannunsa daga jikinta ba danji rake uwa hannun tana ra yimata yawo ajikinta yanzu, a haka ta samu barci ya ɗauketa.

*Washe gari.*

Tun 9:00am gidan hajiya ya fara cika da ƙawayen ta, ƴan siki sai hada-hada suke hajiya ta hansu sakar kekyace biki ake ko suna, sai da aka ɗora babbar tukunya ta girki hajiya aka siyo laimuka taɗau wanka, amma duk abunnan da akeyi Bata gayawa anty ba ƙanwarta uwa ɗaya uba ɗaya, sai misslin ƙarfe 3:00pm sannan dangin Fatima suka zo, kaya iya kaya hajiya ta gani dan abun yayi mugun bata mamaki ko ƴar masu kuɗi sai haka komai anzubo harda albasa da daddawa komai awada ce nan da nan hajiya tafara buɗawa ƙawayen ta suna yimata kirari, tukƴicin naira dubu saba'in ta bayar, wayyo nan fa ƙawayen ta suka fara cewa. "Sai hajiya uwar talakawa." wayyo hajiya kunan ta har rawa yake saboda daɗi kanta yana ƙara girma, Mukullin motar da big boy yabata ta ɗakko tana nuna musu har bakin get sukaje suka ganta masu baƙin ciki nayi masu yi mata zugar ƙarya ma nayi,sai misalin 6:00pm gidan yayi hankali hajiya ta hau raban kayan gara ita da Hannatu, Fatima kuwa tana ɗakinta tanajin daɗi.

Nusaiba kuwa tasha habaici agun Hajiya amma bata ce ko ƙalaba Zabba'u kuwa taci albarkacin motar da big boy ya bata dan har ɗaki taje ta kirata ta nunawa ƙawayenta sirikarta.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now