page 46

140 14 0
                                    

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp nomber*
08085898952


*Page 46*

Tana zuwa gida kuwa ta tarar da babu Zabba'u agidan, ɗakin inna ta shiga ta tsaya akanta "Ina waccan yarinyar ta tafine?" ta faɗa tana mai nuni da ɗakin Zabba'u, jikin hajiya yana rawa ta hau cewa"Haka kawai muna zaune ta futo da akwatu tace sai Huzaifa ya saketa, shikuwa bai tsaya komaiba yayi mata saki uku a tsakar gidannan kuwa, tasa kai tafuce daga gidan." ɗan guntun tsaki fatima tayi sannan tace,"Hannatu maza jeki kiramun ƴan aikin gidannan." da sauri ta tashi ta zagaya bayan gidan sai gata da ƴan aikin guda biyu sunzo.

Fatima tasa hannu a jakarta ta ɗakko kuɗi tabawa kowacce acikin dubu biyar-biyar. "Maza kuje ku haɗa kayanku nasallame ku daga gidannan yanzu bama buƙatar ƴan aiki da kanmu zamuyi aikin." ba wadda tace komai acikinsu suka tashi suka bargun.

Fatima kuwa tayi ɗakinta bata ƙara cewa ko uffan ba, tana shiga rayi wanka tasamu gadonta ta gwanta nanda nan barcin gajiya ya kwasheta.

*Ruga*
Tsuntsuwar data koma kamar bilkisu sak ta futo tsakar gida, ko ina da ko ina take kallo tana girgiza kai, ɗakin inna Larai ta kallah ta wani haɗe rai idonta yayi jajir uwa garwashi ɗakin ta nufa ta ɗaga labulen, inna Larai ta jiyo dan ganin wanene yayi mata haka. "Au ho watakan iskancin nakine ya motsa ko? Shine dan baƙin hula ƙanci zakizo ki ɗagemun labule sauro ya cika mun ɗaki bara kigani dan ubanki." tashi tayi cikin masifa tana riƙe zaninta tana zuwa bata tsaya komaiba jikuke tasss! tass! Ta wanke da mari a kunci biyu. "Kuma wallahi adarannan zakiyi wa su Lami wanki tunda bakida mutunci mutuniyar banza kawai." bazar-bazar ta yi cikin ɗakin ta ɗebo kaya ta watsowa Bilkisu abuska. "Kije abakin rijiya akwai omo da sabulu maza ki wankesu tas ki shanya su." ɗakinta ta koma ta haye kan gado ta bararraje iskar fanka ta rufe ido da sunan tayi barci.

Kayan data watso Bilkisu ta kwashe ta kaibakin rijiya ta zauna akan rijiyar hannunta ta ɗaga daidai saitin ɗakin inna Larai take saiga ɓeraye manya-manya suna bayyana waɗanda yawansu yakai guda talatin, wata dariya ta kwashe da ita ta ɗaga ɗanya tsanta nantake suka shige ɗakin inna Larai.


*Adadin comment adadin type🤷🏻‍♀*

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now