https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*DEDICATEN TO*
*GIMBIYA BALARABA FANS**Page 29*
Zuwa yanzu Hannatu harta saba da abunda big boy yake mata, dakanta ma takeyi masa shikuma kullun cikin kawo mata salo-salon abubuwa yake ga zuwa faty duk ta iyasu da sa ƙananun kaya, ran Huzaifa yana mugun ɓaci daya dan haka yau ya tunkari hajiya da zancan.
"Hajiya agaskiya halayyar da Hannu ta sake ba mai kyau bace, dan haka zan ɗau babban mataki akanta." "To uban ta! Wallahi-wallahi in ka kuskura koda tsawa ce kayiwa yarinnan nan akan wannan abun to ban yafe maka ba, saikace ba ɗan zamani ba, to sokake taƙi wayewa kamar sauran ƴan matan gari, to wallahi ahir ɗinka, kuma ai mijin da zata aura ne yakeso wayayyar mace kaga kuwa dole ta waye itama, dan gidan arziƙi zata tafi." tun lokacin data ce bata yafe masaba hutar kansa ta ɗauke, ragowar maganar sama yayi haƙuri da faɗarta, cikin muryau rauni yace. "Hajiya insha Allah bazan ƙara yi mata magana ba akan abunda take, kema Allah ya baki haƙuri." cikin hayayyaƙo wa tace. "Ameen ameen, daya fima ka wallahi, kullun wannan ƙanwar tawa ce take hure maka kunne ko? To saika yi la'akari da irin halin talaucin data ke ciki, kan ka ɗau maganar ta shashashan banza kawai." jikin sa ba ƙwari ya tashi ya futo, ɗakin Fatima ya nufa dan sunfi mutunci da ita, afalo ya tarar da ita tana kallo, waye ya samu ya zauna sannan ahanka li yace. "Bani ruwa mai sanyi da laimo." girgiza take tana wani jujjuyawa duk dan ta burge shi amma shi gaba ɗaya hanka linsa bama ya kanta, ɗakkowa tayi a ajiye masa agaban sa sannan ta zauna akusa dashi. "Dama tun ɗazu nake son ka dawo, bikin ƙawata za ayi shine nakeso kabani kuɗin anko dana ƙunshi dana gyaran jiki da na ɗinki sai kuɗin gudun mawa." wani guntun tsaki yayi sannan ya zira hannu a aljihu ya zaro kuɗi dubu goma ya ƙirga ya bata.
Wani jijjiya kuɗin take uwa wacce aka bawa bushashen kashin gardi."Mai zanyi da wannan kuɗin? Haba dan Allah wannan ai ko kuɗin ankon ma baza su isheniba bare kuma rago war gaskiya ka ƙaramun nida nake sa ran zaka bani koda dubu ɗarice inyi maleji da ita, wani kallo yake mata na baki da hankali, cikin masifa yace mata. "To bazan bayar ba, ko bikin ƴar gwamna za kice bazan baki har naira dubu ɗariba, daya ke baki san ciwon naima ba da za a kashe wannan uban kuɗin, na ƙarfine ki kwata inkin isa." ko ruwan ma baisha ba ya fuce daga dakin ya ma bar gidan gaba ɗaya.
A ƙafa yake ta tafiya yana tunani kala-kala, ko duhun da gari yayi bai ganiba haka yake tafiya yana tunani aransa.
Yana futa fatima da daga wani uban tsaki. "Tab ɗijan? wallahi baza ta taɓa saɓuwa ba, inbaka bani ta lallami ba ai kabani ta hanyar da dole saika ba yarɗin, nida nake da babar ka a hannuna hhhhh zakaga tsiya ne." tashi tayi ta futo ta nufi ɗakin hajiya.
Hajiya tana zaune ita da Hannatu suna hirar bikin Hannatu irin budurin da zasuyi, wani kyaɓe baki Fatima tayi a zuciyar ta tace. "Kai wannan matar akwai kawo abunda babu shi, bikin da ko kuɗin aure ma ba'a kawo ba amma harta fara tsara yadda zatayi shagalin ta." A fili kuma tayi murmushi tare da samun wajen zama. "Hajiya gurinki nazo." gyara zama Hajiya tayi ta kalleta. "Ina jinki, Allah dai yasa lafiya?" nan da nan Fatima ta maida fuskar ta uwa wacce aka mata shegen duka harda ƙwallar ta. "Hajiya kinga bikin aminiya ta za ayi, kuma kowa acikin ƙawaye na maganar su ɗaya ce, Fatima tayi aure agidan arziƙi, shine fa nacewa yaya Huzaifa ya bani kuɗin hidimar biki, shine ya ɗakko naira dubu biyar ya bani wai har kuɗin gudun mawa, dana yi masa magana shine harda marina." "Mari! abun harda mari kuma, to wallahi bara yazo ya same ni dole ya baki kuɗi kiyi hidimar bikin ki." murmushin mugunta tayi, hajiya kuwa sai sababinta takeyi, Hannatu kuwa wayar ta take danna wa ko ƙala bata ce musuba.
Huzaifa wani shagon saida shawarma yasamu daya ke ɗan gaba da su ya shiga ice cream ya siya da shawarma sai laimo, yazau na yana ci yana tunani kala-kala akan rayuwar sa, sai wajen 10:30pm sannan ya shigo cikin gidan, ɗakin hajiya ya nufa da zumman yayi mata saida safe, Fatima da hajiya ya tarar a falon suna kallo, hajiya tana kallon sa ta wa haɗe rai. "Kai yanzu ka kyauta da abunda kayi, ace dan yarin ya ta tambayi kuɗin biki shine kaba naira dubu biyar, to mai wannan kuɗin zaiyi mata? shine dan ta ƙara yima ka magana harda marinta, to wallahi ka futa daga idona." jin zancan yayi awani hagunce. "Hajiya ita tace miki na mareta? Yanzu hajiya ko wa...... "Kaga kayi mun shiru, kai kanka kasan yarin yar nan haƙuri take da zama da kai, kai ba ishashshiyar lafiya ba, har magani na amso maka amma hidimar ƴan amsar kayan gara sukayi ɓarin sa, amma duk da haka ta shanye bata ce komai ba, shine zaka mareta, to maza kaje ɗakin ka ka ɗakko mata dubu ɗari da hamsin ta fanta ma, dama ai amfanin arziƙin kenan ayi abunda mutane za susan kana da shi." bai ƙara magana ba ya tashi ya futa,zuwa minti ƙaɗan yashigo ɗauke da kuɗi ahannun sa, agaban hajiya ya ajiye kuɗin ya juya zaifuta. "Hajiya saida safe, kekuma nagode." yana gana faɗa yasa kai ya fuce daga ɗakin, yana shiga ɗakin sa yaja ƙofar sa ya rufe.
Yana futa Fatima harda durƙusa wa agaban hajiya. "Hajiya nagode sosai wallahi." "Ai bako mai, maza ɗau ki kuɗun kije kiyi hidimar bikinku, kuma karki matambaye shi zuwa bikin kije abunki kawai." "Kai amma kwa hajiya na gode sosai, saida safe." "Allah ya kaimu." hajiya tace tana washe baki, Fatima na futa itama ta rufe ƙofa tashige ɗakinta ta kwanta.
![](https://img.wattpad.com/cover/182799248-288-k151541.jpg)