page 16

266 17 0
                                    

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳
 
    *SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
      *(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp  nomber*
08085898952

*Barka da sallah my pans Allah ya maimai ta mana ameen🥰🤝🏻*

*Aduk inda kuke masoyan Surukarmuce ina gaisheku kuma ina jinjina muku👍🏻*


*Page 16*

Gyara zama hajiya tayi."To uban kini bibi, kaibaka taɓa ganin mutunba amma har ka yanke masa hukunci, to ba abunda zai faru sai alheri, kuma wallahi kafuta daga idona in ba haka ba nida kaine shashasha." bai ƙara cewa uffan ba jiyayi abinci ya futa daga ranss kwata-kwata,sallamar hannatu ce ta dawo dashi hayyacin sa,ɗago kai yayi ya kalleta ganin shigar datake jikinta da kuma lokacin data dawo yaka mata ya tsawatar mata amma inyayi magana yasan abunda zai faru dan haka yaja bakinsa yayi shiru.

" Hajiya kinga mun daɗe ko? Wallahi gun ne ya ɗauke mun hankali kinga kuwa yadda masu kuɗi suke jin daɗinsu kuwa? " washe baki a
Hajiya tayi. "Ai baki wani daɗeba nawa kika samo? Nasan gun dama zai haɗu su masu kuɗi ai babu ruwansu da damuwa." "Lah yaya ashe kana nan,wallahi idona yarufe sannu da zuwa." yaƙe kawai yayi ya tashi ya fuce daga ɗakin.

Bilkisu saida taga ma komai sannan ta nufi gun inna Larai. " Inna nagama aikin." "To shine zaki wani zo ki tsaya mun akai, salan kisamun ciwon kai ko, maza huce ki bani waje mai kama da aljanu." sumsum sum tabar gun ta je gun umman ta tabata kokon tasha ta kwantar da ita. "Auta ki kwantar da hankalinki wata rana sai labari alƙawari ɗaya nakeso kiyimun." "Wane alƙawarine umma?  Ɗan tari tayi sannan tace. " Inaso duk huya duk rintsi kada kisake ki siyar da mutunciki kuma inaso kiyiwa mahaifinki biyayya mutuƙar bai saɓawa Allah ba indai kikayi hakan to haƙiƙa zaki tarar da farinciki anan gaba." wani hawaye ta share. "Umma namiki alƙawari insha Allah zanyi abunda kika ce." Fifita take yimata har tayi barci ita kuma ta futo ƙofar gidansu ta zauna tana wasa da kara tana rubutu a ƙasa." Salamu alaikum ƴan mata." ɗago kai tayi dan taga wake magana, Musa ne ɗan mai gari, yana yawan yimata magana. " Amin wa alaikussalam yaya Musa kaine ashe? Murmushi yayi dan yana mstuƙar jin daɗin girmamashin datake yi. " Nine Bilkisu jiya da daddare nadawo gari shine nace bara inzo in ganki." murmushi tayi dan tana matuƙar jin daɗin zama dashi yana koya mata karatu da rubutu gashi da mutunci.

"Ya jikin umman taki." "Da sauƙi amma haryau inna Larai ta hana akaita asibitin cikin gari." wata iska ya furzar sannan yace. "Ki kwantar da hankalinki tunda nadawo gari zan san yadda za ayi, baffan ku ya dawo? Miƙewa tsaye tayi. " Baida woba sai zuwa anjima." " To tashi muje ki rakani gun kaka mai ƙuliƙuli." dariya tayi sannan tace. "Amma bazamu daɗeba ko? dan umma tana barci karta tashi tana son wani abu." "Karki damu bazamu daɗeba." tafiya sukayi suna hira suna dariya.

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now