https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*SURUKARMU CE*👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳👩🏽🦳
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________©
*Zainab Abdullahi*
*(Real_shaxee)🍒**Wattpad*
@Real_shaxee*Email*
rzainababdullah@gmail.com*Facebook*
*Zeenat deen shaxee**Watsapp nomber*
08085898952*Page 23*
*Ruga*
Aikin ta fara cikin ƙwarewa ta share gidan tass ta haɗa wanke-wanken sannan ta janyo ruwa ta cika komai na gidan, sannan ta zauna tana jiran su Samira su dawo tayi wanke-wanken ƴan waƙe-waƙen ta takeyi saiga su Samira sun shigo kowacce ɗauke da robobin tallanta. "Inna! Inna!" suka fara kwaɗa mata kira, cikin sanyin jiki Bilkisu tace."Bata nan ɗazu ta futa." wani kallo suka watsa mata, cikin raini Lami tace. " To faɗi ba a tambaye kiba, ina abincin mu?" "Wallahi bata barmun ba namu kawai ta bani." da sauri Laure tace. "Kan ubancan to wallahi saidai ku ku haƙura mu muci aidama bakune kuka yi girkin ba, saiku bari in Baffan daya fi sonku ya dawo saiya dafa muku kuci, Samira ɗakko mana muci." da sauri Samira taje gun samirar da ɗakko ta ta miƙawa Lami. "Ungo ku kuci ni a ƙoshe nake naci awara da ɗan wake ɗazu, bara inje ma ni indawo." amsa sukayi cikin mugunta suka buɗe suka fara cin dambun, ko ƙala Bilkisu bata ceba ta huce ta ɗau robobin ta ajiye fai-fai ɗin rufe nonon da gammon ta huce da robobin gun wanke-wanke ta fara aikinta ko kallo basu ishe taba.
Suna gama ci Lami tasa ƙafa tayi fatali da samirar. "Gata nan inkin gadama ki wanke, inkuma baki gadama ba kibarta anan yau za ayi kwanan yunwa agidannan hhh, Laure zo muje ki raka ni gun Lantana." "To muje ma biya ma mutawo da gyaɗa ina son ci." fuce wa sukayi abun su, Bilkisu ta tashi ta ɗakko kwanon ta haɗa ta wanke su, tana gamawa ta kai kofar ɗakin inna Larai ta ajiye sannan ta huce ɗaki da samirar su.
Tana shiga ɗaki tatarar da umman ta tanata numfashi sama-sama aki ɗime ta nufi inda take. "Umma! Mai ya sameki umma ki tashi dan Allah." kuka ta saki tare da rungumo ta, su Auwalu shigo warsu kenan sukaji kukan Bilkisu da sauri suka yadda kayan hannun su suka nufo ɗakin da sauri, ganin halin da umman su take ciki ne ya ɗaga musu hankali suma. "Yaya Auwalu bara inje in kirawo Baffa yana ƙofar gida." bai saurari kowa ba ya tashi da niyar fucewa umman su ta ruƙo hannun sa. " Karku damu ni tawa tazo ƙarshe, alƙawari ɗaya kawai nake so kumun shine karku yadda wani ko wata yayi nasarar raba tsakanin ku, ga Bilkisu nan nabaku ita amana ku riƙeta kamar ni zan riƙeta kukula da tarbiyar ta da kuma wanda zata au... Ɗuff suka ji dan haka suka hau jijjiga ta, da sauri Salisu yayi waje saiga shi tare da Baffa yana zuwa ya fara duba ta ina rai yayi halinsa, zanin daya ke kusa da ita ya ɗakko tare da lulluɓe mata fuska.
Ganin haka da sukayi suka ƙara rushewa da kuka, kamo su Baffa yayi ya rungume su shi kansa ƙwallah yayi saboda yana son Amina sosai.
