page 12

326 13 0
                                    

https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳
 
    *SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
      *(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp  nomber*
08085898952


*Page 12*




Yana zuwa ya tarar da kofar arufe buga kofar yake uwa zaikarya ta amma taki zuwa ta bude ta kowacce yaje dakinta amma bata budeba ransa yayi mugun baci dakin hajiya yadawo inda ya tarrar da hajiya tafarka zama yayi yana huci. " Wallahi yau yarannan saina koya musu hankali ai zasubude kofar yau kowa a gidan ubansa zaikwana." da sauri hajiya ta dago kanta. " Karabu dasu yarane wataran zasu daina kasan mata da kishin tsiya, komagana karkayiwa kowacce kajinan ko." ko magana baiyiba girgiza Kai kawai yayi anty kuwa tabe bakitayi saboda tasan hakan zata iya faruwa.

Fatima kuwa sai safa da marwa take a dakinta. " Mutanan nan suna naima su farkemun aikina ina bazaiyuhuba, dole insake shiri dukiyar gidannan tawace nikadai zan mallaketa inmallake mutanan gidannan sukuwa wadancan matan kowacce saina sa ansaketa sakin hulakanci nikadai zanzauna agidannan." Wata mahaukaciyar dariya tayi Tare da dakko wayarta. " Hello malam inaso kamun aikin rufe baki yanzunnan kudin aikinka zanzo inkawo maka." Kashe wayar tayi sannan ta ajiyeta.

Zabba'u kuwa tana dakinta." Aikin banza nakawo kaina cikin matsala ina can ina rayuwata cikin farinciki da 'yanci amma nakawo kaina nan,ni wallahi  aurannan duk yafara damuna abunda nazo naima kuma bansamu ba." wani saki tadaka ta hau chatting dinta.

Nusaiba ma taki futowa kwata kwata ga uwar yunwar datakeji ita kuma bata iya kumaiba bare tashiga kitchen dinta tadafa wani abu, ganin yunwa tana naiman illatata yasa tashiga tatafasa ruwa ta hada shayi tazo tana sha tana tsaki.

Anty tana ganin hajiya ta warware tatashi. " Antyna  bara inje gida tunda naga jikin naki da sauki sosai, kuma maigida nasan yakusa dawowa." kyabe baki hajiya tayi. " To tattabara uwar aure mijin da bawani abun duniya bane dashi ko a uguwar ku nasan ba wanda yasanshi bare kuma ace aduniya." murmushi kawai tayi saboda tasaba da jin irin wannan abun jakarta ta dauka. " Hannatu kikula da ita sosai kinji nanda gobe ko jibi zandawo." hajiya tayi sauri tace. " Dan bakin Abu ko dakin amaren bazakijeba sai anyi magana kice ai Huzaifa dankine Wanda kikafiso." murmushi anty tayi tagyara tsayuwarta tace. " takanas naso zuwa ingansu sainace nace bara inbari in ankawo musu gara nazo inga hidima irinta masu kudi ba irin muba saikuma naji shiru haryau,amma zan shiga inza a kawo musu." shiru hajiya tayi har anty da huzaifa suka fuce daga dakin. " Hannatu kinga namanta da batun garako to wallahi ba a isaba bara anjima inkara jin Karin jikina kije kikiramun su."



*Adadin comment adadin type 🤷🏻‍♀*

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now