page 13

298 15 0
                                        

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳
 
    *SURUKARMU CE*

👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳👩🏽‍🦳

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION🤝🏻*
_______________________________________
*We are here to educate motivate entartain our readers*
_______________________________________


©
*Zainab Abdullahi*
      *(Real_shaxee)🍒*

*Wattpad*
@Real_shaxee

*Email*
rzainababdullah@gmail.com

*Facebook*
*Zeenat deen shaxee*

*Watsapp  nomber*
08085898952


*Page 13*





Hannatu tayi saurin cewa. " To hajiya kibari da daddare lokacin yaya baya gidan kinsan halinsa." cikin faɗa hajiya tace. " To uba nane shi? Koya isa ya hananin abunda nayi niyya? matan ma bani na zaɓo masa ba, duk yadda naga dama haka zanyi acikin gidannan." "To hajiya ki kwantar da hankalinki kibari ajinma ɗin." 

Huzaifa yana raka anty ta hau mota kai tsaye ya koma office ɗinsa saboda baya son komawa cikin wannan gidan.

Ƴan aiki suna gama girkinsu suka rabawa kowa har ɗakinsa hajiya ma suka kai mata nata.

Hajiya ce azaune akan kujera duk ta tarasu su huɗu, kallonsu tayi sannan tace. " To ninaga bawace ake shirin kawowa gara, dan haka inaso in tunatar daku zancan gara dan bazan aura muku ɗana ba ku kumore shi amma ku baza a morekuba dan haka kuyi gaggawar sanarwa akawo gara da huri, dan haka maza kutashi kubani guri." ko ƙala ba wacce tace suka tashi suka fuce.

Fatima tana zuwa ɗakin ta kwashe da dariya." Lallai ma matar nan, zakiga gara kuwa da kuɗin ki zan yi garar bakedai son abun duniyaba,zaki gani kuwa ganin idonki."

Hannatu kuwa tana gun big boy acikin motar sa suna zance,hannunsa yasa ya riƙe nata hannun. " Byba dan Allah zaki rakani wani paty abokina shida wata sabuwar budurwar sa, inason zuwa amma kuma banaso inje arainani ne ean kowa yasan banda budurwa sonake yau inbasu mamaki." shiru tayi dan tunda take inba paty bikin ƙawayen taba bata taɓa zuwa wani paty ba. " haba byba yana ga kinyi shiru ko baƙya son zuwa ne? In ba kya so kibarshi kawai." " A a ba haka bane bara inje in tambayo hajiya inta amince aishi kenan."

Hajiya kaɗai ta tarar a falon azaune tanacin ƴaƴan marmari. " Hajiya kinga big boy ne yakeso in rakashi pary abokinsa wai yana son ya nunani agun abokanansa, shine nace bara inzo in tambaye ki." " Kujimu da shashasha ke banda abunki zuwa paty wani abune yadda yake mai kuɗi haka abokanan sama suke kinga kina zuwa zasuyita bulbulo miki kuɗi kina amshewa maza jeki shirya kutafi amma karki daɗe kinjini." "To hajiya." da sauri ta shiga ɗaki tadau doguwar rigar ra mai kyau tasaka sannan tayafa ƙaramun maya fi ta feshe jikinta da turare ta futo.

Acikin motar ta tarar dashi shiga tayi ta zauna. " Hajiya tace muje amma karmu dade." wani mayau darin murmushi yayi. " Karki damu bawani dadewa zamuyiba amma sai munbiya tawani gu anmiki kwalliya ta kece raini, banaso araina mun ke." motar ya figa suka bar gida.




*Adadin comment adadin type🤷🏻‍♀*

SURIKAR MUCE Book 1Where stories live. Discover now